ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“Waime yasa mata wasunku bakuda halaccine? Haba Maman yara, Abunda Jawwad yayi, yai dai2 shine halacci irin kaunar da yaron nan yake masa bekamata kice hakaba, ki kyale shi zuwa wani lokaci tukuna mugani, kinsan kowane dan adam baya wuce rabonsa”

“Naji, Amma Jawwad ya kai munzalin da a yanzu yadace ya fuskanci Rayuwarsa, ya nemi Aikinyi sannan ya mallaki iyali”
“Eh gaskiyane, samun Aiki ba wani babban Abu baneba, kuma bacewa yayi bazeyi Aikin daza’a samomasa ba sedai yace abashi lokacine saboda Jalal, Amma kuma aini har yanzu becemin ga wata wadda yakeso ba tukuna, kinsan mutumin nawa da kunya Akwai fulatancin sosai a tareda shi, Allah yasa ko budurwa ma yanada ita” Abba ya karasa zancen cikin murmushi, Maama tace “inma bashida ita se asmomasa, bazan cigaba da zura masa ido se ya tsofe ba Aure ba, dama maganar danakeson yimaka kenan, ga Naja nan ‘yar gidan Yaya mairo da ita nakeso in hadashi, tunda yarinyar itama ba laifi akwai hankali” Abba ya danyi shiru sannan yace
“To banki ta takiba, Amma banason ayi abunda ze zamana an cutar da dayansu, yakamata muji ta bakinsu tukuna”
“Kamarya semunji ta bakinsu, muba iyayensu bane ba dole subi abunda mukeso, hakan ze kara karfin zumuncin dake tsakaninmu”
“To Allah ya tabattar mana da alkhairi, ni bari in wuce daki zan dan kwanta, kar amanta akaiwa Baban Jalal wannan zumar”
“Za’akai” Abba ya wuce daki.
Jalila tanata tunanin yazata bullowa wannan lamarin, dan in aka hada Jawwad Aure da Naja an zalunceshi, gashi tasan Maama bazata taba barin Jawwad ya Aureta ba, nan duniya tasan inta Auri Jawwad tayi sa’ar miji, salihin bawa da baruwansa da hayaniya”da taga tarasa mafita taje ta janyo trolley dinta ta fara shirya kayan dazatayi Amfani dasu dan tafiya bauchi, taji gara ta dan bar garin tayi nisa maybe ta huta da wannan abubuwan daga wannan se wannan.
“Kayan me kike hadawa haka?”
“Kayan da zan tafi dasu Bauchi mana”
“Jalila bana son kitafi, badan hutunmu next week ze kareba da binki zanyi”
“Allah sarki my Nana, nikaina zanyi missing dinki da kiriniyarki”
“Mtseww Allah raka taki gona, inkin tafi karki dawo bakar kaya kawai, daga nan kema kitafi inda uwarki ta tafi”
Nana ta juyo ta kalli Naja a fusace tace
“Wai Naja ke wace irin mahaukaciya ce” da sauri Jalila ta dakatar da ita ta hanyar cewa “Ke Nana wayagaya miki in kare yana Haushi ana kulashi, kyaleta dan Allah, innaje Bauchi me kike so in kawo miki” Naja tace “Ke kin isa kice min Karya, uwarki ce Karya baniba” Jalila tai sauri tace
“Nana naji kaman muryar Maama tana kiranki yi Sauri kije” Jalila ta tura Nana waje ta dawo ta zauna ta kalli Naja tace
“Uwata batada katon baki da zako zakon fika kuma bata haushi kaman uwar wata, ki kiyayi ranar da bomb dina ze tashi dake, Naja har inda Yayarki Sa’adah ke zuwa a zubar mata da ciki nasani, tsohuwar karuwar Alhaji Kabiru ce dayanzu yake can ana shirin gurfanar da shi a kotu ko karya nayi? “
zaro Ido Naja tayi
“Karya kike ubanwa yagaya miki haka? Waye yayiwa Sa’adah sharri “
“Kinga bana son wani borin kunya, ganina kawai kike amma bakisan waceni ba, bana zama da mutum ba tareda nasan wayeshi ba, karkiyi mamakin kema nasan komai akanki Jalila ta wuce tunaninki Naja, kibini a sannu im bahakaba zanmiki tonon sililin da sekin kasa hada ido da mutane, tun ranar dana ji kina waya cikin dare da Saurayi kema na fara bin diddigin ki dan haka ki kiyayeni”
Gaba daya jikin Naja ya sanyi, yayinda gumi ya shiga tsatstsafo mata ta goshi, tunani tafarayi ya akayi Jalila ta san wani abu akansu haka, bakowa yasan wannan abubuwan da Jalila ta fada ba amma ita ya akayi tasani, Jalila ta tashi tabar inda Naja take tacigaba da hada kayanta. Tundaga Ranar Naja takejin tsoron yiwa Jalila rashin mutunci dan ta tsorata da kashedin datayi mata.
