ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

❤️❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ???? ???? ???? ???? ???? ???? inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku ????????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 2️⃣9️⃣82

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

      _MY FIRST NOVEL _

Banza tai masa ta dauke kanta, yakuma kallonta yace
“Gayamin mana”
A fusace tace “bazan fada ba, meye hadinka da damuwa ta?”
“Nasan kinajin haushina saboda kuskuren da’aka samu, amma…
” kace kuskure? Ba wannan ne karo na farko daka mareni ba, kace na fiye maka shishshigi, nakuma yi Alkawarin na dena yimaka kaikuma meye naka nayi min shishshigi, dalla matsa kabani guri in wuce”
“zan baki guri ki wuce, amma meyasa kika damu dani haka, kike bani wannan kariyar bansaniba, dukda irin halayena? Kinyi kokarin kareni a lokuta daban2 bansaniba meyasa? Gashi kinsan abubuwa dayawa dani ban saniba, at least kin haska wani bangare a Rayuwata da yakasance me tsananin duhu, nesanta Jeje dani hakika haskene me yawa a rayuwata, bansan ya akayi na yadda da Jeje nafara wannan muguwar rayuwar ba, kawai na tsinci kaina a wani yanayi dani ka dai nasan menakeji, amma meyasa kika temakeni, kike kokarin ganin kin canza akalar Rayuwata?” yai tambayar yana kara tsareta da ido, itama kallonsa takeyi dan bata san mezatace masa ba, wani uban tsaki taja ta wuce ta gefensa ta fice daga dakin.
A hankali ya koma ya zauna yana tunanin abubuwa da dama, abubuwa dayawa ya dinga tunawa, Jalila tayi Rawar gani a Rayuwarsa, yanzu ya gane abubuwa dayawa da a da sam besan dasu ba.
Itakam guri tasamu tai zamanta taki komawa cikin gidan tanata zancen zuci, karar motar Jawwad ne ya dawo da ita hayyacinta, shida Abba ne ya dakko shi a Airport, da fara’a Jalila ta tashi ta nufi inda suke, Abba yace “Jalila bakida lafiya ne? Naga kin rame haka” murmushi tayi “Haba Abba duk wannan kibar danayi kayana sunmin kadan fa”
“Anya kuwa in yadda? Idonki kaman kinyi kuka fa”
“Abba nikam meze sani kuka yau zanganka? Bacci nayi kawai, kawo jakan in rike maka” tasa hannu ta karbi jakarsa, Jawwad yana ganin dakiyar Jalila daka ganta kasan tana cikin damuwa, amma ta maze tanata kokarin boye damuwar.
Ba karamin murna sukayi ba dawowar Abban nasu, Jalila tasan koba komai zata samu saukin wani Abun,
bayan sallar magariba suka gabatar masa da Abinci yaci, nan suka sake aka shiga hira da Abba, Maama tanata dan dari2 kar Jalila tagaya masa wani abu, dan ta lura tun dazu Abba yake tambayar Jalila koda matsala amma tace ita ba komai. Sekusan goma na dare suka watse suka tafi dakunansu.

Ilham tagaji da azabtarwar da Jalal yake mata, yakamata sunemi wata mafitar, tsawon shekarun datayi a gidansu Jalal bataga alamar zasu cinma burinsu ba, Jalal mugun baudadden mutum ne, ga tsabar jaraba da masifa, gashi da rashin yadda, kwanan nan ta lura kaman yakara tsanarta batasan metayi masa ba, ta lura yanzu har uwassa ma yakara fita harkarta, ko cikin gidan baya shigowa, mikewa tayi ta tafi palourn mummy, ta tura kofa bako sallama ta shiga ta samu guri ta zauna
Mummy ta kalleta tace “Ke lafiya kika shigomin bako sallama meye haka?”
“Mummy yaushe zaki cikamin alkawari na ne?”
“Wanne kenan?”
“Mummy har yanzu banga alamar Yaya Jalal ze yadda ya Aureni ba, lokaci fa kuremin yake ni macece yakamata zuwa yanzu kiyi wani abu akai, ina sonshi, banajin zan iya Auren wani bashiba, kitemaka Mummy dan Allah kiyi wani abu” Ajiyar zuciya Mummy tayi “Ilham yakikeso inyine? Yaron naan kullum wutar kiyayyata ruruwa take a ransa, kiduba rashin lafiya nayi amma da naje kansa ga yadda ya rikice gana sambatu infita baya son ganina, ya zanyi Ilham? Kaina ya kulle al’amarin Jalal sunfara bani tsoro”
“Kina nufin in hakura dashi kenan?”
“Bahaka nake nufi ba, amma kidan karamin lokaci, nina miki alkawari ai, bakuma zan saba ba”
“Shikenan Mummy seda safe” Ilham ta tashi ta fita ranta a bace, ji take kaman ta shake Mummy, takoma dakinta ta kulle kofa, ta dau waya takira ummanta tagaya mata abunda ke faruwa, tace mata ta kwantar da hankalinta, in tasamu lokaci taje gida, zasu san yadda zasu bullowa lamarin Jalal da Mummy.

