ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila ciki ya fara tsufa, ta kammala makaranta zata yi service ɗinta a kano, Seda Jalal ya shirya mata walima a gida akaci aka sha ga cikin ta nan yayi girma gwanin sha’awa yayi mata kyau, ‘yan uwa da abokan Arziki sun halarci taron sosai.

Har yanzu Mummy a ƙule take da Jalila, bata sonta sam bata ƙaunar yadda Jalala ke nan nan da Jalila, haka dangin Daddy ma suna matuƙar ƙaunar Jalila tanada kirki ga kyauta, ɓangaren Daddy ma yanzu ya dena ɗaukar abunda Mummy ke masa a baya, duk sati uku yana zuwa ya ganta amma halinta yake sawa yaji baya son zuwa inda take, Hajiya Salma kam tana ta ƙara ƙoƙari gurin ganin ta kyautata wa Daddy, Sosai hawan jini ya taso Mummy a gaba, yanzu ko gani bata yi sosai seda glass hawan jini ya taɓa mata zuciya da kuma ganin ta, ga dukiyar a jibge amma bakomai take iya ci ba, ba ko ina take iya zuwa ba saboda yanayin larurar da take ciki.

Jalal koya tafi Lagos baya iya daɗewa saboda hankalinsa yana kan Jalila, yana tausayin ta bakomai take iyayi ba cikin yayi girma, dan haka ya ɗauke ta ya tafi da ita Lagos yaci gaba da kula da ita.

Wani labari ne ya iske Mummy daga kamfanin Jalal abun ya matuƙar girgiza ta ya ɗaga mata hankali hakan yasa ta kira Jalal a waya tace lallai yazo tana son ganin sa, ya sanar mata yana Lagos tace “lallai ya bar abunda yake yi ya dawo”

“Mummy a ƙarƙashin wasu fa nake aiki, haka akeyi kawai in taho ba tare da izini ba, idan na samu matsala fa?”

“Jalal dole ka bar wannan banzan aikin ka dawo ka kula da dukiyar ka akwai matsala, bazan lamunci abunda ke shirin faruwa akan dukiyar ka ba”

Cikin rashin fahimta Jalal yace “meke shirin faruwa akan dukiyar tawa?”

“idan kazo ka ji”

Comment yayi ƙasa fa ko kun gaji ne, nima se in tafi hutu se kun ganni ????????????????

Share please

07063065680
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

ABDUL JALAL

Story, writing and edited

By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girl)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣3️⃣117

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

          _MY FIRST NOVEL _

Ajiye wayar Jalal yayi tare da dafe kansa yayi shiru, Jalila tace “me yake damunka ne, Ina fatan dai lafiya ko?”

Cikin damuwa yace “Mummy ce ta kirani wai lallai in koma tana son ganina, Akwai abunda taji yana shirin faruwa akan dukiya ta”

“Subhanallah Allah yasa dai lafiya? Yaushe zamu koma kenan?”

“ba inda zani” Jalal ya bata amsa

“Saboda me? Kiran mahaifiyarka ne fa”

“Nasani Jalila nasan akan abunda take magana, indai zan biye wa Mummy bazan taɓa abun Arziki a rayuwa ta ba, shiyasa bana son raɓarta komai nata na son kanta ne”

Jalila cikin sigar rarrashi tace “Jalal me yasa kake me tausasawa ga wasu can bare amma baka iya tausasa wa mahaifiyarka, duk wanda yakamata ya more ka a bayan ta yake, kayi haƙuri da yadda Allah yayi ta ka cigaba da yi mata Addu’a wataran se labari, kai ka ɗai ne ɗan da ta mallaka, be kamata a ce kana mata irin wannan halayen ba”

Kaman ze kuka cike da zuciya da ɓacin rai yace “nika ɗai take dani, kuma nika ɗai take azabtarwa”

“Jalal ya za’ayi mahaifiyar ka ta haife ka sannan kace tana azabtar da kai, baka fahimce ta bane….

