ABDUL JALAL PART 2

Da magariba Saudat tanata safa da marwa a daki, tarasa meyake mata dadi, khadija zatayi Aure ta batta, gashi khadija tasamu me kudi itakuwa ko oho, ga Salma na wasu maganganu da bata gane kansu ba, “gaskiya yakamata inyi wani Abu, bari inji in Salma na gida gara tamin kwatancen gidanta inje inji komai, sannan inyi fafutukar haduwa da Habib”
Wayarta ta dakko da sauri ta dannan lambar Salma, aiko a fusace Salma ta daga wayar “me kike nema a gurina kuma, kun kwacemin miji, hakan yayi sanadiyar samun sabani da iyayena, kun rabani da farinciki na, shine kika bugo kiji kona mutu ko? To ban mutu ba da raina”
Cikeda mamaki Saudat tace “dan Allah Salma kiyi hakuri bangane mekike nufi ba”
“dole kice baki ganeba, maciya Amana kin hada kai keda yayarki zata Auremin miji, Saudat kurasa wanda zaku cuta seni Habib dina yayarki zata Aura, nagode Saudat karki kara kirana a waya, kuma ko a lahira bana fatan Allah ya hadani da ireiren zuri’arku” Saudat bata karasa gane me Salma take nufi ba, dan kojinta bata gamayi ba, dan tuni ta saki wayar a kasa, kokari take ta tabattar da bacci take kokuma idonta biyu, kaman wadda aka tsinkula tayo waje da sauri daga dakin.
Khadija tana kwance tana wayada Habib
“Hayatee dan Allah kazo inganka mana, tunda satin biki yakama banaganka ba kuma kacenin kadawo daga tafiyar”
“kiyi hakuri Dijart, wallahi Salmace duk ta birkicemin, kuma bata da lafiya dole ina tareda ita kiyi hakuri, Tana bukatar kulawa ta mussaman”
“nibana bukatar kulawarka kenan?
” bahakabane ba deejart, ita daza’ayiwa abokiyar zama tana bukatar rarrashi da kulawa, yawwa nace dama kinsan Salma ne? “
” Meyasa ka tambayeni”
Saudat ce ta fado dakin bako Sallama tayo kan Khadija, da sauri khadija ta tashi zaune ta kashe wayar
“Khadija wane Habib din zaki Aura?
Waye Habib din?” dama khadija tasan wannan ranar zatazo, dan haka ta mike da sauri ta rufe kofar dakin, saboda yan biki sunfara zuwa gidan da mutane, ta dawo ta kalli Saudat tace
“ina jinki, mekike cewa?”
Cikin fada tace “tambayata ma kikeyi? Waye Habib din dazaki aura?”
Cikin dakewa tace “Habib Kamal me Gwal, mijin Salma kawarki shi zan aura” A razane Saudat ta kalleta “ke yanzu khadija bakji kunyar gayamin haka ba, macuciya Azzaluma, na yadda dake kici amanata, mijin kawata, wanda nakeso nazo nagaya miki matsalata, kikace zaki temakamin ashe cuta ta zakiyi khadija, na yadda dake amma kimin haka”
“ke dalla dakata, mekikace mijin kawarki, aigara ace nina aureshi akanki abun kunyar seyafi sauki, ni abun kunya gaba na bashi ba bayaba, kekikace ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba, kema Auren cin amana kikaso kiyi ai, Saudat na dade ina mafarkin Auren miji irin Habib tun ranar da naganshi naji nakamu da sonsa amma abun mamaki, kika rigani gayamin kema kina sonshi, a lokacin nan dana gayamiki ina sonsa nima toda biyu babu za’ayi, shiyasa namiki shiru, na gargadeki da kinemi wani karki tsaya jiran Habib amma kimayi bris dani, kisani mutuwa ce kadai zata iya hana Auren nan, duk wani shige da fice dazakiyi a yanzu aikin gama ya gama baki isa kiyi komai ba, dan ba karamin shiri nayi ba”
Fashewa da kuka Saudat tayi tace “khadija da tun farko kin sanardani kina son Habib, dazan iya barmiki shi, da ban wahal da kaina haka ba, amma kika bari na dinga lalube kina rainamin hankali, tun tasowarmu kaf cikin yan uwana uwa daya uba daya dake na yadda, amma kinmin cutarwa mafi muni khadija!!!! Kinsa na zubda hawaye kin bakantamin rai kinmin tabo me muni da bazan manta ba, kin kwace abunda na kallafa raina aki, shikenan ki shirya ki rubuta ki Ajiye idan harni Saudat yar halak ce haihuwar uwa da uba, wallahi senamiki mummunan tabo kema ki Auri Habib ga daula nan kinsamu, amma ki saurar zakiga nima abunda zan iya” ta juya da sauri fuskarta duk hawaye zatayi waje khadija ta rikota, karo na farko dataji tausayin Saudat amma ta basar tace
“Saudat ki fawwalawa Allah lamarinki, kiyi wanka da fetur, sannan ki hau risho da wandon leda yafimiki sauki akan hana Auren nan, kisawa zuciyarki salama kibi a sannu kema sekiga kin samu ko wanda be karasa Habib bane, kinfi kowa sanin hatsarina karkije garin daukar fansa kikuma ruftawa wani tarkon wanda bazanso hakan ba, har yanzu ina kaunarki yar uwata, kar abunda nayu miki ya shafi zumunci da kaunar dake tsakaninmu”
Fizge hanunta tayi da karfi ta bude dakin ta fice, Ajiyar zuciya khadija tayi ta koma ta zauna tayi murmushi tace “Saudat kenan, na dade ina ankarar dake amma baki gane ba, naciki wasa se hakuri”
Tundaga lokacin nan Saudat tafara rashin lafiya har akayi gama bikin khadija, tarasa nutsuwarta gaba daya, banda tunani babu abunda take, so take ta samu hanyar dazata turawa khadija bacin rai dan ta huce, tarasa mezatayi danta huce, kasa samun mafitane yasata takara shiga damuwa da halin rashin lafiya, yayinda khadija ko a jikinta hidimar bikinta kawai takeyi, anyi hidima sosai a bikin khadija anci an sha, anyi watsi da nera yadda yakamata.