Shikam Jalal yakara takure kansa, tun ranar bekuma haduwa da Jalila ba, yana son ya ganta amma baya samun damar hakan, dan ko a waje baya ganinta, Jalal baya son kowa yaje inda yake, baya iya cin Abinci idan ya tuna abunda Jeje da uban gidansa yayi masa saboda laifin da banashiba seyaji duniyar takara yimasa Zafi, ga abunda yaji Da kunnensa Ilham na fada akansa itada mahaifiyarta, Gakuma Jarumatar da Jalila ta gwada saboda shi abun ya dade yana bashi mamaki ya akayi Jalila ta gano Jeje da uban gidansa akansa suke Aiki harta hada wannan gwaramar, yana son jin wasu abubuwan daga gareta, idan yaji duniyar tayi masa zafi, seya sha giya ya bugu sannan yake jin dadi.

Jalila tashirya kayanta tsaf tun dare, ji take kaman za’acireta daga prison zata tafi kwana biyu ta huta da tension din da suke kanta.
Tun safe Jalila tayi wanka, tai waya da Hanan tace mata zasu karaso da wuri.
Jawwad yaje ya takura Jalal yaci Abinci ya dinga yi masa Nasiha akan wannan takura Rayuwarsa da yayi, Jalal yace “Dan uwa, Nayiwa Kanwar ka laifi fa, nikuma tayimin Abunda har in bar duniya bazan manta ba”
Jawwad yasan Jalila yake nufi yace
“Allah yasa ba wani laifin tayi maka ba? Nasan Halin Baby sarai in wani abun tayi maka Allah yabaka hakuri”
Jalal yai murmushi yace “Ba laifi tayimin ba, Amma tayimin abunda banida abun biyanta, inajin kunyarta abubuwan danayi mata abaya” Jalal ya karasa maganar idonsa fal kwalla
“Subhanallah haba Jalal, haba ‘yan mazan daddy, hawaye a idonka, kadena damuwa kaji, komai ze wuce banason ganin ka cikin damuwa muje kaci Abinci, Yau Jalilanma zata tafi bauchi”
“Bauchi kuma?”
“Eh Jalal, nima ban soba amma tasamu ta huta, zaman gidanmu sam baya mata dadi, Maama tana takuramata kuma Yaya mairo ce take zigata, banajin dadin abunda suke mata, inta tafi ta huta kwana biyu, tashi muje ka karya”
Jalal be kuma cewa komai ba yabi bayan Jawwad suka fita. Da kyar Jawwad ya takura Jalal yaci Abinci shima kadan yaci yace ya koshi. Jawwad yaita tunanin me Jalila tayiwa Jalal haka har yake cewa baze manta ba?.
She kusan karfe daya na Rana su Hanan suka karaso kano gidansu Jalila, a guje Jalila ta fito daga cikin gida ta rungume Hanan cikin farinciki, Hanan tace “Nayi missing dinki ‘yat Baba” suka kuma rungume juna suna murna, Jalila ta kalli Abdallah tace “Babban Yaya sannunku da zuwa ya hanya?”
“Hanya Alhamdilillah, da tuni munzo amma Hanan tasa muka makara”
“Aina sani ita tahana kuyi sammako” Hanan tace “to mukoma kenan?”
“A’a ni bance ba, ina Baban yake?”
Hanan tace “Daddy shida Mummy zasuje su tarar da mu acan, dama zamuyi biki, yarinya har Anko daddy ya dinka mana nida ke”
Jalila tai musu jagora har cikin gida a palour tabasu gurin zama, taje ta sanarda Abba su Hanam sunzo, dukda wulakancin da Maama takewa Jalila, amma ta sakarwa su Hanan fuska ba laifi, Jalila taje tagayawa Nana su Hanan sun karaso. Naja najin haka ta biyo su dan ganin wai wacece Hanan din nan ne tana zuwa palourn tayi turus, se yanzu ta tuna suntaba haduwa a gidan kamarta daya da Jalila, Amma Hanan takara kyau sosai seda Gaban Naja ya fadi, Hanan tanada kyau sosai gata ta iya gayu, Nana ta fito palour suka gaisa dasu Hanan nan aka shiga hira a palourn, Abdallah yace “Nifa banga Jawwad ba da mutumina Jalal” Nana tace bari inje in kiramaka shi, nasan besan kunzo ba tashi tayi ta fice a palourn Maama da kanta ta kawo musu Abinci, Abba ba ruwansa ya zauna suka dinga hira da Abdallah, Jalila ta janye hannuna Hanan zuwa dakinsu, Nana ta dawo itada Jawwad, Jawwad yashigo da fara’a ya zauna kusada Abdallah suka gaisa daga nan sukayita hira.
Naja ta babbake a daki, dan haka Jalila bata samu damar yiwa Hanan hirar datake so ba sukayita hirarsu ta rayuwa, Hanan taji muryar Jawwad a palour tacewa Jalila zanje wanke Hannu”
“baga toilet ba kishiga mana ki wanke”
“Ba wanke Hannu zanba Jawwad nakeson gani”
Naja tace “Ke mekikace meye hadinki da shi dazaki ganshi?”
Ko tsayawa Hanan batayi ba tayi waje, amma kafin takarasa palourn ta tsaya ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito palour,
Da sauri Naja ta fito itama, unexpected Jawwad ya daga ido yasauke akan Hanan, takara kyau dressing dinta ma yayi ba karya, gaba daya besan lokacin dayake kallonta ba, tabass Hanan kamarta daya da Jalila a ransa yace “tsarki ya tabatta ga Allah, ba dangin iya bana Baba, amma ya halicci masu kama daya kuma ba twinsa ba, sedai sunada dan banbanci”
Cikin kasaita ta wuce shi a palour ta nufi kitchen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button