ABDUL JALAL PART 2

“to kiyi haƙuri zakiyi baccin Insha Allah, ba abunda yake miki ciwo dai ko?”
“Jalal ina jin tsoron haihuwa, Hanan tace min akwai wahala fa”
“haba Jarumar mata, ita Hanan ɗin da suka haihu ba gashi ya wuce kamar ba’ayi ba, kiyi ta ambaton Allah komai zezo da sauƙi Insha Allah, da kinji ciwo kimin magana”
Jinjina masa kai tayi tace “to ɗan kwanta, se in kwanta a bayan ka”
Ya juya ya kwanta ta tada kai da bayan sa, ta ɗora ƙafafuwan ta akan pillow, A hankali yaji tana sauke numfashi alamar tayi bacci.
Ɗan girgiza kai Jalal yayi, lallai mata sun cancanci a girmama su kodan Albarkacin wannan ɗawainiyar da suke yi Allah ka ɗai yasan me suke ji, ko iya tashi da ƙyar da juyi ya ishi abnun tausayi, dan wani lokacin idan tana bacci ya kalli cikin yana ganin yadda cikin yake motsi, Yana wannan tunanin shima baccin ya ɗauke shi.
Juyi Jalal yayi akan gado yaga bata kan gadon ya kunna fitilar ɗakin can ya hango ta durƙushe a gaban gado tana ta haɗa gumi dukda fankar da take ta juyawa a ɗakin amma Jalila gumi take, da sauri ya sakko yana kiran sunan ta.
Kasa magana tayi sedai juya kai a hankali tace “Jalal bayana ze ɓalle”
Riƙota yayi yace “Sannu bari in saka riga mu tafi Asibiti”
A daren ya ɗauki Jalila suka tafi Asibiti, amma koda suka je aka sanar da su labor take yi amma da sauran lokaci.
Ba Jalila ba shi kansa Jalal seda ya ɗan karaya duk wannan wahalar ace da sauran lokaci.
Haka suka kwana a Asibiti, yana ta nafila da Adduoin Allah ya sauke ta lafiya.
Da safe yaje gida ya dafa Abinci da kansa ya kawo mata, tana zaune kaman ba me labor ba.
Zama yayi suna hira ya haɗa tea ya bata tana sha suna hira, wata nurse tace “gaskiya ba haihuwa zakiyi yanzu ba soyayya ma kike yi zaki ci ƙaniyar ki ne”
Jalila dai ba tace komai ba ta cigaba da shan tea ɗinta, Ba yadda Nurses ɗin basu yiba Jalal ya fita ba yaƙi, tana cikin shan tea ɗin tayi jifa da kofin hannun ta, ta riƙe rigar Jalal tana ambaton Allah gaba ɗaya Jalal ya ruɗe da ƙyar ya ƙwace rigarsa duk ta yamutsa ta, tun daga nan Jalila take fama kasancewar haihuwar fari ce.
Jalal ya kira Maama a waya ya sanar mata suna Asibiti, ya kira Hajiya Salma ya gaya mata suyi wa Jalila Addu’a suna Asibiti.
Befi minti Arba’in da wayar da Jalal yayi wa Maama ba tazo Asibitin.
Jalal ya fito harabar Asibitin yana ta kaiwa yana komawa, kallo ɗaya zakayi masa kasan hankalin sa ba’a kwance yake ba.
Suka gaisa da Maama ya rakata ƙofar ɗakin da Jalila take, suna iya juyo Jalila tana ambaton Allah daga inda suke.
Maama taita kwantarwa da Jalal hankali, suka ci gaba dayi mata Addu’a.
Jalila tun karfe biyun dare suke Asibiti se karfe sha ɗayan daren Washegari ta haihu, ta haifi ƙaton jariri namiji su kansu ma’aikatan seda sukayi mamakin girman jaririn.
Seda suka kintsa Jaririn da Jalila tsaf sannan suka sanar da Maama Jalila ta sauka lafiya.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi tare da fadin “Alhamdilillah”
Jalal ta kira a waya tace yazo tana son ganinsa, sam Jalal ko Abinci be iya ci ba, gaba daya tausayin mata ne ya mamaye zuciyar sa be taba zaton mata na shan wahala iirn haka idan zasu haihu ba, ya dauka abun ba wuya.
Yana zuwa Mama ta sanar da shi Jalila ta haihu kasa magana yayi se murnar tareda sauke ajiyar zuciya kafin daga baya yace “Alhamdilillah”
Suka shiga dakin da Jalila take, tana zaune an hada mata tea tana sha, kaman ba itace ta ke ta shan wahala ba.
Jalal ya kalli Jalila yace “Sannu Jalila ya jiki? Ina ne kuma yake miki ciwo?”
Tai murmushi tace “Alhamdilillah ina haihuwa na dena jin ciwon komai”
Maama tace “Sannu Jalila”
Jalal ya karasa gadon Baby ya dakko shi, jaririn kato dashi kaman Jalal yayi kaki ya tofar saboda kamar da suke yi.
