ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Tabdijan da alama Habib ya debota da zafi sunan baban Salma fa yasakawa dan khadija.

A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu ‘oinku
Sannaan masu rokon adinga posting a Facebook insha Allah za’ a fara posting din Littafin ABDUL JALAL Facebook tundaga farko
Insha Allah, za’afara posting a group din
AISHA HUMAIRA NOVEL FANS (Daddy’s girl) dakuma sauran groups nagode sosai ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 2️⃣3️⃣76

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

          _MY FIRST NOVEL_

Saudat ta danyi shiru sannan tace “kumafa hakane amma tayaya kenan?”
“bari muje gida zan gayamiki meyakamata kiyi”

Watarana Khadija ta shirya da dauki Jalal taje gidansu, suka wuni acan se magariba suka koma gida a hanyarsu takomawa ta hadu da Kabir, amma ta dauke kanta kaman bata sanshiba ta zuge glass din motarta tai tafiyarta, Kabir yayi mamakin girman motar da khadija take ja, kana ganinta zaka san tana cikin daula da jin dadi, gefe ga danta kaman ba dan hausawa ba kyakyawa dashi. Taja motarta tabar gurin ya dubi shikuma irin rayuwar dayakeyi ta wahala, ya gyada kai yace “wallahi khadija senayi silar kin fito daga wannan daular dan bazaki yaudareni a banza ba”
Haka Rayuwa tacigaba da gara Kabir wanda hakan yasa yafara shaye2 miyagun kwayoyi.

Bayan Rabuwar Salma da Habib an takuramata a gida akan lallai setayi Aure, wani Ambassador yafito yana sonta, akayi bikinsu, abun Allah ko wata guda batayi a gidansa ba Allah yasa ta samu ciki, Masoya da yan uwa sun tayata murna sosai har Allah yasa ta sauke lafiya ta haifi namiji akasamasa Mahmud, bayan mahmud ta haifi Yusuf da Yasmin, Mahmud shine wanda mukazo dashi, zakiga yana kama da Jalal. Amma Allah yayiwa Ambassador Ahmad Rasuwa shekaru biyar dasuka wuce. Dan haka tai zamanta a England.

Khadija ta karbi makudan kudi a hannun Habib tafara kasuwanci, tana zuwa kasashe daban2 tayi sarin kaya ta sayar, tana da manyan shaguna a fadin kasar nan, wanda dukkansu mallakinta ne.
Saudat ta haifi diya mace, bayan danta munir, wadda itace Ilham, khadija taita zaryar Asibiti akan tanason takuma samun ciki, amma abu ya gagara har wasu kasashen sukaje da Habib amma aka sanar matada bazata kara samun ciki ba, Mahaifarta tasamu matsala sakamakon rauni datayi saboda yawan shan abortion pills datai tayi, khadija ta damu sosai har tagaji ta hakura.
Saudat ta nunawa khadija komai ya wuce, Khadija ta dinga mata barin kudi baji ba gani, Khadija tagayawa Saudat halin da take ciki
“Saudat naso ace nakuma samun haihuwa, ko mace in haifa, Jalal yasamu dan uwa”
“tunda Allah yabaki Jalal dinma ai ki gode masa, dan wani har ya mutu bazega kwansa a duniya ba”
Gefe guda Saudat tayi farinciki jin cewa khadija bazata kuma haihuwa ba, hakan yasa takara kudurcewa ranta seta Rama abunda Khadija tayi mata akan Jalal.

