ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Daga Alkalamin
Aysher cool ????️????️????️????️????️????️
I don’t want stickers or just thanks, comments nakeso, dan shike bani karfin gwiwa, ina Alfahari daku
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 1️⃣1️⃣64

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

Kallo daya tayi musu ta dauke kanta ta wuce cikin dakinsu, itakanta Maama seda tasha jinin jikinta dan gani take kaman Jalila taji abunda tace, tashi Jawwad yayi ya fice, yayinda Nana da sauri itama ta mike da nufin bin bayan Jalila amma Maama ta hanata, “Ina zaki? Karki sake Kibi ta mayya” haka Nana ta hakura tafasa bin Jalila, Jalila tana shiga dakin tai jifa da jakarta da hijabinta akan gado ta zauna ta fashe da kuka me tsuma zuciya, dama tsanar da Maama take mata harta kai taci mutuncin mahaifinta haka shida baya doron kasar tsawon shekaru, ga kazafi datakeyi wa uwata, menayiwa wannan matar hakane meyasa ta tsaneni, banda albarkacin Abba dasu Nana da matar nan itada zuri’arta suka ganni se sun canza hanya, “zamana a gidan nan baze yuwu ba, bazan cigaba da jure cin zarafin iyayena ba musamman uwata ba dan kawai tubabbiya ce gara inshiga duniya, to amma inna tafi Jalal fa? Tabdijan wallahi matar nan tahana Jawwad aurena bata isa ya auri wata Naja ba, in ita Maaman bata san wacece Najaba to nina sani, Jawwad kuma dan uwana ne, intace baze aureniba baze auri Naja ba wallahi, bazan zauna a kasheni da bakin ciki a biyeba, ta karkashin kasa zan fara ramawa nagaji” “Enough!!!!” Jalila tafada da karfi idonta duk hawaye, guri ta nema ta kwanta hawaye na cigaba da bin gefen idonta to Jalal dinme ma? Nagaji tafiya zanyi sena bar gidan nan wallahi nagaji da wannan abun da akemin, hijab dinta tasaka ta mike. Nasihar ummi ta dinga tunowa wanda take yawan yi mata akan hakuri da rayuwa dakuma karbar kaddara, komawa tayi ta zauna ta fashe da kuka me ban tausayi.
Jiki a sanyaye Jawwad yayi sallar magariba, gaba daya yarasa abunda yake masa dadi, Jalal ne ya shigo dakin da sallama, amma sam Jawwad bejiba hankalinsa baya jikinsa, dafa shi Jalal yayi cikin damuwa yace “Jawwad lafiya kuwa? Meyake damunka kake tunani haka?” Ajiyar zuciya Jawwad yayi, ya danyi shiru na wani lokaci sannan yace “Jalal ina cikin damuwa, narasa meyakamata inyi” “gayamin meya farune?”
Nan Jawwad yagaya masa komai sanna ya dora da cewa “Jalal babban damuwana shine cin zarafin da Maama tayiwa iyayen Jalila ina kyautata zaton Jalila taji abunda Maama tace, amma ban tabbatar ba, data shigo ba wanda ta kula a cikinmu, wallahi bana zaton zan iya auren Naja bazan iyaba wallahi”
Shiruu Jalal yayi, “Jawwad a duk lokacin da aka ci zarafin Ummi, har cikin zuciyata nakeji, raina yana baci, bana manta Alkhairi Jawwad, idan har a matsayinmu na hausawa zamu cugaba da aibata wanda suka karbi Addinin musulinci daga baya to tabbas wanda ba musulmi ba zasu dinga kyamatarmu da addininmu, Jawwad kayi hakuri, amma mahaifiyarka da yan uwanta basa kyautatawa, dukda ina gefe ina fadar rashin kunyar yarinyar nan bazan mata sharri ba tanada matukar biyayya wadda wanda dayawa aka haifa a musulincin basuda ita, kuma itama ai a musulinci aka haifeta, Ummi mace ce me karamci da ilimi riko da Addininta yasa ta baro iyayenta gidan jin dadi dau shekaru ba tareda ta waiwayesu ba, soyayyar datakewa mijinta da yan uwansa ce tasa nima naci Albarkacinku, Jawwad mahaifiyarka bata kyauta ba, kuma zigata akeyi amma kasani gara wanda ya tuba daga baya akan abunda yar mahaifiyarka take aikatawa”da sauri Jawwad ya kalleshi yana kokarin yayi magana, Jalal yace “karka tsananta tambaya dan bazan gayamaka komai ba amma lokaci zenuna komai, mahaifiyarka zatayi nadamar abunda tayi, kayi kokarin ganar da ita, tun kafin tasamu kanta a halin datawa mahaifiyar take ciki, nima da datawa damuwar nazo maka amma bari in kyaleka ka huta, kacigaba dayaimana addu’a kaji dan uwana, banason damuwar ka ina kaunarka dan uwana kadena damuwa” Jalal ya dan daddaki bayan Jalal alamun rarrashi, daga nan ya tashi ya fice.
