ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Share please

Daga Alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️

I want Comments not stickers or just thanks what’s app only ????????????
07063065680

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE 1️⃣2️⃣65

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

    _MY FIRST NOVEL _

“Waime kake kallo hakane?” Jalal yaima Jeje tsawa cikin inda2 Jeje yace “ohhh am sorry J, nothing, dan samomana kayan washi mana, tunda kwana biyu bamu hadu ba” Jalal yace “to jirani ina zuwa” Jalal ya mike yaje part dinsa ya kawo musu kwalaban giya da wayne cups ya ajiye akan table din”Jeje yace “yauwwa nace meyasa kadena zuwa club, friends nata tambayarka yane? Ga beb dinka Hannah duk tana cikin damuwa irin sosai kagane eh”
“kai bari kawai, haka nan bana son zuwa club din nan, a gida nake dura duk abunda nakeso normal ne ai nan da can” “A’a akwai banbanci, nan ba wasu zafafan mata, bawani sauti me ratsa kunnuwa, kodayake bebs din dake ratsawa a gidan nan naku ma sun isheka kallo, especially wannan zazzafar baby girl din, komai nata me kyaune,” hade rai Jalal yayi, a fusace yace”kamanta kashedin danayi maka abaya ko” Jeje ya sauri yace “ohh No am sorry bazan karaba Insha Allah, yanzu kaga dakkomin wani product din wannan ta isheni, kusan kullum ita nake sha, nasan bazaka rasa na manyan kai ba, dan Allah kabani wani product din” “bazanje ba sedai karka sha” “please am sorry nasan kanada masu tsada dan Allah ka dakkomin” banza Jalal yaiwa Jeje, sekuma can jumawa ya tashi ya tafi dakko masa wata giyar
Jalila ta shiga palour bakowa, Seta jiyo sautin maganar Mummy a bangaren daddy, kaman sa’insa sukeyi, dan girgiza kai Jalila tayi, be kamata taje musu a yanzuba, tana jiyo muryar daddy yana “yan uwanane gurina zasuzo ba gurinki ba, insunzo sedai kibar gidan”
“Amma kamanta abunda yafaru ne? Har kake wannan tunanin?”
“ni ba abunda ya faru tsakanina dasu sedai tsakaninki dasu” Jalila juyawa tayi tafito da sauri dan karma su fito su ganta su gane taji sa’insar da sukeyi. Koda ta fito harzata tafi, ta juyo Jeje cikin wannan muryar tasa mara dadin ji yana cewa “hi beb i like your confidence, akwaiki da fada da cikawa, ” tsayawa tayi cak ba tareda ta juyo ba, yacigaba da cewa “kin fada kuma kincika, kinyi nasarar batamin aikina na wannan rana wanda na dora raina akaki, amma ki saurari hukuncin dakuma abunda ze biyo baya” juyowa tayi ta kalleshi, kawai taga kwalaben giya akan tebur, take taji ranta yabaci koya daddy zeji in yafito yaga dansa yana shan giya a cikin gidansa, shida wani dan iska ta kalli Jeje “ai fada da cikawa baka ga komai ba, se randa sharrin ka yakoma kanka, se ranar dana ga karshenka, asararrae dan wahala, kalle ka sekace karen arna tir da kai da halinka, kuma shi zalunci in abunyine kacigaba, nima bazan gajiba”
“Jalal, shike kama da kare amma ba dainiba shike kama da karnuka, kuma kisa ido, zakiga yadda ze koma ke, zakiga yanda zan maida shi, senacika alkawarin da na daukarwa me gidana, se Jalal ya lalace fiye da tunaninki seya kare rayuwarsa a prison a wulakantacce, ke asuwa naganin bayana karya kikeyi, dukda bangane meye nufinki akansa ba amma zanyi maganinki wallahi, senamiki tabon da harkibar duniya bazaki manta ba”