” Enough Jalila kidena pretending kaman baki san komai ba mana, Jalila bana jin daɗin Alaƙata da mahaifiya ta, ina kulle kaina inyi kuka da hawaye na saboda rashin soyayya da kulawar mahaifiya, ban san jin ƙai na tsakanin ɗa da uwa ba, kullum tunanin Mummy burin ta kowa ni abu da take hange ya cika, bata tunani makoma ta, duk lokacin da nayi niyyar in shiga jikin mahaifiya ta in bata kulawar da zan iya, se ta bijiromin da wani abu da yake saɓanin tunani, me yasa yaushe Mummy za ta gane inda rayuwa ta dosa,? shi kansa Daddy yanzu bata gaban sa, shekaru talatin da uku yana haƙuri, Jalila har yanzu ina ganin lokacin da mahaifiyar Daddy ke zubar da hawaye saboda halayen mahaifiya ta yaushe Mummy zata canza tunanin ta se yaushe? Yaushe zata gane mutunci da soyayya gaba suke da dukiya? “

Jalal ya ɗau zafi sosai dan har jijiyoyin kansa sun fara miƙewa ya zuciya da yawa.
Ƙara matsowa kusa da shi Jalila tayi tace
“Jalal a duk lokacin da mutane zasu zauna da junansu ba dan Allah bato tabbas wannan zama ba shi da wani amfani, wanda suka zauna da Mummy a baya ba masu ƙaunarta bane, masu son abun hannunta ne, Baka tunanin in kayi haƙuri da ita kai mata biyayya a hankali ta shiryu? Rayuwarmu da mukayi a baya da wadda muke da kai a yanzu misali ce a gareka, Jalal baka da uzuri a gurin ubangiji idan ka mutu kana ɓatawa mahaifiyar ka rai, abubuwan da tayi tsakanin ta da Allah ne, Amma kai zaka yi aikin gyara halayen Mummy idan kaso”

“ta yaya?”

“ta hanyar bata matsayin ta na uwa, ka girmama ta, duk lokacin da tazo da abunda ba dai dai ba ka gyara mata cikin sigar rarrashi, kuma kaga yanzu bata da cikakkiyar lafiya tana buƙatar kulawa Amma kai baka shiga sabgarta Daddy ma ya ƙyaleta dama bata wani jituwa da ‘yan uwan ta me kake tunani ze faru da ita?”.

Haka Jalila ta cigaba da lallaɓa Jalal da yi masa nasiha har ya amince zasu tafi Kano dan yaje yaji neman da Mummy ke masa.

Koda yaje kiran da take masa ba akan komai bane face wasu daga cikin
ma’ aikatansa za suyi ritaya, ya ware wasu maƙudan kuɗi domin ya sallame su, tun yana ƙaramin yaro suke juya masa dukiyarsa sunyi wa kasuwancin sa bauta, dan haka ya ware kuɗi masu yawa akan cewar ze basu, sannan ya bawa kowannen su vacancy na mutum biyu ze ɗauke su aiki, shine Mummy take faɗa akan danme ze bayar da wannan kuɗaɗe masu yawa haka?
Ƙarshe dai haka ya taho ya bar gidan ransa a ɓace tare da dana sanin zuwa gidan da yayi, yana mamakin wannaan hali da zuciya na mahaifiyarsa be san meze sa zuciyar ta tayi laushi ba.

A kwana a tashi tunda cikin Jalila ya shiga wata takwas zuwa tara aka yiwa Jalal ƙarin matsayi akai masa transfer ya dawo kano gaba ɗaya, Jalila tafi kowa farinciki da wannan transfer.
Jalila bata da aiki se ɗora yaran su Nana a status ɗin ta, Jaririyar Hanan kamarta ɗaya da Jawwad Jalila taita tsokanar su da “gidan Jajaye, uwa Ja uba Ja ‘yarsu ma Ja”

Jalal na shan wahala tunda cikin Jalila ya shiga wata tara yau tace nan ciwo gobe tace can, ba ƙaramin tausayin ta yake ji ba, wataran se dare zata tashe shi tace “ita ta kasa bacci” haka zeta faman rarrashi.

Ummi ta gayawa Jalila kayan da zata shirya na haihuwa da alamomin da za taji wanda zata gane naƙuda ne. Gaba ɗaya jikin Jalila yayi sanyi dan tana matuƙar jin tsoron haihuwa sam ta kasa bacci, ga shi a satin nan tana ta fama da ciwon baya da ƙafafuwa, ga ciwon mara da yasa ta gaba ya hana ta bacci sam.
Juyawa tayi ta kalli Jalal yana ta baccin sa ita kam bacci ya ƙauracewa idon ta, tashin Jalal tayi ya kalle ta yace “Baby lafiya kuwa?” kamar zata yi kuka tace
“na kasa bacci fa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button