ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Gaba daya zuciyar Naja ta gaama tsinkewa, Ganin Hanan taki dawowa yasa ta fito harabar gidan, amma tayi tozali da Hanan da Jawwad se murmushi yake, tunda take da Jawwad maganar minti goma bata hadasu balle yaita wannan murmushin, Nana ma befiye shiga harkarta ba, a da tayi tunanin ko Jalila yake so, wato wannan yarinyar me girman kan bala’i ita yakeso, koma dai duka yake sonsu ne tana tsaye tana kallonsu
Jawwad yafara magana “Hmm Hanan ina kika samo wannan ideology din, yazakice Baby Akwai wanda takeso, kuma munayiwa juna son ‘yan uwan taka?”
“Ban fada domin in shiga tsakanin ku ba fa, nawa hasashen ne haka, Ita kanta Jalila bata son wa take so ba, bakowane lokaci take yadda da zuciyarta ba tana karbar abubuwane da lissafin kwakwalwarta”
“Hanan ya akayi duk kika san Jalila haka ne?”
“Haidar a zaman danayi da Jalila motsi tayi nasan abunda take nufi, nasanta fiye da yunwar cikina”
kyar yake kallon Hanan ko kyaftawa bayayi yana juya maganganun ta a ransa, ganin yanata kallonta yasa tace “ya dai kona bata maka raine?”
“Ina so kicigaba da magana ne, komai kikayi kyau yake miki” murmushi tayi tana rufe fusaka,
yace “masha Allah yanzuma bakiga yadda kika kara kyau ba”

Abdallah da Jalal suka fito daga part din Jawwad, ba karamin matching Jawwad da Hanan sukayi ba, suka nufosu Abdallah na shirin sukarasa ya tsokane su, shikuma Jalal Jawwad kawai yakson ya titsiye yau, amma kafin su karasa Naja ta rigasu dan Naja ba karamin kulewa tayi ba, dan haka ta taho kaman wata kura, ta nufo su Jawwad, tana zuwa ta rike kugu tace “ke wace irin matsiyaci ya ce haka? Nace miki Jawwad shine wanda zan Aura na meye zakizo kina wani shige masa, kina wani salon karuwanci meye haka?”
Hanan kaman tayi magana, sekuma ta fasa tace bari inga matakin daze dauka
Aikuwa Jawwad yace “Naja meye hakane wai? Yazaki kirata da karuwa me tayi miki? Wannan wace irin magana ce”
“Eh dole kace wace irin magana ce mana, kasan ni zaka Aura amma kazo kunfi minti Ashirin a nan gurin alhalin niko hirar minti goma bakayi dani”
Jalal yace “wai dan Allah meyake damun wasu matanne, yanzu meye hakan kuma?”
Abdallah yace mata se Addu’a ai, se yanzu Naja ta lura da shi, wancan zuwan ma tare sukazo, ita da Abdallah ze Aureta aida ta hakura da Jawwad
Abdallah yace “kinga baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah, Kekuma Auta, Jawwad fa Ustaz ne, kinzo kin wani kanainaye shi tun dazu, kina kashe masa murya kina fari, Ashe ma ankusa Aurar dashi, ai seki hakura” gaba daya sukayi dariya suka maida Naja kaman wata mahaukaciya,
Hanan tayi murmushi cikin kasaita tace “Macen data kai mace, itace idan tace tanason take samu, ba ragowar muna mata ba” shikam Jawwad ba karamin kunya Abdallah yabashi ba
Sannan Hanan tace “gaskiya Abdallah kai dan hana ruwa gudune, Yaya Jalal ka shiga tsakanina da Abdallah, My Haidar karka damu da Abdallah haka yake da wannan takurar”
Jalal yace “Inyee ashe har suna aka canza maka abun masoya kai Jawwad, se anyi magana ya dinga sunkuyar da kai waishi kunya, bayan yagama zuba kalamai shima”

Da sauri Naja ta shige cikin gida, tanata kumfar baki a palour ta tarar da Nana sun fito Jalila daga part din Abba
“Ni za’ayiwa hauka, ni wannan yarinya zatayi wa karuwanci, wallahi yau duk bala’in da za’ayi se anyi, shegiyar yarinya a gabana kaman zata hadiye Jawwad kan bala’i, a fusace Nana tace
“Ubanwa ya hana kiyimusu can sekinzo mana nan, inkina yiwa Jalila tana kyaleki, ita wannan a yanzu intaga dama wallahi zata saka sojoji sumiki dukan mutuwa, dan ko a ina take a a fadin kasar nan akwai yaran babanta”
Jalila tace “Nana, bari inje waje inga meke faruwa, Nasan halin Hanan sarai, ba kanwar lasa bace, dukan sojoji yafiye maka dukan wannan bakin nata, koba komai yau na huta, Anamin maganin karya me remote”
Aikuwa Jalila takara angizo Naja, “ke dan abu ta kazakazanki, nikike cewa karya?” Ai Jalila bata jira taji metake cewa ba ta fito.