Da sassafe Jalila suka shiga kitchen hada Abinci, bayan sun kammala kowa ya hallara a palour don karyawa, bayan an gama breakfast suka shiga hira, anan Maama ta sanarda Abba ai Naja tazomusu hutune, sannan akwai maganar datakaeso zasuyi da Abba amma ba yanzuba, ba karamin faduwar gaba Jalila taji ba dan tasan be wuce zancem Auren Jawwad da Naja ba.
Abba nan yashiga rarraba musu tsaraba kamar yadda ya saba in yayi tafiya, Abba yabada zuma a gwangwani yace akai gidansu Jalal, A ajiyewa daddyn Jalal, ya daga waya ya kira Jawwad yace yana son ganinsa, bayan yagama waya da Jawwad ya kalli Jalila yace
“Baby Babanki yayo waya daga Kaduna (baban Hanan) yace nan da kwana uku zasuzo, yanaso zasuje dake Bauchi yana neman Izinina, nace masa inkin amince ba damuwa amma bana so ki dade a can” Jalila tai murmushi tace “Na yadda Abba, zanje” Nana kam ta hade rai tace “Ni gaskiya ban yadda ba” Abba yace “Jalila nayi mamakin saurin Amincewarki da batun tafiyar nan, iya sanina dake ba kyason barin gida, amma ya’akayi haka, ko akwai wani abu bakyason gayamin ne?”
“Haba dai Abba, ba wani abu ni kawai inason inzaga inje garuruwan dabantaba zuwa ba”
“Eh hakan yana da kyau, amma bazan bari ki dade ba kinga ga komawa makaranta”
Jawwad yai Sallama ya shigo palourn, ya durkusa ya gaida Abba sannan ya gaida Maama, aciki ta amsa masa dan tanajin haushinsa, yakoma gefen Abba ya zauna yace
“Abbana gani, Allah yasa ba laifi nayi ba”
“Aini baka laifi a gurina, da dai wannan ce tafi kowa iya laifi” Abba ya fada yana nuna Nana, dariya sukayi, yayinda Nana ta dan hade fuska da sigar shagwaba tace “Abba niko? Aikam bana wani laifi ni” Abba yace “Anya kuwa a tambayi Jalila?” haka Abba yasake ya dinga wasa da dariya dasu, banda Maama da take ta cika tana batsewa, Naja kam dama tuni tabar gurin, Abba ya kalli Jawwad yace “Babban mutum, daddynka yamin magana yace yasamo maka aiki a NNPC amma kace kai A’a, yace in rarrasheka ka karba, meyasa bakason Aikin”
“Abba ba banaso bane ba, banason tafiyane saboda Jalal, bansan wani hali ze shiga ba, dukda Alhamdilillah ana samun cigaba a daidaituwar lamuransa, amma banason in tafi yacigaba da mummunar Rayuwa tunda……… Ai kafin yakarasa a fusace Maama tace” Jalal din ubanka ne? Kai meyasa bakada tunani ne? Ana nema amaka gata amma kana maganar wani, baka isaba seka karba ka tafi, tunda kagama karatun zaman jiranwa zakayi? Shiru Jawwad yai bece komai ba, a hankali Nana da Jalila suka zame suka bar palourn ya rage saura Maama, Jawwad da Abba, Abba yace “Jawwad tashi kaje zamu karasa maganar” Jawwad ya tashi ya tafi, Abba yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button