ABDUL JALAL PART 2

Kusan awa guda kafin likitan tazo,
“kiyi haƙuri Hajiya Khadija muna kan wani aiki ne shiyasa banzo da wuri ba, me yake damunki ne?”
Mummy babu baki sedai Nuni, likitar tayi gwaje gwajen da ya dace ta gano jinin Mummy yayi mummunar hawa, idan bata kula ba idan ta faɗi zata iya samun shanyewar ɓarin jiki.
Ta zauna taita bawa Mummy shawarwari amma sam Hankalin Mummy baya kan likita harta gama surutan ta tai mata allurai Mummy bata san me likitan tayi ba, ita dai tasan tana cikin tunani bacci ya kwashe ta.
Ilham an sallami mamanta daga Asibiti saboda ciwon ta bana Asibiti bane, Ilham tattar duk abunda suke dashi tana kai Umman ta gurin wasu ‘yan tsibbun ko zasu dace amma abu yaƙi, daga ƙarshe ta ɗauki umman ta zuwa gurin wanda yayi Asirin farko shima ya tsufa sosai ko gani baya iyayi ya bayyana musu cewar
“Yawan karatun Al’ qur’ani da kuma, zumar da Jalila ta dinga bawa Jalal ce ta illata Aljanin, sannan Jalila tana da tsari a jikinta sabo da riƙo da Al’ƙur’ani, shiyasa Aljanin ya samu nakasa kuma ya koma jikin Saudat, da an karya Asirin kafin Jalal ya haɗa shimfiɗa da Jalila da baze koma kan umman ta ba”
Ilham tace “Yanzu babu wata dabara ko wani abu dazaka iya yi mana akan wannan larurar”
“yarinya babu wanda ze iya yiwa mahaifiyar ki komai, sedai kukoma ga Allah ku zuba mata ido a haka, duk wanda yace ze muku magani ƙarya yake yi, tun a baya da yarinyar nan ta fara bibiyar sa na nusar daku, Amma kuka gaza ɗaukar wani ƙwaƙwaran mataki, yanzu se dai kuyi haƙuri”
Haka Ilham ta tattaro suka dawo gida, ba wani me basu wani taimako musamman idan akaji abunda sukayi, yayan Ilham yana prison baban su kuwa idan ya shura ya bar gida se ya shekara uku be zoba, ga dangi da ‘yan uwa dama ba wani jituwa ake ba, Saudat bata ganin kowa da mutunci dan haka ba wanda ya damu da halin da suke ciki, a hankali komai nasu ya fara ƙarewa saboda jinya, ga Ilham ta fara gajiya taita hantarar Umman ta wasu lokutan, idan tayi ba haya ko fitsari a zaune setai tafiyar ta ta barta a gurin se ta daɗe cikin najasa sannan tazo ta kula da ita.
Abubuwa suka cakuɗewa Ilham abunda za suci ya fara nema ya gagare su, da dane da sedai tayiwa Mummy waya ta turo kuɗi, banda wanda zata sata ta kawo gida, se yanzu take dana sanin abunda tayi, da ta sani da ba ta ga yawa duniya su sukayi wa Jalal Asiri ba da koba komai baza su rasa Abunda za suci ba.
Jalila tana kwance a jikin Jalal tana chatting taga surutun da ake a group ɗinau na makaranta yayi yawa dan haka ta sauka ta shiga domin ganin surutun me sukeyi haka?
Sameera ce da Saleema ‘yar gidan oga KB aka kuma kamawa a gidan karuwai suna aikata miyagun laifuka har an kaisu kotu an yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali.
Da sauri Jalila ta miƙe zaune tace “Zaujee kaga”
Ta nuna masa ya karɓa ya gani yace “Allah ya kyauta”
Jalila tace “Zaujee Saleema ‘yar Oga KB ce, shi yana prison itama yanzu zata tafi prison na ɗauka tun a wancan lokacin ta shiryu”
Jalal yace “Jalila dan Allah karki saka damuwar wasu a ranki ki hana mana jin daɗi, shiyasa fa ban gaya miki su Hannah ma an kaisu prison ba, Sannan Jeje yayi rashin lafiya lungs cancer yai ta fama a prison ga rashin kula watansa guda da mutuwa, shima oga KB yana Aisbitin cikin prison paralyze ya kama shi”
“Innalillahi wa inna ialaihi raji’un”
Shi Jalila ta dinga nanatawa ta kalli Jalal tace
“Zaujee me Jeje zeje ya cewa Allah, mutuwa ake tsoro dama, Allah ya karɓeka ba zato ba tsammani ba tareda ka shirya mata ba, Allah ya jiƙan musulmi”
“Ameen ya Allah, bance kuma ki zauna ki damu kanki ba, in kuwa naga kin damu na dena baki labari”
“to bazan damu ba” ta faɗa a sanyaye, amma ƙasan zuciyar ta so take tayi kuka
Seda sukai wata guda a UK sannan suka fara haramar tafiya, dama tana kewar Nijeriya sedai suyi waya da ‘yan gida, ga shi tayi missing wasu abincin Nijeriya, dukda sun sha yawo sunsha soyayya sunyi ƙiba sunyi kyau daga ita har Jalal ɗin, sukaje suyiwa su Nana sallama.
