ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

      _MY FIRST NOVEL _

Jalila tace “Yasalam, Nana kiname Ilham zata shigo har cikin gidan nan ta daukarmin abu natane? Meya kai hannunta kayanmu harta daukarmin abu”

“Jalila Al’qurani fa ba Novel bane ko littafin hausa da zan kamata da kokawa in karba, gyaran daki nakemana tashigo ta ganshi ta dauka”

“Nana kingama dani dakika bari ta tafi dashi, amma tunda tace idan na dawo na je karba ki gayamata ta saurari dawowarta wa, tasan karona da ita ba dadi, zanzo in karba idan bata bayar dan Allah ba zata bayar dan dole, karma kikuma tada maganar tabaki zan dawo in karba, banda Jahilace me zatayi da Al’qurani metasani aciki? Inma tasani bashida amfani a gurinta ai”

“To nidai Allah yabaki hakuri, ni bayan haka wasu maganganu tazomin dasu dasam ban gane inda ta dosa ba?”

“Kamar yaya?” Jalila ta fada a kagauce

“Nikam Baby meye hadinki da Jalal ne?”

“Wane irin tambaya ne wannan Nana?”

“Jalila inkinga rashin mutuncin da Ilham ta dingayi a dakinmu sekinsha mamaki, tana gayamin wai na hada kaidake zaki kwace mata Jalal, wai taga abunda ban ganiba, Kina son Jalal ne, Naja tazo suka hadu sukayi tayi, ni abun yabani mamaki iya sanina ko shiri bakwayi dashi amma maganganunta sun ban mamaki “

Jalila tayi ajiyar zuciya tace
“Nana kyale ta aikinyi ne bata dashi, kinsan tun asalina yarinyar nan batayi min ba, shiyasa take neman masifa, nime zanyi da wani Jalal, ai Jalal se ita makakkiya itama din ba Auren ta zeyiba, ki manta da ita zan dawo ai daidai nake da ita ai”

Nana tace “Hmm Jalila kenan, inaji kaman kina boyemin wani abune, amma inba rami meyakawo rami? Shikenan dai sekin dawo din, ki gaida min Hanan dan Allah ????”
Nana ta kashe wayarta, Jalila ta kalli Hanan a salube,
“me Nana take nufi?” dan daga mata gira Hanan tayi tace
“Queen kenan, naga kin damu da abunda Ilham tayi, amma keda bakyasonsa meyasa kike son abunda yafito daga hannunsa haka har kikejin babu dadi?”

“Hanan bansan mezan gaya miki ki yadda dani ba wallahi, Hanan Al’qurani abune me girma, sannan inason sanin meye Jalal ya ajiye tsawon lokaci ni banganiba, sannan muddin ina raye Wallahi sena nunawa Ilham iyakar ta”

“to meye na wannan tada jijiyoyin wuya haka easy queen i know you can do it, amma meye next plan dinki akan Jalal, kina ganin tafiyarsa Dubai akwai Alkhairi kuwa?”

“To yatafi uwar Dubai mana, daga nan yatafi bangon duniya idan yanaso? Ke nagama abunda zan iya akansa kowa tasa ta fishsheshi, dama yace ina takuramasa kinga se yaje yayi abunda ya gadama, nima takaina nake, yatafi bayan duniyama yaje ya bude gidan giya in yanaso” takarasa fadin haka tana kokarin kwanciya
Hanan tace “karya kike tawajena, nasan halinki kaf Jalila yanzu kina jin wani abu ze sameshi zaki kuma tashin hankalinki, kya gama zagaye zagayenki ne”
Banza Jalila tai mata ta ja bargo ta shige, Hanan tai murmushi itama ta kwanta.

Jawwad yaje kiran da Mummy take masa, amma ya lurada wani kallon banza da Ilham take masa bebi takanta ba ya durkusa ya gaida Mummy dake zaune a palour,
Har kasa ya durkusa suka gaisa, Mummy tace “yawwa Jawwad dama nace kazone saboda Jalal, inason ganinsa amma nasan nidashi bazezo kiran danake masa ba, dan Allah Jawwad ka dinga yimasa fada, sati me zuwa daddynsa zezo akwai maganar danake so muyi nida shi da babansa, dan Allah idan daddynsa ya dawo zanmaka magana inaso ka kawomin shi “
Jawwad yace
“insha Allah Mummy zan masa magana, acigaba da hakuri ana masa Addu’a Insha Allah komai ze wuce, Alhamdilillah yanzu yafara rage wasu abubuwan”

“Hakane Allah yasa hakan nima ina masa addu’a”
Yatashi yai sallama yafita, Ilham tayi tsaki tace “Nifa Mummy gani nake wannaan Jawwad din ke kara ziga Jalal yake wani rashin mutuncin yake kara kina”
“Kinga nidai ba wannan ba, kokarina kawai inga abunda na shirya ya tabatta akan auren nan naku, idan kika matsa kika nuna bakyason Jawwad kinsan baze taba aurenkiba ko? Dan haka kishiga hankalinki”
Ilham ta zumbura baki ta tashi tabar palourn.

