ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Tunda yan maiduguri suka tafi Jalila bata kara saka Jalal a idonta ba dan sam yadena zuwa gidansu, ga Jawwad yanata complain akan Jalal bayacin Abinci yana damun kansa sosai, ga matsalar da Jawwad yake ciki shima Maama nata tursasa shi tace se ya Auri Naja, amma ita Nana ta tirje tace bazata Auri faruk ba an kyaleta, Jalila tarasa yadda zatayi taga Jalal, duk abun yafara damunta. Ga yaya Jawwad dinma ta dena ganinsa ko waya basa yi, yadena shigowa cikin gida. Zaman cikin gida ya isheta dan haka ta fito danta sha iska, ta fito ba dadewa Jawwad ya shigo yayi parking, duk taga ya dan rame, yafito ya kulle motar, takarasa inda yake “Yaya Jawwad wai meyake damunka hakane, ka rame kuma tun shekaranjiya ban kuma ganinka ba” cike da damuwa yace mata “Baby Jalal, yana nema ya kashe kansa”
“Kamar yaya?”
“Ankuma kwantar dashi a Asibiti, tun shekaranjiya ina can, banason inkira Daddy kar adaga masa hankali, idan Mummy taje gurinsa, seyace seta tafi bayason ganinta yanzu haka jikinsa yakuma rikicewa, yanzu haka tun jiya yana ICU, maybe yau zasu fito dashi” nan da nan jikinta ya hau rawa, cikin rawar murya tace
“Subhanallah Allah yabashi lafiya, if you don’t mind zan rakaka in dubashi”
“Shikenan naji amma kibari seda safe in Allah ya kaimu zanzo muje” ta jinjina masa kai takoma cikin gida

Yau Hannah har gidan Jeje taje nemansa tayi sa’a kuwa yana nan, Jeje yayi mamakin ganinta sosai “yau kece da kanki a gidana”
“Eh nice amma kasan duk lokacin daka ganni bukatace ta kawoni, almost one week ina nemanka, bana ganinka layinka baya shiga, amma naji ana rumors ankamaka kai da megidanka a gidan karuwai meye gaskiyar lamari” shiru Jeje ya danyi ya kalli Hanna
“Ni ina zargin dasa Hannunki akan abunda yafaru dani, shekara da shekaru inawa Oga Kb aiki inasamun rufin Asiri a gurinsa, ina hutawa da ‘yarsa ba tareda yasani ba lokaci daya aka masa cunen gidan danake zuwa yakamamu, yanzu ya sallameni tareda cin alwashin seyaga bayana, wallahi Hannah indai dasa hannunki a wanna cin zarafin da’ akamin bazaki tsira daga sharri na ba”
Murmushi Hanna tayi sannan tace “Aidama karshen alwa kasa, kuma ramin mugunta kurarrene, Jeje idan har zanmaka wannan manakisar yan sanda suka maka kaida uban gidanka to wallahi da duk yadda zanyi bazaka fita daga hannun yan sanda ba daga kai harshi, dara ce taci gida kawai, kakoma kayi tunani ka sake nazari waze iya aikata maka haka, kasan innice nayi maka wannan aikin bazanji tsoron gayamaka bako? tunda irin tarbar danasamu daga gurinka kenan shikenan nagode ni na tafi, amma kakiyaye shiga hanyata, kasanni ban da kyau”
tanagama fadin haka ta juya tanufi motarta, yayi Yunkurin ya biyota amma ta tashi motar tabar gurin.
Yauma Jalila ba bacci, saboda tashin hankali da damuwa, se addu’a da takeyi, Nana kam ta gaji da tambayar ta meyake damunta. Da Asuba Jalila tai wanka tai salla ta shiga kitchen ta dama kunun gyda da dankalin turawa, karfe bakwai tagama shiryawa tsaf tana jiran Jawwad, Nana tai juyi akan gado ta kalli Jalila
“wai shirin mekikeyi hakane?”
