ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Bayan sun gaisa Maama ta nuna masa ɗakin da Jalila ta shige tace “tana ciki tunda ta shigo bata kulani ba bansan me ya faru ba”
Jalal ya jinjina kai ya nufi ɗakin da Jalila take, ta ƙule akan gado tana ta sharar hawaye, Jalal yaje ya zauna a kusa da ita yace “Jalila ki taso mu tafi gida”
Shiru tayi ba tace komai ba.
Yasa hannu ya ɗago ta gaba ɗaya yace “kiyi haƙuri kizo muje gida se muyi magana”

“ni ba zan biki ba ka ƙyaleni, ka bari Mummy ta samo maka matar da take so ka aura”

Ɗan ƙura mata ido yayi kafin daga baya kaman wanda aka yi wa dole yace
“har kina tunanin akwai macen da zata iya zama dani bayan ke? Kin sanni fiye da yadda kowa yasan halina, Jalila just recently kika gama gayamin cewar duk tsanani bazaki rabu dani ba, yanzu har anzo tsananin da zaki karya Alƙawarin da kika yi? Duk ƙoƙarin da nake yi ba kya gani? Mene makomar rayuwar mu da ɗan da yake cikin ki idan muka rabu? Anya Jalila kina min son da nake miki?”

Ɗagowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye tace
“Jalal idan har ina maka son gaskiya ne, to zanso in kasance da kai har cikin Aljannah, Jalal bazan so Allah yayi fushi da kai saboda saɓawa iyaye ba, Amma nima nasan tabbas zan shiga mawuyacin hali idan na rabu da kai”
Ta ƙara sa maganar tareda rungume Jalal ta fashe da kuka ta cigaba da cewa
“Jalal nayi wauta abubuwan da nayi maka a baya, Amma dan Allah Mummy tayi haƙuri karta rabani da kai, hukunci mafi tsauri da zata yi min shine rabani da kai, in aka rabamu zuciya ta ba zata iya ɗaukar hukuncin ba ina sonka Jalal, nayi dana sanin abubuwan da nayi maka a baya Amma dan Allah ku yafe min “

Tausayinta ya mamaye ilahirin jikin Jalal, gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi ya ɗago ta suka fuskanci juna yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta

“Babu me raba wannan soyayyar se ubangijin da ya haɗata, lokaci ne Mummy zata yi nadamar abunda ta aikata, Amma kuskure mafi muni a gare ni shine kice zaki rabu dani, Akwai hatsari a cikin aika ta hakan, ki dena kuka kar kisa Baby na cikin damuwa”

“kafi damuwa da Babyn ka dani ko?”

Jalal yace “ni na isa ina sonku gaba ɗaya, ku ɓangare ne me girma a tare da ni, Allah ya raba ku lafiya”

Jalila ta amsa da “Ameen”

Jalal yace “tashi mu tafi gidan mu”

Maƙale kafaɗa tayi tace

“sedai in zaka saimin goba me tsami”

Murmushi yayi yace “shikenan tashi mu tafi”
Ta ɗauki mayafinta suka fito, Suna fitowa Maama tace “zaku tafi ne? Jalila ina da fura zo ki karɓar muku”
Jalila tabi Maama Jalal kuma ya fita.

Maama tace “Jalila shi lamarin Aure haƙuri ake yi, karki ƙara cewa zaki rabu da mijinki akan abunda be kai ya kawo ba”

“Insha Allah Maama bazan ƙara ba”

Tabawa Jalila fura da Nono suka yi Sallama suka tafi.

Daddy kam faɗa ya cigaba da yiwa Mummy, Mummy ta nisa tace
“waini abunda ya bani mamaki shine ya’akayi yarinyar nan tasan Kabiru har tayi sanadiyar zuwan sa prison? Ko dai kuna rainamin hankali ne kawai kaida ɗanka?”

Daddy yace “se kije ki bincika, abunda ya dace kiyi kenan tun farko ba shirme da son zuciya ba”

Daddy beyi mata wani bayani ba ya tashi ya ƙyale ta.

Jalal ba ƙaramin tausayin Jalila yake ba, cikin na wahal da ita ɓangaren Abinci wataran da Asuba haka ze farka ya ganta a zaune tana cin biscuit ko goldenmorn wataran ko brush ba tayi ba, bata laulayi sedai zazzaɓin dare da yawan ciwon ciki.
Jalal ya fara shirin komawa Lagos dan hutunsa tuni ya ƙare, ya ƙara ma sosai, Jalila se rigima take baze tafi ya barta ba, ya rasa inda ze sa ransa se rarrashin ta yake amma fafur taƙi se koke koke take, ta koma masa kamar wata ‘yar ƙaramar yarinya yace “ze tafi da ita Lagos tace ba zata ba makaranta zasu yi final exams”

Saura kwana ɗaya ya tafi, tana kwance a jikin Jalal tana ta zuba shagwaɓa, ya biye mata yana ta rarrashi, Wayar Jalila ce ta fara ringing Jalal ya miƙo mata wayar tasa hannu ta karɓa taga Ummi ce, zumbur ta miƙe zaune ta ɗaga wayar

“Ummi na ya kike?”