“Shikenan naji nakuma yadda, koni ko kai duk wanda yasamu dama yaga bayan dan uwansa, sena wulakantaka daga kai har megidannaka, ainasan waye megidannaka zaka gani, banda ai sam Jalal be dace da tarayya da tababbe irinka ba tunda kaikayi sanadiyar yazama haka, ka cutar da rayuwar sa, sannan kacigaba da wargaza masa rayuwa, nikuma zancigaba da bashi kariya dayi masa addu’a har zuwa numfashina na karshe kuma insha Allah seka wulakanta kafin in bar duniya, sanna kasani…….. Shiru tayi ganin Jalal yafito da wata katuwar kwalbar, yaje ya zauna, tana tsaye tana kallonsa ta gefen flours Jeje yaimata wani shu’umin murmushi, Jalal sam be kula da itaba, saboda tana bayan inda yake a zaune, Jeje ya bude giyar ya zuba, sannan ya zubawa Jalal a cup ya mika masa, Jalal ya karba ya kai bakinsa ze sha, Jeje kuma idonsa na kan Jalila, yanaso yaga yadda zatayi da hanzari ta kaaraso inda suke, Jalal ji kawai yayi an kwace kofin hannunsa ta kalli fuskar Jeje ta watsa masa ruwan giyar nan a fuskarshi , gaba daya suka bita da kallo, ta kalli Jeje cikin zafin rai tace “Asararre tababbe mara zuciya, wallahi inbaka ji tsoron Allah ba, mushen jaki seyafi karshenka kyan gani, saboda rashin mutunci a cikin gidan mahaifinsa zaka biyo shi kuyi shaye2” ta kalli Jalal tuni idonta yacika da hawaye “kaima saboda rashin zuciya Jalal mahaifinka na cikin gidan nan kana nan kana sha masa giya a gida, kowane lokaci ze iya fitowa yazeji in yaganka a haka? Memakon ma kuyi a dakinka amma kake shan giya a bainar jama’a ko kunya bakaji, kodayake bakaji kunyar Allah ba sena mutane, bakaji dadin halinka ba wallahi”
Jalal sam ba abunda Jalila tayi bane ya bata masa rai illa irin kallon maitar da Jeje yakemata, ta juya ta hankade tabur din da giyar take kai, suka fadi kwalaben suka fashe, tana kuka tana fadin “Jalal kaji tsoron Allah, Allah ya tsinewa me shanta, da duk me ta’amali da ita, amma giya a cikin gidanku, gidan mahaifinka” ta kalli Jeje “kafita kabar gidan nan, wallahi bantaba tsanar mutum a rayuwataba kamarka, idan na ganka jinake kaman naga shedan natsaneka wallahi, kallon nan danake maka kaman zuciyata ta fashe haka nakeji, in baka bar gurin nan ba sena maka illa da kwalba” ta durkusa tana kuma fasa kwalaben dabasu fashe yadda takeso ba, Jeje ya kalli Jalal “J man, anya yarinyar nan ba mahaukaciya bace ba, kalli fa abunda takeyi” kafin ya rufe bakinsa tafasa hannu da kwalba, da sauri Jeje ya durkusa ze tabata, cikin zafin nama Jalal ya janyeshi, “meye haka kake kokarin yi” Jalila gaba daya ta hargitse kaman mahaukaciyar, Jeje yace “haba J kalli yadda beb din nan takeyi inta illata kanta ba karamar asara za’ayi ba, kallon Jeje yayi,”get out from here” da mamaki ya kalli Jalal “me kake nufi?”
“kafita ka tafi yanzu ka bar gidan nan” “Amma Jalal……
” kafita nace bakaji menaceba ne, kosokake seta illata kanta” Jeje ji yayi gaba daya duniyar tamasa zafi jiyake kaman ya mutu ya huta yau shi Jalal yakewa wannan tsawar saboda mace, ya juya ya fice daga cikin gidan, da sauri Jalal yasa hannu dago Jalila daga durkushen da take, ya jinginata a jikin bango sannan yasa hannunsa ya dafe gefe da gefe, ya kalleta yace “baki da hankali ko?, sekinyiwa kanki Illa tukuna, ji yadda kika yanke hannu meye amfanin hakan da kikeyi ne? Ina ruwanki dani dolene sekin shiga shirgin rayuwata” idonta duk hawaye tai masa wani irin kallo, shima kallonta yayi daga sama har kasa, ya karewa rigar jikinta kallo sannaan ya kalleta