“Asibiti zan raka Yaya Jawwad muduba Yaya Jalal” dan zaro ido Nana tayi, sannan tai murmushi
“Yaukuma da kanki kike cewa Yaya Jalal” takuma murmushi tace “Zanso inje nima induba shi, amma wallahi bacci nakeji, kuyi masa sannu in an sallamoshi naje in duba shi, kokuma in Maama zata semuje tare” Nana ta juya tashige bargo, Jalila na nan zaune, wajejen karfe takwas Jawwad yakirata a waya yace tafito su tafi, da sauri ta dakko kwandon kayan Abincin ta fito, Jawwad ya kalleta yace “Baby hada hidima haka, Abinci kika mana”
“Eh Yaya, koba kwaso?”
“haba mu mun isa, taho mutafi” ta shiga mota suka tafi, suna zuwa Jawwad yaimata jagora har dakin da Jalal yake, suka tura kofa suka shiga ta tsorata da ganin Jalal, yana kwance akan gado dagashi se dogon wando da singlet, yanata sauke numfashi a hankali, ya rame matuka gashi yayi duhu se dogon hancinsa yakara fitowa sosai, drip yana shiga jikinsa a hankali, hawaye yafara bin idon Jalila a ranta tace “idan har Jalal ya mutu ina da alhaki, ninakara assasa bata masa rai”
Jawwad ya dora hannunsa akan gadon da Jalal yake ya sunkuyar da kai, Yana dago ido Jalila taga kwalla a kwance a idonsa
“Yaya karka karaya mana, zeji sauki” Jawwad yai murmushi yace “Baby Jalal wani bangarene na rayuwata, inajinsa a raina kaman wani bangare na rayuwata, banason rasashi, banason wani abu yasameshi da inada yadda zanyi in kawar masa da damuwarsa, danayi amma ba yadda na iya kaddara tariga fata, haka Allah ya kaddara masa, ina fatan Allah ya musanya masa da kyakyawar kaddara ” Jawwad yai ajiyar zuciya yace “Bari inje gurin doctor inji meze ce, kizauna anan anjima su Ilham zasuzo nima yanzu zan dawo, inkuma ya tashi kafin in dawo kikirani beci Abinci ba” ta jinjina kai, Jawwad yafita yabar dakin guri ta samu ta zauna akan kujerar gaban gadon Jalal, Hawaye tacigaba da sharewa lokaci zuwa lokaci tana dorawa kanta alhakin wannan rashin lafiyar da yake,
A hankali Jalal yai juyi, da sauri ta goge idonta ta tsaya tana kallonsa bude idonsa yayi a hankali ya saukesu akan Jalila dake goge hawaye, kura mata ido yayi ko kyaftawa ba yayi.

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.

???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 2️⃣5️⃣78

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

          _MY FIRST NOVEL_

Ya dau lokaci yana kallon ta, cikin rawar murya Jalila tace “Sannu ya jiki?” shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa, “Ko inkira maka Jawwad” still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi “Inkira maka likitane” takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta “Kukan mekikeyi? Nakumamiki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?”
Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace “kidenamin kuka, nagaya miki kincikamin kunne”
“Yi hakuri na dena” tasa hannu ta share hawayenta, Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace “Sannu ya jikin naka?”
“Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni” murmushi likitan yayi sannan yace “kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma dawo da kai Rai a hannun Allah”
Jawwad yace “rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza’a sallameshi ba seya warke gaba daya”
Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace “Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi” Sannan likitan ya kalli Jalal yace “Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni”‘imar ubangiji meze daga maka hankali haka? ” kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa ” Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo’in ciwon ido dake sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic ” shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace “Shikenan doctor za’a kiyaye Insha Allah”
“Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki” doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace “Kaji abunda doctor yace ko? Please and please kakiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa” Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace “Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin”
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace “Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba”
Jalila tace “Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye” takarasa maganar tana dan tura baki, Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace “itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin” Jawwad ya mike ya fita, Jawwad na fita Jalal yai kokarin komawa ya kwanta beci Abincin ba da sauri Jalila tace “Ai bakaci Abincin ba” ya kalleta “Bazanci ba” yakuma kokarin kwanciya Abincin ta dauka ta dora a inda ze kwanta tace “wai meyasa kafiye taurin kaine? Cewa fa akayi kaci Abinci”
“Ke har na kaiki taurin kaine? Waima ina ruwanki danine? Dan giya, mara tarbiyya, zan lalata miki dan uwa, me kike nema a gurina, dauke Abincin ki bazan ciba, kintaba gayamin idan na mutu bakida Asara to meye naki na damuwa da banci Abinci ba?” yasa hannu ya dauke Abincin ya dora akan drower na kusa da gadon sannan yace “Dama a duniya daga daddy se Jawwad ne suke sona se yan uwan daddy, nan duniya idan na mutu ba wanda yakeda Asara, sesu”
kura masa ido tayi “Meye kuma kike kwalalamin idanuwa haka, kidena kallona” yai kwanciyar sa.