Jalila yadda taga rana haka taga dare, se tufka da warwara kawai takeyi, gashi tunda ta dawo Nana ko dakin bata shigaba, Maama ta hanata Nana bata kwana a dakin ba a can gurin Maama ta kwanta.
Bangaren Jawwad ma hakane, juyi kawai yakeyi, ya daga waya zs kira Jalika yaga inya kirata ma mezece mata, tunda be tabbatar Jalila taji abunda Maama taceba.
Washegari Sam Jalila bata nuna da wani abu a ranta ba, sedai ko karyawa batayiba ta fita domin tafiya makaranta, a kofar gida tasamu Manu yanata goggoge mota, suka gaisa takoma gefe tana jiransa yagama su tafi, Jalal yana cikin motarsa a kofar gida, zeje wani guri, daga cikin motarsa yana ganin yadda ta rame, da ganin idonta kaman bata samu bacciba ta kwana cikin damuwa, lokaci2 tana goge idonta da handkerchief, Jalila tanada yawan fara’a bata fiye hade raiba, musamman in ta samu abun tsokana, amma yau fuskarta sam babu annuri, setayi kaman wadda ta dade tana jinya, har cikin ranaa seyaji babu dadi ganinta a haka, haka manu ya dauketa ya kaita makaranta.
Hannah abun duniya ya dameta tarasa ta ina zata bullowa lamarin Jalal, amma tanason sanin matsayin Jalila a gurinsa, yazama dole taga Jalila, amma kafin taga Jalila kokuma bari in bari tukuna, amma bari inje gurin wannan garan sena hadu da Jeje, Hannah ta shirya tsaf ta dau mota, ta tafi inda tasan Zata hadu da Jeje, Jeje na ganin Hannah yafara murmushi yana tafa hannun sa “barka da dawowa Gimbiya Hannah” daga masa hannu tayi alamar bata son surutu, guri ta nema ta zauna tana facing din Jeje, Jeje ya rigata magana ta hanyar cewa “dama nasani Hannah zaki dawo, zaki cigaba da aiki damu kin temaki kanki da kika gane hakan, don Jalal baze taba aurenki ba, ni kaina yau rabon da Jalal yazo mashaya ya dade, shiyasa wani shirin muke sakeyi akansa zuwanki a yanzu kinzo akan gaba” “kaga dan Allah kayi shiru kaji meyake tafe dani se surutu kake, kai ka isa inyi magana in janye saboda wani banzan me gidanka baku isaba wallahi ka tsaya ka saurareni, nazone in gaya maka wanda yasa aka dauke Jalal ranar birthday dinsa ba kowa bane face wannan yarinyar data kawo cake” a razane ya kalleta “are you serious?” “sekaje kayi bincike, da bakinta tagayamin haka, sannan kasani in har tana raye to baka isa kuyi nasara akansa ba, seku sake shiri sannan nima bazan bari kuyi nasara akansa ba saboda aurensa zanyi, mataki ya rage ku dauka akan wannan yarinyar, danni nafi karfinku kasani” “Amma hannah……..” kaga ni na riga nagama magana” ta mike ta bar gurin, jinjina kai Jeje ya dingayi yana tuna abunda Jalila tagaya masa daren da yafara ganinta akan Jalal, tabdijan yazama dole ya dau mataki akan yarinyar nan. Yazama dole anjima inje gidansu Jalal da kaina, inbahakaba akwai yuwar wannan yarinyar tamayar mana da aiki baya, bazan bari oga KB yaji wannna zancen ba mara dadi”
Anfito daga exams Jalila tana tafiya kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, daka ganta kasan bata cikin walwala, gani tayi an sha gabanta tana daga ido taga saleema, matsawa tayi da niyyar wucewa, takuma shan gabanta “Ke magana zanyi dake” Jalila ta kalleta “ina jinki” “Kashedi na karshe zanmiki akan Zahrah, ta kawo mana kararki dan haka ba ruwanki da rayuwar da takeso tayi, dan haka kidena mana shishshigi, bake ba zahra” Jalila ta dakko wayarta tana dannawa sannan tacewa Saleema “tsakanin nida zahra wakika haifa da kikemin wannan kashedin?” “haka kikace to kicigaba karki fasa zakiga abunda ze biyo baya”