Kabir yashiga matsanciyar damuwa gameda Auren khadija, yayi kuka, yayi kukaba adadi, ga fushi da mahifiyarsa keyi dashi, ga basussukan mutane saboda yadda yakecin bashi yana kashewa khadija, gaba daya duniya tayimasa zafi, yarasa meyake masa dadi.
Tunda Allah yasa khadija ta shiga gidan Habib komai yafara rushewa, gaba daya hankalin Habib yakoma kanta, Salma dama bata da surutu, khadija tafita baki, dan haka ta shiga hadasu fada, dama khadija bata kaunar dangin Habib tunda taji labarin basa son Aurenta, da Habib baya wata guda cikakke beje maiduguri ba amma tunda ya auri khadija seyayi watanni bejeba, Salma sedai ta zauna tasha kuka, ya shirya musu tafiyar wata daya Dubai shida Salma da khadija, Salma tace bazataba, ya dauki khadija suka tafi basu dawoba seda sukayi wata uku, gaba daya Salma ta zubawa sarautar Allah ido.
Idan yan uwan Habib sukazo gidan ta dinga rashin mutunci kenan tana habaici
Tunda taje dakin miji Saudat bata taba zuwa gidanta ba balle takirata a waya, hakazalika seda ta shekara guda cif sannan ta yadda tabi Habib maiduguri ta gaida mahaifiyarsa, tunda mahaifiyar Habib taga khadija taji sam bata kwanta mata ba dan sam babu alamar kunya ko kara a tareda ita, tunda ya aureta shekara guda sannan tazo ta gaishesu. Ta lura khadija a tsaye take ga Salma ta rame matuka tayi duhu, dan bata gayawa kowa meyake damunta, kota fada ba a goya mata baya sedai ace tayi hakuri kishine ke damunta.
Maman Habib ta kirashi dakinta, ta dinga masa fada, akan yadinga adalci tsakanin matansa, in bahakaba seyayu danasani, dan taga alamun wannan tsagerar daya aura kamar suna cutarda Salma, dan ita sam wannan yarinyar batayi mata ba, banda rashin mutunci shekara guda da aure sannan sukazo yakawota gida sugaisheta shi kansa ya canza gaba daya,
Haka yaita bata hakuri, yace insha Allah ze gyara amna yana kokarin yimusu adalci.
da kyar khadija ta hakura ta kwana biyu a garin tace ita ya maida ita gida ta fuskanci danginsa basa kaunarta.
Watan khadija biyar a gidan ta fuskanci tanada ciki, koda tagayawa Habib yayi murna matuka, tunda ya auri Salma shekara biyu kan na uku amma bata taba ko batan wata ba, sunje Asibiti ance lafiyarta kalau, dan haka yayi murna da wannan cikin
“Habib kadena murna da wannan cikin zubar dashi zanyi wallahi!”
Cike da mamaki ya dubeta “kamarya ya? Ina neman abu in samu kice zaki zubar khadija why?”
“ban shirya haihuwa yanzu ba wallahi, da kuruciyata bazan tsufa ba wahalar yaya ta kasheni ba, tun kafin muyi Aure kasan burina inason yin karatu me zurfi a kasar waje, tayaya zanyi karatu da ciki, kwata2 yaushe nayi Auren zanyi ciki, wallahi sena zubar”
“khadija kiyimin rai dan girman Allah kiyi hakuri, kibari ki haifamin cikin nan seki tafi karatun”
“sekuma kayi, in kanason cikinka seka dauka ka maida shi jikinka ka haifa, amma indai a jikinane bazezo duniya ba gara ka hakura inkun matsu kaje kaimata cikin ta haifa maka”
Saroro yayi yana kallonta, ba kunya take gasa masa wannna maganganun.