Kawai Jalila ta mike ta fice daga dakin, Ajiyar zuciya Jalal yayi dayaga ta fita ya dakko Abincin data zuba ya ci ya aje sauran. Jalila na fita tasamu guri ta zauna a waje ta dakko wayarta tafara chatting tana daga kai ta hango Ilham da mahaifiyarta a harabar Asibitin kallo daya tayiwa Saudat tagane itace mahaifiyar Ilham,
da sauri Jalila ta tashi ta koma dakin Jalal, tana zuwa taga yaci Abincin yana kashingide ya lumshe ido, yana jin motsinta ya bude ido,
“Ke meya dawo dake, ko dama bakida zuciya?” cikin tsiwa tace
“dama ina naga zuciya, tunda kaima bakada ita”
Dan zare ido yayi, ashe halin nata yana nan
Ta fara hada kan kwanuka, Ilham ce da Mamanta suka shigo da sallama yanajin muryarsu yai Sauri ya rufe idonsa. Kai kace bacci yake, Tunda Ilham taga Jalila a gurin Jalal ta hade rai kaman taga kashi
Jalila ta maze tace “Sannunku da zuwa” yawwa maman Ilham ta amsamata, tabasu guri suka zauna Ilham se harar Jalila take, ita kam Jalila data kalli Ilham seta mata murmushi Maman Ilham tace “Yame jiki?”
“da sauki Mama”
“naga alamar kaman yana bacci ne ko?”
Jalila ta waiga ta kalleshi yawani rufe ido kaman gaske amma idonsa biyu, se Jalila ta kudurce wani abu a ranta dan haka Jalila tace “
eh likita yamasa Allurai yasamu bacci, likita yace baze farka ba se bayan Awa biyar, yanzu besan me ake ba”
Maman Ilham ta kalli Jalila tace
” Sedai bangane wannan ba, bakowa a gurinsa seke? ko itama a dangin babanasa take?”
Ilham tai farat tace “Inafa,” yar shishshigi yar wahala dai, me hana ruwa gudu, me cusa kanta inda Allah be kaita ba” Jalila tace “haba Ilham, wani ma se yazata banida kirki, menamiki haka ina laifin kice, Sauro me hana giwa bacci, Raina kama kaga Gayya” Jalila ta karasa maganar tana murmushi tace “Mama bari in saka wayata a caji, in karbo muku ruwa a waje” Jalila ta mike ta dau wayarta ta dan daddana sannan tasaka ta a caji ta fita. Ba’a wani dade ba, Jalila ta turo kofa ta shigo da ruwan roba ta ajiye musu ko sha basuyi ba suka tashi sukace tafiya zasuyi. Tai musu sallama suka mata banza Ilham nata gaya mata bakaken maganganu bata damu ba suna fita taje ta dauki wayarta ta bude, maganganun dasukayi tsaf tayi recording dinsa tai Saving tajuya ta hada kan kwanukan da Jalal yaci Abinci, bude idonsa yayi yana kallon ta tana dagowa suka hada ido
“Akwai matsala ne?” Jalila ta tambayeshi
“Wani Apple kika hanani ci kika musanya ranar da mukayi baki?” tambayar tazo mata a bazata, ta dan tabe baki sannan tace “Apple kuma ni ban san zancen ba”
“Karya kikeyi” Hade rai tayi sosai
“Eh kasan na saba” tacigaba da abunda take, ko ina yasan wannam maganar oho masa, ta mike tsaye taji ya janyo ta da karfi kan gadon, take jikinta ya hau rawa ta tsorata sosai ta ware ido tana kallon sa
“Ina tambayar ki kina rainamin hankali wani Apple kika hanani ci, kuma meyasa?”