“bazan dena ba, mekika isa kiyumin meze biyo bayan?” cikeda da gadara saleema tace “Abunda ze biyo bayan abune mafi muni da bakinciki a rayuwarki abu mafi kunya da asara” murmushi Jalila tayi
“shikenan ina jira, nabaki nan da yan kwanaki in har abun da kika fada be faru daniba to ke ze faru akanki, sha3 kawai” binta da kallo Saleema tayi, yayinda itakuma ta wuce, office din sir Hafiz taje, yanata marking, ya kalleta “hmm Gimbiya yar senaga dama se yau kikazo kiran danayi miki” shiru tayi batace komai ba “well ya exams din” “lafiya kalau Alhamdilillah”
“meyake damunkine? Naganki kaman bakida lafiya” “lafiya ta kalau” ta bashi amsa a takaice
Mikewa yayi ya tattare takardun gabansa yasaka a drower yace mata “biyoni” ba musu tabi bayansa, sun danyi tafiya me nisa sannan sukazo bakin wani office, Sir hafiz ya bude kofar yamata alama yace “bisimillah” Jalila ta kalleshi “fara shiga zanbiyoka abaya” murmushi yayi “kina zaton zan cutar dakene anyway biyoni a baya” suka shiga office din, office din babbane sosai ya hadu matuka, se kamshi da sanyin Ac ne ke ratsa ko’ina a cikin office din, kallo daya tayiwa mamallakin office din yana kashingide yana dannan laptop dinsa, sallama sir hafiz yayi, da fara’a wanda ke danna laptop ya dago tareda amsa sallamar, musabiha sukayi da sir hafiz suka gaisa, ita dai Jalila kallonsu kawai takeyi Sir hafiz yace “kalleta ina fatan ita kake nufi” mutumin ya kalleta “eh itace Hafiz nagode sosai Allah yasaka da alkhairi” suka kuma gaisawa sir hafiz ya kalli Jalila yace “to game son ganin naki nan” batace komai ba sir hafiz ya juya ya fice, mutumin ya kalleta “bisimillah ga kujera nan kizauna mana” ya mike ya yaje fridge ya dakko mata ruwa da lemo ya ajiye a gabanta, “wai meyasa kake nemana, ni dai ban sankaba menayi maka” murmushi yayi ki kwantar da hankalinki dolece tasa na nemeki saboda naganki da abunda na dade ina nema ” kallonsa tayi irin ban fahimta ba
“dan Allah a ina kikasan ABDUL JALAL, meye alakarki dashi?” kallonsa tayi cikeda mamaki sannan tace “waye kuma hakan?”
“Naganki a motarsa jiya yakawoki school shiyasa na tambayeki”
“kai mene alakarka dashi?” “Abokina ne, mun dade bamu hadu ba sena ganku tare, shiyasa na tambayeki saboda akwai wani muhimmin abuna a tare da shi?”
“shiya kamata ka tambaya alakar dake tsakanina dashi tunda abokinka ne, kokuma inbaka lambarsa seka tambayeshi” “to shikenan bani lambar tasa” mikewa tsaye Jalila tayi sannan tace “Sena tambayi izininsa tukuna” ta juya tai ficewarta daga office din tana zancen zuci “wannan wane irin abune kawai kawani fara tambayata waimeye alakata dashi mtseww” wata Jalila ta tsayar ta tambayeta sunan me office din, tagaya mata sunanshi malam Sagir Ahmad, Jalila taimata godiya ta tafi,
Koda ta fita tsaki yayi, ya dauki wayarsa, ya dan daddana sannan yasa a kunnensa “hello, ke gaskiya yarinyar nan tanada matukar wayo, taki yadda tacemin komai a game da alakarta Da yayanki” Ajiyar zuciya Ilham tayi “kai duk dabarar naka da iya maganar amma ka kasa” “lallai Ilham, yarinyar tana da lissafi batacemin komai ba akan alakarsu” “shikenan nagode sosai” “yawwa to se anjima” Ilham ta aje wayar ta jinjina kai “shikenan tunda kinki fada, bari in je gurin malam inji meze cemana, Allah ya kaimu goben”
yauma seda Jalila tasa nikab taje dan bare gidan dasu Saleema suke sheke ayarsu, ta tsaya daga waje, maza da mata ba wanda baya zuwa gidan nan, seda ta tabbatar su Saleema suna zuwa gidan nan kuma babu kalar yan iskan da babu. Ta dau lokaci a labe tana kallon masu shiga da fitaa a gidan sannan ta tari abun hawa takoma gida.