Zaman bauchi ya karbi Jalila, tayi kalau da ita, kusan koda yaushe tana tareda Anty fiddo kokuma gurin inna, susha hira taci dariya, gashi cousins din Hanan suma ‘yan shaftane mazansu da matansu, haka ake zuwa a cika babban palourn gidan aita wasa da dariya, samarin gidan da yawansu suna suna son Jalila amma fafur Hanan tace, ai Jalila tanada miji. akwai wani cousin din Hanan yusuf akayi bikinsa, komai da Jalila akeyi, kaikace ‘yar gidance dama can sunsanta, sunajin tsoron yusuf sosai saboda baya wasa ma sosai, anan gurin babban abokin ango ya like yace shi nan duniya Jalila yakeso, Yusuf yaji dadin hakan, dan haka yace “Aitunda daddy yace da Hanan da Jalila duk’ ya’yan sane, shima da Jalila da Hanan duk kannensa ne, ya yaba da halin Jalila dantafi Hanan nutsuwa”
Bayan biki yusuf yasamu daddyn Hanan, yagaya masa Abokinsa Ahmad yana rikon ‘yar baba
Daddy yai murmushi yace “indai’ yar baba ce inta amince sannan kun cika ka’idojinmu ai semu duba inkun cancanta abaku semu baku”
Yusuf yace “daddy kenan indai ana sanmu ai zamucika dukkan sharudanka” daga nan sukayi ta hira daddy agaban Mummy akayi tace “Amma danayi murna, dan Ahmad mutumin kirki ne zataji dadin zama dashi, amma ina tunanin yadda zata zauna da matar Ahmad, kasan ‘yar taka bata da hakuri’ ya’yannak ban san wadda tafi wata hakuri ba”
Daddy yace “Ai indai tana sonshi lafiya kalau zasu zauna, inmuka koma zanyiwa Abbanta maganar, indai basuyiwa wani Alkawari ba, Zanbawa Ahmad”
Yusuf yaita godiya kaman shi za’a bawa.

Daga Jalila har Hanan basu san me akeyiba Yauma, an taru a palour ana hira da daddare Daddy yake cewa abashi list din sunayen wanda ze samawa aiki, Jalila ba karamin birgeta family din nan suke ba, kansu a hade yake haka aka gama hira aka watse.
Jalila kullum tana tareda Inna, sannan Mummy Hanan duk ta dena mata wannan wulakanci datake mata abaya.

Jalila suna chatting da suleiman yake gaya mata, an tabattar da Alhaji Kabiru yana saida makamai da kwayoyi shida Jeje, ranar litinin za’a kaisu kotu, Jalila ba karamin farinciki tayi ba, taitayi masa godiya. Ta zauna tayi shiru tayi wani tunani, amma bata gayawa Hanan ba tasan damunta zatayi da tsokana dan haka tabar abun a ranta

Da safe Jalila bayan sungama breakfast taje tasamu Mummyn Hanan tace “Mummy dan Allah kan daddy ya fita inason inganshi”
Mummy tace “to shikenan zan masa magana” Hanan tace “queen me zakicewa daddy ne? Ina fatan bawata matsala?”
“Ba wata matsala inason inganshiine”
“to shikenan”
Mummy taiwa Jalila iso, taje palourn daddy , ta shiga suka gaisa yanata tsokanarta tana murmushi, se bayan sun gaisa tace
“babana gurinka nazo kamin wata Alfarma”
“Ina jinki ‘yar Baba fadi komene? Insha Allah in zan iya sena miki shi”
Jalila ta kwashi kusan Awa guda a gurin daddy sannan ta fito, ko Hanan bata gayawa Abunda ta tattauna da daddy ba.

Har yanzu Jalal baya walwala sosai, daddynsa yadawo Nigeria, yakan shiga cikin gida gurin daddynsa, amma babu ruwansa da Mummy balle wata Ilham, Iyakar Jalal dakinsa, sedai wani lokacin yakan fito amma baya nisa sosai, Jawwad ne ke takuramasa yadan fita dashi suzaga gari, Jalal yadena zuwa club amma yana shaye shayensa a dakinsa be denaba.

Hannah duk yadda zatayi taga Jalal abu ya gagara, dan haka ta yankewa kanta shawara ta karshe, ta shirya tsaf ta tafi gidansu Jalal, Jalal na cikin dakinsa a kwance besan me akeba, daddy yana gaggawa ze fita da yamma motar Hanna tai parking a kofar gidan, ta fito daga motar da wata irin shiga da bata kamaci dan musulmi ba, da sauri takaraso gaban daddy tace “barka da yamma”
Yace mata “yawwa barka” ya dauke kansa yana kokarin bude motarsa tace “Amma dan Allah Jalal fa?” seda gaban daddy ya fadi, kaddai ace Jalal yafara neman matane ya dake yace mata “lafiya me Jalal din yayi miki?”
“meyema bemin ba? