ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Bayan sallar isha’i Jawwad yasa Jalal a gaba yayi salla suka zauna suna hira, Jalal yace “Jawwad ina jin bacci, bari in tafi gida” “No karka tafi yanzu ka tsaya baby zata kawo mana tea, ka tsaya kasha seka tafi” “ok bari in jira, ina son sha, kasan wani abu”
Jawwad yace “A a seka fada” “har yanzu ina mamakin me aka zubamin a giya wanda ya bugar dani haka tsawon lokaci”
Jawwad yai ajiyar zuciya “Jalal shiyasa nake gaya maka tun ba yauba, hulda da mutane irin wannan be kamata ba, kasan wani abu? Jalila ce tasa aka dawo da kai gida, tunda kafita daga gurin nan, ni bansan meyafaru ba, bayan ka bugu tasa manu ya daukeka yakawoka gida” kallon Jawwad ya danyi, ya dan tabe baki irin he don’t care din nan, wayar Jawwad tafara ringing, ya kalli Jalal yace masa “excuse me please” ya daga wayar
“Hello My Jawwad ya kake?”
Muryar Hanan ce, Jalal ya kafe Jawwad da ido, Jawwad yace “ina lafiya Hanan, ya mutan gidan”
“Nifa fushi nake, ashe Jalal yayi birthday bako gayyata ko my Jawwad”
“A a Hanan ba haka bane, Jalila ce ta gayamiki ko?” “A a, wannan ce zata gayamin, bata gayamin ba, hotuna nagani suna yawo a social media, kunyi kyau bama hotonta da Jalal, best couples of the year, kyanta ace wedding pictures ne”
Ba Jawwad ba hatta Jalal dayake gefe yana jinsu seda gabansa ya fadi, amma yarinyar nan ta cuceshi, tarasa dawa zata hadashi se wannan fitsararriyar yarinyar Allah ya kiyaye,
Hanan tace “My Jawwad ya kayi shiru ne” “bakomai Hanan, ni banga hotuna nan ba” “bari in turomaka, zaka gani sunyi kyau, idan birthday na yazo, irinsu zamuyi” Jalal yawani hade rai, Jawwad ya kashe wayar, ya dafe kai “wallahi wannan yarinyar tafi Jalila rigima” Jalal ya dan kalleshi, wa din? Kafadi son ranka dai” “ba son rai bane Jalal, hanan tafi baby rigima, banason Jalila ta gane, zataji ba dadi” dariya Jalal yayi “ganewa ta nawa sedai kar akuma, ai gara Hanan din akan wannan fitsararriyar, gara ta gane din” wani irin kallo Jawwad yai masa, ya cigaba da latsa wayarsa, hotunan da Hanan ta turo masa yake gani, wanda mafi yawa Jalila ce a jiki da Jalal, nan take yaji wani abu yazo ya tsaya masa a rai, Hanan ta turomasa “ya ka gansu, sunyi kyau sosai, sun kuma dace da juna” da sauri Jawwad ya rufe data, ya kashe wayar gaba daya yayi shiru, shikuma Jalal ya nuna ko a jikinsa, kuma yasan shima Jawwad din kishi yake, dan yasan zeji ba dadi, Jalal yai kaman besan wasu hotuna bane, ba a dadeba sega baby Jalila ta kawo musu tea, amma taga Jawwad wani iri, kaman yana cikin damuwa, ta dan kura masa ido tace
“Yaya lafiya dai, yanaganka a haka, kowane abu ne yafaru” girgiza mata kai yayi “Bakomai Jalila” gyda kai tayi, ta tashi ta tafi, Jalal ya zauna ya sha tea dinsa yayinda wanda aka hada tea din dominsa yakasa sha. Bayan Jalal yagama, ya mike abunsa ya tafi gida. Daren ranar da kyar Jawwad yayi bacci, yana matukar son Jalila, meyasa hanan takeson rikita komai ne tana kokarin hada Jalila da Jalal itakuma ta maye gurbin Jalila, sam hakan ba me yuwuwa bane haka ya kwana wannan tunanin. Bangaren Jalila kuma, ta takura kwakwalwarta gun tunanin meye alakar, baban faruk da Jeje, idan har shi yana hulda da mutumin banza kaman Jeje, to mezesa yayiwa Jalal wannan muguwar tsanar haka? Waima yanzu a gurin wa zataji waye Jalal, waze gayamata tarihinsa, Jawwad sam yaki gayamata,sannan meye burin Ilham akansa, meyasa hanna ta bugar dashi haka ranar birthday dinsa? Tarasa me bata amsar wannan tulin tambayoyin, ji tayi kanta yana neman yafara ciwo, dan haka ta hakura da tunanin tayi bacci.