Ko a gida ma tunani taitayi, ko Jalal zatayiwa zancen wannan Sageer din cab toma tayaya zan tari wannan jarabbabben da wannan maganar ko ina, tana cikin tunanin ne Nana ta shigo dakin da fara’arta tace “kindawo ashe?” “Eh na dawo Nana” “yaya Jarrabawar” “Alhamdilillah”
“Jalila taso zomuje ankawo sabon order na laces da turaruka, zomuje mu zaba”
“kai Nana wane irin lace kuma? Duk kayan damuke dashi” “to Ai Abba ne yayo waya yace muje” “to bari indakko hijjabina” “kai Jalila ingo mayafin nan dora, banaso wasu su rigamu zuwane a zabe abarmu” Jalila ta karbi mayafin hannun Nana ta yafa, ta kalli Nana “Nana gaskiya mayafin nan yai kadan dubi kayan jikina fa?” “wallahi watakila har muje mu dawo bazamu hadu da kowaba taho kawai” Nana taja hannunta suka tafi gidansu Jalal, Mummy bata babban palour dan haka sukaje part dinta, tana palourn ta tana kallo, Ilham tana kwance tana gyara dogayem faratan ta cikin girmamawa suka gaisheta ta amsa, Ilham bata kulasu ba, Nanace taitayiwa Ilham korafin ta dena nemanta yanzu zumuncinsu ba kamar da ba, nanma Ilham batayi wani responding ba a zuciyarta tace “kina tareda babba makiyata zan dinga sauraranki, taanar danake mata yanzu ai harda ke” Nana tace “Mummy anuna mana kayan mu zaba tun kafin azo a kwashesu” murmushi tayi tace “to hajiya Nana, dankuwa kinsan akwai costumer da Jalila ta hadani dasu sunce zasuzo da sun rigaku zuwa da sun kwashe” Jalila tai murmushi “Mummy ashe har yanzu suna zuwa” “muna hulda sosai suna siyayya a gurina, Jalila maza shiga bedroom dina ki dakkomin mukullaye acikin wardrobe dina, se muje a bude store ku gani” Jalila tana mamakin yadda Mummy batajin komai take turata kan kayanta, Ilham seda ta dago ta kalli Mummy, Mummy ta dauke kai, meyasa Mummy bata yadda da ita akan irin wannan lamuran nata, tsabar haushi Ilham ta tashi takoma baban palour, Jalila taje ta dakko keys, sukaje store suka gama ruwan idonsu suka dauki kaya” Mummy tabiyosu sun fito babban palour sega Daddy ya shigo shima suka gaisa daddy yace “Jalila na kuwa tura Jalal nace masa yace inason ganinki sega faduwa tazo dai2 da zama” murmushi tayi “ai bansaniba Daddy dana zo” yace hakane ya kalli Mummy yace “yan borno zasuzo next weekend Insha Allah”
A razane Mummy ta kalleshi, Ilham ma seda ta tashi zaune, Mummy tace “yan barno kuma? Meza suzo suyi?” “Zumunci mana, dan haka Jalila naga kin iya wannan kayan dadin Abincin naku na yan zamani da irin namu na yan da, dan Allah inban takuramiki ba inaso za’ayimin zamuyi baki ne nasan Madam bazata iya ba ita kadai” Jalila ta dan rusuna “bakomai Daddy Insha Allah ba damuwa za’ayi”
Nana tace “daddy dama Abincin hada wani na kwadayi” murmushi yayi “Eh mana Nana irin naku na zamani ba” Jalila tace “amma wani irin Abincin kakeso ayi musu sannan su nawane”? “Yawwa takwarar son, nagode sosai, yanzu kije gida kiyomin list din Abunda za’a bukata, kiyi musu kawai Abinci me dadi, nasan zasuzo da dan yawa ina jiranki kiyo list din, wanda muke dashi shikenan in babu se a siyo, inkin tashi kizo kiyi anan karki bata muku gida “
“to Daddy bari inje yanzu zan kawo maka Insha Allah”
Su Jalila suna futa Mummy tace “dan Allah dagaske kakeyi koda wasa!”
“daga snake shiyasa ban takuraki nace kiyi musu girkin dazaki karbesu ba gara nasa na waje suyimin tunda ke ba lallai kiyi ba, bayan shekaru yan uwana zasuzo sukawomin ziyara” daga haka ya wuce part dinsa, dafe kai Mummy tayi tanemi guri ta zauna ita kanta Ilham kanta ya kulle,
Jalila tana zuwa gida, ta zauna tayi list din abunda take bukata ta fito domin kaiwa Daddy, amma tundaga kofar gida taci karo da motar Jeje, “Wannan annamimin mayen yazo kenan” tana shiga taga Jalal da Jeje a harabar gidan, suna zaune akan fararen kujeru suna hira, suna shan wata irin taba me girma sosai dan tafi wadda Jalal yake sha girma, zuwa tayi ta wucesu cikin gida, Jeje da kyar ya iya dauke idonsa akan Jalila, saboda karamin mayafine ajikinta gashi doguwar rigarta cif jikinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button