“lafiya ƙalau ya me jiki kuma?”

“lafiya ƙalau Ummi, jikin ta da sauƙi”

“Masha Allah dama zamu zone gobe insha Allah”

Tsalle Jalila tayi tana murna “Allah yakawo ku lafiya Ummi na”

Ta ajiye wayar tana tsalle daga wannan kujerar zuwa waccan tana rawa, Jalal kallon ta kawai yake yace “Ayi a hankali dai, kar ki illata min yarona dan Allah”
Zuwa tayi ta zauna kan cinyar sa tace

“Ummi ta fanshe ka mijin so, a tafi Lagos Allah ya kiyaye hanya se an dawo, gobe insha Allah zasu zo”

“Allah ya shirye ki, da su Ummi baza su zoba haka zan ci gaba da fama dake ko, kiyi ta bani wahala?”

Ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjinsa tana dariya tace
“kaifa ranar kace Yaya Jawwad dole ya kula da Hanan tunda ɗansa ne, kaima yanzu tunda naka ne sekayi haƙuri damu”

Dariya Jalal yayi yace “ba kya mantuwa ko? Zaki ramawa Jawwad”

Dariya tayi tace “daɗin ta dai kai ka faɗa ba wani ba”

Washegari da wuri Jalal ya tafi Lagos, su Ummi kuma suka zo da Yamma, Jalila tayi murnar ganin su Ummi, Ummi da mahaifiyar ta da wasu ‘yan uwan ta suka zo, Jalila ta rasa inda zata sa ranta dan murna, tai musu kyakywar tarba da Abincika kala2, Ummi taji daɗin inda Jalila ke zaune kuma ga dukkan alamu Jalila na cikin kwanciyar hankali a gidan Auren ta.
Ummi ta kalli Jalila tace

“Baby wannan ƙiba haka?, kice in fara tara kayan yara, Babyna girma yazo”

Jalila ta kalli cikin ta ta rufe fuska tace “ni bani da komai, sedai in kayan teddy wasa na zaki saiwa”

“hmm kinkusa ɗaukar teddy me rai ai, Allah ya raba ku lafiya”

“in ba da hanjina zamu rabu lafiya ba ni ba komai a cikina”

Ummi tace “Jalila baki da kunya, ko kunya ta ba kyaji ko ni zaki kalla kiyi wa wayo Allah ya shirye ki”

Rufe fuska Jalila tayi tana dariya.

‘yan uwan Ummi basa jin hausa, se yarabanci turanci, da fulatanci kaɗan kaɗan.
Jalila ta sake ta sha hira da Ummi, ta gaya mata halin da ta ke ciki da Mummy, Ummi taita rarrashin ta tana bata haƙuri.
Ƙarfe goma na dare Abba ya turo da mota yace a ɗakko su Ummi, Jalila tayi tayi su Ummi su kwana a gidan ta suka ƙi suka tafi gidan Abba.

Washegari da safe Jalila ta kira Jalal a waya tace masa tana so tabi su Ummi gidan Abba ba ta jin daɗin zaman gida ita kaɗai, Jalal ya batta da safen ta shirya ta tafi gida itama.

Ummi ta shiga duba Mummy, Sam tarbar da Mummy taiwa Ummi bata ji daɗin ta ba amma ta danne ta ƙyaleta.

Kwanan su Ummi uku Jawwad yai waya “Hanan ta haihu ta haifi mace”, Jalila kaman ita akace ta haihu ta dinga murna.

Maama tace “Allah ya raya, saura Nana itama Allah ya raba lafiya Jalila kuwa dama da saura”

Kwanan Hanan biyar da haihuwa Nana ma ta haihu, Itama mace ta haifa, sedai Nana seda aka mata aiki aka ciro yarinyar.

Ba’ayi suna ba seda aka jira Nana ta zo Nigeria, aka shirya gagarumin taron suna a garin Bauchi, sunan Jaririyar Hanan Zainab, ta Nana kuma Ummu Salma sunan Hajiya Salma.

Jalal yayi bajinta shi yayiwa Jarirai abun yanka, banda kyautuka da ya basu, se bayan suna Ummi ta koma garin su.

Jalila tasha labarin labor a gurin Hanan hakan yasa ta ƙara tsorata sosai, Jalal ya ɗakko Jalila suka dawo kano.

Komai ya ƙarewa Ilham, gidajen masu kuɗin unguwarsu take bi tana musu wanke2 da wanki ana biyan ta sannan ta samu na Abinci, gashi yanayin rashin lafiyar mahaifiyar ta da firgitar da take cikin dare yafara taɓa ƙwaƙwalwarta, wani lokacin da rana tsaka ma se taita zabura kaman zata zura da gudu, Abun ya haɗu ya yamutse mata, gaba ɗaya ta koma wata iri ta koma kamar wata tsohuwa gaba ɗaya a firgice take.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button