“ni nace maka ban san zancen ba, ka tambayi wanda suka gayamaka mana, ni kacikani” kara karfin rikon yayi taji kaman ze karya ta, sannan yace “ke bana son karya, for the last time ki gayamin” kawai ta fashe da kuka, mamakine yakama shi, in wani ya shigo se a zata wani abun yayi mata, dan haka a hankali ya sake ta ta mike da sauri ta koma waje, tana fita ta dakko wayarta kunna maganganun Ilham da mamanta. Kawai taji maganar Ilham tana cewa
“Umma wannan itace munafukar da nake gayamiki duk lokacin danayi wani yunkuri zanyi wani aiki akansa itake lalatawa, na dade da gane take takenta sonshi take, amma taki yadda tana rainamin hankali, tasamun Ido ta hanani sakewa, duk lokacin danayi Yunkurin wani abu idonta na kaina, seta wargaza gashi ta hadani dawata tsinanniyar karuwa wai budurwar Jalal ce, hatsabibancin yarinyar nan ya wuce tunaninki, harda wani alwashin indai tana Raye seta rusa shirina akan Jalal” mamanta tace
“Ke sokuwar inace? Kika kasa gayamin tuntuni mu dau mataki akan shegiya”
“Umm har gurin Malam na kaita amma yace baze iya komai akanta ba, dakike ganinta ita ta musanya Apple din dana sawa maganin ranar, makira tsinanniya” umma ta girgigiza kai tace
“Tab aikuwa da sake, dole muyi wani abu karta bata mana aikinmu, amma Khadija kuwa tazo taga halin dayake ciki?” Ilham tace “Ai ingayamiki baya son ganin ta, kinga abunda ya dinga yi kuwa sekace ya haukace, dakinsa na nan kaman kantin mahaukaciya ya fasa komai a dakin, sangartacce ubansa na dawowa za’a canza masa komai” suka cigaba da maganganun su a zatonsu duk Jalal bacci yake besan mesuke ba, ita kuwa Jalila tana sane tayi haka.
Shiru Jalila tayi tana tunani “Kenan Jalal yaji duk maganganun da sukayi shine yake tambayata? Kafin kuga bayana zanga naku”
Jawwad ta hango ya taho da leda a hannunsa, yana zuwa inda take yace “Am sorry na tafi nabarki ko? Na dade bansamu maganin bane, bari inzo in maida kw gida nasan kin gaji”
“To Yaya sannu da zuwa”
“Yawwa babyn Yaya” yai mata murmushi ya wuce, yakai minti goma sha biyar sannan ya fito ya dauki Jalila suka tafi gida. Suna zuwa gida gaban Jawwad yafara faduwa, sakamakon tarar da Maama a harabar gidan da sukayi a tsaye da alamu a zuciye take, Jalila ta fito daga mota, Maama ta dinga jefamata wani irin mugun kallo, Jalila ta basar tace “Maama sannu da gida” tafada tana kokarin wucewa cikin gida “Dakata algunguma” ta dakatar da Jalila, Jalila ta tsaya ta sunkuyar da kai, Jawwad yafito ya rufe mota yakaraso gurin Maama yace “Maama, meyafaru ne?”