“Idan kika kuma bari naganki da kaya irin wannan sena bata miki rai, sena yaga kayan ko agaban uban waye, sena miki rashin mutincin da bakya tunani” idonta duk yayi ja tace “au yanzun meya hanaka yagamin rigar, tunda baka da hankali, Jalal baka da hankali na fada kuma zan fada ko agaban waye baka da hankali, ai daka sani ga yagamin riga seka tabbatar min lallai giyar daka sha tafara aiki, yanzu kagama cemin ina ruwana da rayuwar ka, nima ina ruwanka datawa rayuwar, kanwarka wace irin shigar ce batayi seni zaka dingayiwa shouting haka, ko tsirara zan tafi ba ruwanka dani, in kafasa yagamin kaya baka kaunar Allah, sannan ka gayawa abokinka zan gauraya dashi, dagani kabani guri in wuce ko in hankadeka akan kwalaban nan, koka mutu banda asara” banza yayi mata ya cigaba da kallonta, “Nine banida hankali ko? “eh baka da hankali, ka matsa in wuce nace ka tsaya kana karemin kallo, duk ka cikani da warin giya, da kaurin hayaki, kaman zanyi amai. Jitayi kaman wani abu yana shanshana mata kafa, dubawatayi taga menene, ihu tayi, ta rungume Jalal tana” wayyo Allah na mene wannan” dubawa Jalal yayi seyaga ashe dan karensa dayake cewa bobby ne kiwata shiyake a part dinsa ya bar kofa a bude shine yafito, karen dan guntune da kadan yafi mage tsayi, ga jikinsa buzu2 da gashi gashi kato sosai amma ba tsawo, daga England daddy yakawo masa shi, Jalila bata taba ganin kare irin wannan ba, kuma batasan dashi a gidan ba.
Ilham se kiran layin Maminta takeyi ta labarta mata abunda yake faruwa a gidan, amma wayar taki shiga ba network, dan haka ta yanke shawarar bari ta fito waje kozata samu network.
Koda bobby yaga Jalila ta tsorata sekara zuwa kusada ita yakeyi, yana shanshana mata kafa, sosai take ihu tana kara shigewa Jalal, hmm dariya ma tabashi tagama zaginsa kuma yanzu abun tsoro yazo ta rirrikeshi, dan haka ya kyaleta Bobby se zagaye mata kafa yake,
“Nashiga uku, Dan Allah a temakeni, wani abu ze cinyemin kafa, waimeye haka bazaka hanashi ba banaso, dan Allah banason mage fa” duk ta yamutsa masa kaya gashi ta goge masa jinin hannunta duk a rigarsa, janyota yayi ya tsayar da ita “meye haka? Kare ne fa kalli” itadai bata taba ganin Kare a haka ba, Jalal ya dago bobby a hannunsa yana nuna mata, aikuwa Bobby yai tsalle yakoma jikinta, ihu takumayi tana nema fita a hayyacinta, tana kokarin cire Bobby a jikinta, dan tsoro yakebata, sosai takuma rike Jalal tana ihu, Jalal ya riketa ya dauke Bobby a jikinta,
Abunda Ilham tagani ne yai matukar tayar mata da hankali, tarasa idonta biyune kokuma mafarki takeyi, Jalila ajikin Jalal, abunda bata taba ganin yayi ba, nan take taji kirjinta ya buga da karfi, tama rasa me zatayi, ta juya takoma cikin gida da gudu. A hankali yacewa Jalila “Nutsu mana is just a dog, ba abunda ze miki, kalli yadda kike nema ki firgita kanki, duk tsiwar taki kalli yadda kika rikice akan kare, seki dagani ai, tunda ba jikin Jawwad bane, jikin makakke ne mara daraja, kokindena kyankyamin gashin jikin nawa” tsaki Jalila tayi ta juya, girgiza kai Jalal yayi, Jalila tai tafiyarta gida.
Nana tazo ta zauna a kusada Jalila tace “Jalila kamshin wani turare kikeyifa” “kamar ya?” “kamar yadda nagaya miki, kamshin me dadi” “turare na dai dayane kuma kinsanshi sekuma me?” “hmmm bakomai, yaushe zamu kai dinkine?” “ko yaushe ne kikaimana, ni har yanzu bamu gama jarrabawa bane” “to shikenan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button