Jalal yace “Maama yanzu wannan nawa ne? Ni Allah ya bawa?”
Maama tace “naka ne Jalal, Allah ne yaba ka”
Ya ƙanƙame yaron a kirjinsa ya tafi gadon Jalila ya zauna a gefen ta yace “Masoyiyya kalli waini ni ne da ɗa yau”
Maama ta fita ta basu guri.
Jalila tace “Zaujee ya zama Daddy”
Ya haɗa da jaririn da Jalila ya rungume su yace “Jalila ban taba zaton zan samu wannan Ni’imar ba, Allah ya shiryeni ya bani mace ta gari, yanzu kuma ya bani ɗa, Alhamdilillah”
Jalila ma rungume shi tayi tace “Zaujee kaga wahalar nan dana sha? Watakila Mummy ta sha wahala fiye da wadda na sha a gurin haihuwar ka, shiyasa Annabi salallahu alaihi wassalam yace “abi uwa sau uku sannan yace uba” dan haka zaujee dan Allah ka gyara tsakanin ka da Mummy “
“Jalila ina ƙaunar mahaifiya ta kamar yadda kowace halitta ta keyi, halayen mahaifiya tane bana son zuwa inda take”
Maama ta dawo ɗakin tace “Jalal ya kamata ka tafi gida dare yayi, gobe in Allah ya kaimu in an sallame mu se kazo ka dauke mu”
Da ƙyar Jalal ya yadda ya tafi gida.
Washegari da safe aka sallami su Jalila suka wuce gidan Maama, aka dinga sanar da ‘yan uwa da abokan arziki Jalila ta haihu.
Nan da nan gidan Jalila yafara ciki da mutane, kowa ya ɗauki Yaron nan seya yaba kyansa.
Jalal bewa yaron nan huduba seda Jawwad yazo, yai masa huduba da sunan Jawwad Aliyu Haidar.
‘ yan garin su Mummy sunzo, mutanen Bauchi da Maiduguri ma duk sunzo, Hajiya Salma ma kwana uku da haihuwar tazo, dan taya su Jalila murna, kowa se yaba girma da kyawun jaririn yake, babu wanda yayi zaton Jalal ze samu canjin rayuwa daga tsohuwar Rayuwar da yake a baya.
Ranar suna ƙaton hall Jalal ya kama saboda taron suna, taron Sunan ya tara jama’a masu tarin yawan gaske, akaci aka sha jariri yaci sunan mahaifin Jalila kuma sunan babban Amin Jalal, Jawwad.
Kamar yadda kuka sani dama dangin Jalal Akwai bajinta haka suka dainga yiwa jaririn nan da mahifiyarsa kyautuka, kowane bangare yayi bajinta daidai gwargwado.
Akwatuna Jalal yayiwa Haidar da kuma Jalila ya bata kujera me girma a kamfanin sa, tare da rantsatsiyar motar hawa, (mhmmm Abun manya dai na manya ne) “
Jawwad yaji dadin karar da Jalal yayi masa, nasakawa dansa na fari sunan mahaifin Jalila kuma sunan Jawwad.
Kullum se Jalal yazo gidan Maama dan ganin Jalila da Haidar, Daddy ma ya zazzo ganin Jariri yayi masa Adduoi tare da bashi kyautu ka.
Tunda akayi haihuwar nan Mummy bata taba zuwa taga me aka haifa ba, musamman da taji abunda Jalal yayi, Abun ya damu Jalila matuƙa.
Dan haka da daddare da Jalal yazo ganin Jalila ta saka masa kuka
“Zaujee kwana goma da haihuwa ta, Koba danni ba yakamata Mummy tazo taga jikan ta, Jalal ina cikin matukar damuwa akan lamarin nan”
Jalal yace “Jalila zaki tausayamin idan kika san kuncin da nake ciki na halin ko in kula da mahaifiya ta ke nunawa akan al’amura na, ko baki fada ba dama nayi niyyar insha Allah da kaina zan kaiwa Mummy Haidar, da safe zanzo muje”
Jalal yaita rarrashin ta yana kwantar mata da hankali, Sam Jalal baya kara akan dansa, ji yake kaman ransa yaita kallon Haidar yana cewa “yanzu ni Allah ya bawa ɗa, dukda tarin laifukana a gare shi Alhamdilillah”
Tun daren Jalila take Addu’a tana fargabar me zata tarar in suka je gurin Mummy.
Kamar yadda suka shirya da safe, Jalal yazo ya dauki Haidar Jalila tace Hanan ta raka ta da yake bata koma ba, sukabi bayan Jalal zuwa gidan su.
Suka tarar da Hajiya Salma a gidan da Daddy, Mummy kana kallon ta zaka san ta rame saboda rashin lafiya, Amma har yanzu tana nan da gayun ta, hannun ta yasha lalle Ja, kanta ba ɗan kwali tai parking din gashin ta, wani abu take sha a cup kamar bata san da zaman Daddy da Hajiya Salma a gurin ba se kaɗa ƙafa take abun ta.