“Ubanka ne yafaru, daga gidan ubanwa kuke? Da kuka fita tun farar safiya se yanzu kuke dawowa?” Jawwad ya dan girgigiza kai yace “Kiyi Hakuri, ta rakani gurin Jalal ne, muna Asibiti tun dazu”
“Yimin shiru makaryaci banza da na wofi, kai ko kunya bakaji ka dingamin karya, Asibitinne se yanzu zaku dawo, tafara janka gantali ko, wallahi ka biye mata kafara aikata wani abu dayasaba da al’adunmu se ranka yabaci, tun yaushe Nake maka magana akan Naja, fafur kaki kaje ko inda take, tunda abun naka hakane Naja ta dawo gidan nan, kuma kobakabso seka Aure ta” ta juya ta kalli Jalila tace “Kekuma ko mayyace sekin kyalemin dana, akan me ke baki da zuciya ne? Wallahi kifita daga idona, shegiya mayya” ba Jalila ba hatta Jawwad seda ya dago Ido suka kalli Maama a tare, Jalila ta juya ta shige cikin gida ta barsu a gurin, tana shiga palour ta fara kicibisa da yaya mairo da Naja, a ranta tace “Ashe wannan ibilishiyar matar ce tazo shiyasa yau akemun saukalen Rashin mutunci, tun daga harabar gida ai shikenan”
Aibata gama zancen zucin ba ta tsinto muryar Yaya mairo tana fadin “Ga shedaniyar nan makira, wallahi kozaki mutu gidan nan ma se ya gagareki zama, kuma seya Auri Naja, danbazamu Aura masa Arniya ba, wadda uwatta ta gudu tazabi barbadanci ta battaba, Nutsatsiya zamu aura masa yar musulmi” Jalila ta tsaya ta waiga taga daga ita se su a palourn Maama tana waje tana cigaba da saukewa Jawwad kwandon jaraba, Jalila tace “To ayi mugani mana, karewar nutsatsiya masallaci Zaku Aura masa, sannan kika kuma zagarmin uwa wallahi sena kira taki uwar na zaga dan uwa bata fi Uwa ba” Naja ta mike a fusace tace “Ke dan uwarki uwatawa zaki zaga”
“badai uwata ba, wannan tsohuwar banzar kika zaga, kinbiyata ladar haihuwarki datayi, kuma Na zageta ita wacece? Ko fin tawa uwar tayi? Kuma wallahi takuma zagarmin uwa sena fasa mata kai da wannan flask din” Jalila ta nuna tea flask din da takaiwa Jalal Abinci a ciki, hangame baki Yaya mairo tayi Jalila tace “Yanzu nasan ciwon kaina, ina zubarda hawayena ne a inda yakamata, nadena asararsu akan maganganun ku, iyakaci duk tsufan mace ta zagarmin uwa sena rama wallahi, Sannan ke Naja naji ance kindawo gidan nan da zama, kinyi kwantai ana cusa masa ragowa yana baya so amma, saboda ansan baki da mamora, se cusaki akeyu, to kinkawo kanki, bacin ran da uwarki ta dinga kunsamin tsawon shekaru sena ramasu akanki wallahi, kuma kafin inbar gidan nan sena sena tabattar da kin barshi tukuna” Jalila ta juya tai wucewarta daki yayinda Naja da yaya mairo suka rasa abun cewa, Naja tai karfin halin cewa “Lallai yarinyar nan rashin mutuncin ta yakara yawa, amma karki damu, ni zan saita mata zama namiki alkawarin, setabar gidan nan da kafarta, kuma sena Auri Jawwad, kiyi hakuri zan ramamiki” Naja na rufe bakinta, sega Maama sun shigo ta sako Jawwad a gaba tanata masa masifa shikam ya sunkuyar da kansa kasa har suka shigo cikin palourn
Nan Maama da yayarta, Yaya mairo suka saka Jawwad agaba da fada, shikam yayi shiru yakasa cewa komai babban abunda yake kona masa rai be wuce yadda suke cin mutuncin Ummi ba, matar da basuda tabaccin tana raye ko bata raye, seda sukayi suka gama sannan ya mike ya bar palourn, Yaya mairo tacigaba ds zuga Maama tana kara cusa mata tsanar Jalila a ranta. Yaya mairo ta tafi tabar Naja a gidan, koda Nana ta dawo gida ta tarar da Naja a gidan ba karamin haushi taji ba, dan sam Allah be hada jininta dasu ba.
Jalila takira Hanan a waya, tagayamata abunda ke faruwa, Naja ta dawo gidan da zama ita ake so Jawwad ya aure. A fusace Hanan tace “Kan bala’i, wallahi ba’a isa ba” cikin mamaki Jalila tace “Kamar yaya kenan?”
“kamar yadda nagaya miki, ai wannan fadan banaki bane Jalila nawane, ai muna nan zuwa Kanon very soon, ina baze yuwu ba, ai gara in barmiki Jawwad da ina gani ya Auri wannan yarinyar, gentle man like Jawwad, be dace da Auran ballagaza kaman wannan yarinyar ba dukda kasancewar ta yar uwassa” Hanan ta dinga masifa karshema ta kashe wayarta. Mamaki duk yakama Jalila dama dagaske Har yanzu Hanan bata hakura da Jawwad ba? Haka Jalila taita tunani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button