Ummi ta dade bata haihu ba, sunyi girma lokacin da Allah yabata haihuwa, Tunda Allah yasa Ummi ta haifi yarinya mace, hakan yakara saka Jalal zaunewa a gidansu Jawwad, kullum suna tare suna Rainon Kanwarsu, Jalal yaitabin Uncle Aliyu kanin mahaifin Jawwad yana cemasa dan Allah asakawa jaririyar nan sunansa wato Jalal. Aliyu yabiye masa yace Jalal sunan mazane amma insha Allah zanmaka takwara, karka damu, Ranar Suna yasamata Jalila, yace yayiwa Jalal takwara, Habib yaji dadin karar da Aliyu yai masa, yadda suke nunawa dansa soda kauna, duk rikicin da Jalila takeyi intaji muryar Jalal yanzu zata fara murna, gaba daya Jalal jiyake Jawwad da danginsa sune komai nasa.
Fafur khadija tahana adinga kai Jalal dangin mahaifinsa, acewarta tunda basa kaunarta danta ma basonshi suke ba, Amma a haka Habib yake zuwa yakaishi ko a ranar ne su juyo, duk dangin Habib sunsan Jawwad, Jawwad yanajin yaren kanuri kaman yadda Jalal ma yafara jin fulatanci saboda kauna da shakuwa.
Jalila na karama sosai Mahaifinta yanemi Aiki a garin kaduna yatafi da Ummi da Jalila, saboda yawan tsangwama da iyalannasa ke fuskanta, dukda lokacin Jalal da girmansa yashiga secondary, amma haka ya dinga rikici yana kuka, Shi be yadda a tafi da Jalila ba ya saba da ita. Tare yake cin Abinci da ita, komai yagani na wasa se yace ita ze kaiwa, komai yaci seya ajiye nata. Jalal ya dade yana damuwa akan barin gari da uncle Aliyu sukayi, Abun har yafara bawa khadija haushi, yadda ya tashi hankalinsa akan wanda ba dangin iya ba na baba sun bar gari. Ummin Jalila seda tayi kuka lokacin dazata bar kano, saboda ta riga ta shaku da yaranta Jalal da Jawwad
Bisa ga Shawarar zulaiha, Saudat seta dakko Ilham tace ga Ilham nan tabawa khadija ta dinga debewa Jalal kewa ze manta da waccan yarinyar, khadija tayi murna da wannan kyauta da Saudat tayi mata, lokacin Ilham nada shekara takwas khadija ta karbeta, amma sam Ilham basa shiri da Jalal dan sam bata da kunya shikuma ga son girma, dan haka har dukanta yake, Jawwad yaita masa fada yace Ilham kaman Jalila takefa itama kanwarmuce, Jalal yace “Jalila ba mara kunya bace, ni Jalila ce kawai kanwata ba wannan ba”

Har yanzu khadija bata fasa yawace2 kasuwanci ba, Jalal ya tashine a tsakanin kwararo ba bu shakuwar uwa a tareda shi, Allah ne ya dubi Jalal ya hadashi da mutanene kirki irin dangin Jawwad.

Jalal yanada matukar kwakwalwa, sarrafa abu da haddace shi baya masa wahala, dan suna Jss2 suka Sauke Al’qur’ani, suka juya hadda, wanda wannan nasara tasu da taimakon Allah da taimakon Ummine da mijinta, Saboda itake tsayawa taga sun iya dukkan wani karatu dasuka koyo a makaranta, sunyi nisa sosai a haddarsu dan sunkai izufi Arba’in Rayuwar Jalal tafara samun matsala, Jalal yana SS2 a secondary komai nasa yafara lalacewa, sakamakon haduwa da miyagun abokai dayafarayi, Jalal yanada kyauta ga faran faran da mutane, ba babba ba yaro kowa nasane, duk wanda yakeda bukata Jalal ze dauka yai masa, hakan yasa har manya suka fara girmama shi suna gaisheshi.
Jalal lokaci daya ya canza watarana khadija bata kasa tana can harkar kasuwancinta daga Daddy se Jawwad da Jalal a gidan Ilham kuma tana gidansu, ‘yan fashi suka shigo cikin dare, suka kama masu gadi suka kullesu, suka shiga cikin gidan, Habib yace su dauki duk abunda sukeso a gidan amma karsu taba masa yaransa, suka sakasu kneel down, sannan tattara abunda suka samu a gidan har zasu tafi dayan ya juyo ya saita Habib da bindiga, gaba daya yaran suka fara kuka, dan fashin ya musu tsawa amma suka ki yin shiru, dan fashin ya saita Jawwad yace “bari in kashe tilon dannaka dan yafiye maka komai a duniya kuma da alama yana sonka sosai” zatonsu shine Jalal, dan haka ya saita Jawwad da bindiga, Habib yace dan Allah karku kashemin shi, gaba daya yaranane, tunda kun samu abunda kuke so dan Allah ku kyalesu garani kukasheni, dan fashin nan yamasa banza ya dan kunamar bindigarsa, kawai Jalal ya mike tsaye, bullet din ya shigeshi a gefen kirjinsa, yan fashin na ganin haka, suka kwashi abunda suka kwasa suka gudu. A gigice Habib da Jawwad sukayi kan Jalal amma yana kwance kaman ba rai jini nata malala a kirjinsa, hakan ya firgita Jawwad kwarai shima ya suma a gurin, misalin karfe uku na dare haka ya daukesu ya tafi dasu Asibiti.
Da kyar aka cire bullet din a kirjin Jalal, ya galabaita saboda a gefem zuciyarsa bullet din yasameshi, shima Jawwad da kyar aka samu ya farka. Wannan fashi ana kyautata zaton dasa Hannun Kabir a ciki, amma ba’a tabattar da hakan ba. Seda Habib ya kai su Jawwad Dubai aka dubasu acam sannan hankalinsa ya kwanta, seda akayi kwanaki sannan khadija tasan meyafaru.
Akaita zuwa duba Jalal, Allah yatemakshi ba’a dadeba ya warke suka koma makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button