Jalila tace “Yaya Mahmud yaushe Zakabar Nana tazo Nigeria gara ta haihu a Nijeriya”
Mahmud yace “Injiwa? Gara ta haihu anan semu taho Nijeriya”
Jalal yace “Sarkin wayo so kake yaronka ya zama citizen ɗin UK kenan?”
Mahmud yace “Ashe ka gane bros”
Haka sukayi sallama suka koma gida, Washegari ƙarfe goma Mahmud yaje ya ɗauke su ya kaisu airport sukayi sallama shi yakoma.
Maimakon su sauka a Kano se suka sauka a Abuja gidan su Jawwad, Jalal be gayawa Jalila ba, ya dai ce mata ze kai ziyara Abuja sam bata kawo gidan su Hanan zasu ba.
Tana ganin Hanan suka rungume juna, cikin Hanan har yafi na Nana fitowa da girma.
Jalila taita tsokanar Hanan tana gwada yadda take tafiya, Jawwad kansa yaji daɗin ganinsu, gaba ɗaya sunyi ƙiba, Jalal kamar ba shine me yawo da Sarƙa, da askin banza a ka ba yayi ƙalau da shi ya zama babban mutum.
Jawwad ya ja Jalal suka fice suka bar su Hanan a gida, dukda ranar suka sauka Amma Jalila seda tayiwa Hanan gyaran gida da sauran abubuwan da bata iyayi, saboda tana shirin zata koma gida haihuwa.
Jalila se santin gidan Hanan take yi, ta fita ta ɗan zaga ta samu ƙanan guava sun faɗo ko nuna basu yi ba, take taji ranta ya biya ta tsinto tazo saka a leda ta jefa a jakarta, Hanan har mamakin ƙibar da Jalila tayi take
“Jalila anya ba’a gamu ba kuwa? Kinga yadda kika zama wata uwar mata”
Jalila tace “Aka gamu dame?”
“ciki mana” Hanan ta bata amsa
“An gaya miki kowa irinku ne, bani da komai hutawa ta nake”
Hanan tai murmushi tace “to me yake hanaki cin Abinci se kin zaɓa?”
Jalila ta ɗan yamutsa fuska tace “ke nifa ba abunda yake damuna, ni ba laulayi nake ba, bani da komai tunda muka bar Nijeriya komai ya dena min daɗi ne kawai Abincin su bana jin daɗin sa ne”
Hanan ta ƙyale Jalila dan tasan ta da taurin kai.
Kwanan su Jalila uku suka baro Abuja zuwa kano, Hanan kuma ta tafi Bauchi a can zata haihu, tunda suka taho Jalal yake lura da Sam Jalila bata son Abinci se dai ciye ciyen shirme, ga bacci kamar wata kasa duk inda ta samu bacci, abu kaɗan ze mata ta fara kuka yanayin nata ya ɗan fara damunsa daya takura taci Abinci seta fara kuka ga yawan complain na ciwon ciki da take yi.
Haka suka dawo gida, kwanan su biyu da dawowa Jalila ta matsa masa suje yaga halin da Mummy take ciki, ba dan yaso ba ya shirya da daddare suka tafi.
Abunda ya basu mamaki be wuce yadda ta rame ba, da ƙyar take iya miƙewa ma bata da lafiya sosai.
Duk tsaftar Mummy amma gidan duk yayi ƙura, ko magana bata iyayi.
Suka ɗauke ta zuwa Asibiti, likitoci suka rufu akan ta saboda a galabaice take.
Jalal suna reception suna jira, ya hango doctor Salis ya miƙe yaje suka gaisa cikin fara’a doctor Salis yace
“Jalal keine ka koma haka? Kayi ƙalau da kai se jin labari nayi wai kayi aure daga kai har Jawwad ba labari”
Jalal yace “Aini nawa Auren ne yazo ba shiri, Mummy muka kawo Asibiti babu lafaiya, kuma muna tare da madam ɗinma kuwa dan Allah ka dubamin ita na kasa gane kanta”
Jalal ya nuna masa inda Jalila ke zaune tana danna waya, suka ƙaraso inda Jalila take doctor Salis yace
“kai wannan ai Jalila ce, ita ka aura Jalal”
“Eh itace”
“Allah sarki ashe shiyasa aka dinga yimin hanya2 ashe kaine a gurin, masha Allah, Allah yasanya Alkhairi ya baku zaman lafiya”