Ya zuba mata ido yana ta kallonta tana shiryawa a gaban mudubi, dan waigowa tayi, ta kalleshi tai masa murmushi “ka dena kallona” “ta yaya zan iya dena kallon ki, kowa yana son abu me kyau, ni kekadaice abu me kyan da idanuna ke iya gani, kinga babu batun dena kallonki” murmushi takumayi masa “hmmm my cwt kenan, to nagama yi maka kwalliyar zo ka daukeni” ba musu ya mike yazo gaban mirror ya tsaya ta miko masa hannu, ya dauketa kaman wata yar baby, ta makalkaleshi tana dariya, ya nufi kan gado da ita, yayinda take kallonsa tana murmushi.
A hankali JALAL ya bude idonsa, yana kallon dakinsa, idonsa ya sauka akan agogo, karfe takwas dai2, se yanzu yagane mafarki yake, wani dogon tsaki yayi, ya tashi zaune “wannan wace irin masifa ce, shikenan kullum babu mafarkin wadda zeyi se wannan yarinyar, shi a yanayin dayake ganinsu ne shida ita yake bashi haushi” tsaki Jalal ya kumayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet, domin yin wanka yai salla “
Karfe tara da rabi, Jalila tana ajinsu, an fara lectures, amma sam hankalinta baya kan malamin, tayi zurfi a cikin tunanin ta, gata a aji amma hankalinta yayi wani gurin, lecturer ya kalleta, cikin tsawa yace mata” Ke! Tunanin me kike haka ina lectures ” a hankali ta dago ido ta kalleshi, ta maida idonta kasa, ba tareda tace masa uffan ba,” ni kikewa wannan kallon ina miki magana, tashi tsaye, seda taja wasu seconds sannan ta mike, “bayanin me nagamayi yanzu?” ta daga ido, suka kalli juna itada malamin, ta dauke kanta tai masa shiru “wai ba magana nake miki ba” still dai shirun takumayi “ok get out from my class” ba musu balle bada hakuri ta dau jakarta, da wayarta ta nufi hanyar fita wasu suna kibashi hakuri, banza tayi musu, malamin yacigaba da mita “irin wannan sune jakan aji, irinsu ke kwasar carry over, se tsabar iskanci waisu yaran masu kudi” “tunda ka koreni kuma gashi na fita kacigaba da yimusu lectures din mana karka shiga lokacin su” tsit ajin yayi ana kallonta, tai ficewarta abunta” mamaki ne yacika daliban, dama tana magana haka, amma Allah yayi mata baiwar murya me dadi, sedai ana tsoron lecturer saboda masifaffe ne, da kyar in bata jawa kanta carry over ba a gurinsa, dan masifaffe ne gashi baya uzuri, yan ajin suka fara gulma, ji yadda take magana da izza, lallai wannan muguwar yar rainin hankali ce, itakam tana fita tasamu guri ta zauna ta cigaba da tunaninta
Siyama ce tafado mata a rai, kwana biyu basuyi waya ba, dan haka ta dakko wayarta ta kirata, bugu biyu Siyama ta dauka
“hajiya Jalila manyan kasa talaka najinku dama”
Jalila tai murmushi “ke banason wulakanci fa, yakike yasu umma?” “duk muna lpy Alhamdilillah, yauba lectures ne naga kin kirani yanzu” “akwai lectures koroni akayi” Siyama tace “hali zanen dutse, har yanzu biki canza ba ko? To university ba secondary school bace, ko islamiyya, Allah sarki malam babba yanata tambayata ke”
“Allah sarki malam, kice masa ina lafiya, ke ba ruwana da wata university, wani hakuri zan bashi ya riga ya koreni, hada wani wai irinmu ne dakikai” “hnm adinga hakuri dai sisy, nace ya mutuminki kuwa?