Jawwad duk yarasa ya zeyi dasu Jalal, se tsokanar sa sukeyi shida Abdallah yana sunkuyar da kai, itakuwa Hanan ko a jikinta data fuskanci sun takura masa, se tace
“cwt Haidar don’t mind them, kaga Abdallah aiba a magana shima haka yake zuwa ana kashe masa murya, idan ana masa wannan kashe muryar seka sace shi ka gudu be saniba” seda ta danyi murmushi sannan tace “Kaga yaya Jalal Allah kadai yasan shime ake masa, shima nasan yana zagayewa yaje akashe masa muryar dayake takura maka, kaima ka dinga ramawa amma zanso inga budurwar Yaya Jalal inga in an kashe masa muryar shi ya yakeyi, sweet Haidar sena koya maka magana, adena takuramana”
Jalal yai dariya yace “Ni Hanan aibana soyayya, ban santa bama balle inje a yimin wasu kalamai,, in aka fara yimin kalaman zan kiraki kizo kigani, sedai fatan Allah ya hadamu da masoyanmu na gaski….. Jalila ya hango tana sakkowa daga steps, tayi kyau sosai, amma abunda yabashi mamaki ta rame, “ko bata da lafiya ne? Tayi rama sosai, itama tana daga ido sukayi ido hudu, taji gabanta ya fadi “kaddai ace har yanzu Jalal bashida lafiya, wace irin rama yayi haka?” kallonta yake yadda take tafiya step by step, Hanan kam tuni taga abunda yake faruwa tai murmushi a ranta
Jalila ta karaso tace “Yaya Jawwad ina fatan komai lafiya, naji Naja tanata masifa, Hanan me kikayi mata ne?”
“meko zanmata? Dan kawai ta ganni da Haidar ne”
Abdallah yace “karya takeyi tun dazu ta tsareshi anan tana zuba masa kalamai, tun yana jinkunya naga alamar kalaman sun fara shigarsa, murmushin yake Jalila tayi tace” nikam ki lallaba ku rabu lafiya”
“karma a rabu lafiyan ba abunda ya dameni bane, haidar dina ne agabana”
Abdallah yace “ke Hanan kinfiye zakewa, ance miki anbadashi amma kin nace” Hanan ta lura yadda Jalal ke kallon Jalila, itama Jalila tana satar kallonsa amma bata bari su hada ido, Hanan ta gyar murya tace
“Queen kinga Yayyenki nan biyu sun takuramana, shi Abdallah nasan yadda Siyama ke kasheshi da kalaman soyayya, amma shi Yaya Jalal ban saniba, da nasani da na ramawa Haidar, amma gayamin ko kin san budurwarsa?” hararar Hanan tayi tace “Aiba tare muke yawo ba balle in san budurwarsa, seki tambayeshi ai”
Hanan ta tintsire da dariya dama tana sane tayi hakan?
Jawwad yace “Baby ina Abba ne?”
“Yana cikin gida, yaya Abdallah ku shiga sekuyi sallama da Abban”
“ok bari muje”
Jawwad ya musu rakiya suka nufi cikim gida
Jalila tayi mamaki yadda Jalal yake hira bazakece shine ba, Jalila tafara kokarin saka jakarta a mota
Jalal ya dan kara kurawa Jalila ido, yazo kusada ita ya tsaya, ya danyi kasa da muryarsa yace
“meyake damunki kika rame haka?” bata dago ba tace
“ni ban wani rame ba, dama haka nake”
“hmm, shikenan tunda kince haka, amma yaushe zaki dawo?”
“Ka Aike nine, wai ina ruwanka danine?”
“Aiba abun zafi bane, meye nayin fushin kuma?”
“idan na tafi bazan dawo ba, idan na tafi zan hutawa raina indena ganin masu ba kanta min rai, kaima ka huta dame yi maka shishshigi, kaci karenka babu babbaka, inka gadama kaima ka gina club din shna giya”
“meyasa ba kya mantuwane? Abu baya wucewa a gurinki kenan?” Su Hanan ya gani suna fitowa dan haka yace mata
“zaki iya zuwa ki zauna a wani garin, kibar Jawwad din naki da Nana tsawon lokaci?, idan ina ganin ki inajin kwarin gwiwar dena wani abun, dama zan miki sallama ne dan inaga kafin ki dawo, zan koma Dubai da zama, bazan kara dawowa Nigeria ba, har abada, ina fatan kiyafemin kura kuran danayi miki, Sannan Nagode da kokarinki a kaina, keda Ummi bazan tabawa mantawa daku ba, sannan A shekarun baya, wani zuwa da kikayi, Su daddy sun baki kyaututtuka, ciki hada wani Jan Alqur’ani me red din box, nina baki kyautar wannan Alqur’ani sannan Akwai Ajiya ta a ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button