” waye mutumina kuma? “
” Jalal mana” siyama tabata amsa
Tsaki Jalila tayi “ta yaya yazama mutumina?” “knfi kowa sani, nace yafara shiryuwa kuwa? ” “tab shiriya se ta Allah, dan banga alamaba, abun se addu a, niba wannan ba ma kinsan wani abu” “a a sekin fada” “Siyama hanan ce takeson Yaya Jawwad dina, kuma fa da gaske take” “to meye a ciki, ai abun farincikine” “haba Siyama ya kike fadin haka, da wanine ba yaya Jawwad ba, se in hakura in barmata, amman kaman baki san abunda ke tsakanina da yaya Jawwad ba”
“da kenan abunda ke tsakaninki da Yaya Jawwad, amma yanzu naga kin canza sheka zuwa Jalal” “mtseww, kinfiye wasa Siyama, wannan bugaggen uban me zanyi dashi”
“karki rainamin hankali mana, in bahakaba me yakaiki gurin birthday dinsa kukayi hotuna, hada kallon soyayya” zare ido Jalila tayi “nidin, nasan naje gurin birthday dinsa, amma wani irin kallon soyayya” siyama tai dariya tace “kai Jalila ansan madarar gogewa mutane hadda, to a status din mutane na ganku”
lecturer da yakori Jalila ne ya taho, da wasu dalibai su hudu suna binsa, Jalila tace “hmm ke se anjima, zamuyi waya” ta kashe wayarta, lecturer yazo saitin Jalila ya tsaya ya kalli daliban “kun ganiko, na koreta daga aji, memakon tabani hakuri tazo nan tayi zamanta tana waya da samari, se karshen semester yazo tasamu carry over ace bani da mutunci” ita dai shiru tayi masa, yagama masifarsa yai gaba, wani daga cikin daliban ya dawo da baya yace” yan mata meyasa baki bashi hakuri ba ai ba a haka tunda gaba yake dake seki lallaba a rabu lafiya “
“akan me zan bashi hakuri, yayi kama da wanda za abawa hakuri ya hakura ne? Kuma fa dagani hakurin kuke bashi kowata alfarma kuke nema a gurinsa amma ga yadda yake wani shareku”
“eh to kinsan Jami’ a se hakuri, kowane lecturer da irinsa, kuma ko dan kar ya kadake, ai da kin bashi hakuri ” Jalila ta kalleshi tace
” Yaya na nagode da shawararka amma bazan bashi hakuri ba, kuma koda ban taba zama a lectures dinsa ba banida test banida assignment indai zan shiga exams dinsa sena ci” tana gama fadin haka ta mike, tai tafiyarta. Ji tayi yau makarantar ta isheta dan haka ta kira manu, tace yazo ya maida ita gida , befi minti shabiyar ba sega manu yazo, ya dauketa don tafiya gida, Jalila tace “Manu wai yana ganka haka, kaman mara lafiya” manu yace “ke dai bari Mamace ba lafiya an rubuta mata maganin dubu hudu, kuma ni bani dako sisi, gashi ba adade da biyana albashi ba”
“Allah sarki amma meyasa baka tambayi Abba ba”? “haba Jalila, idan na tambayeshi ai ban kyauta ba, kullum cinkin yimin hidima yake, sedai inkina dashi ki aramin” “Bakomai akwai kudi a account dina muje banki, se mu tsaya in ciro in baka” “kai godiya nake uwar dakina, Allah yasa kifi haka, Allah yabaki miji nagari, ya jikan magabata, Allah ya…
” Ameen nagode, godiyar ta isa haka, yi sauri muje”suna zuwa banki Jalila ta sauka ba layi sosai, dan haka bata wani dade ba ta ciro kudin ta nufo hanyar fita taji ana fadin
” Yan mata adon gari, in baku babu gari, inkunyi yawa gari ya baci, amma kyawawa irinki dazasu cika garin nan, dayakara kawatuwa, barka da wannan lokaci” daga kai tai ta kall
i me maganar, koda tai tozali dame maganar, take gabanta ya fadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button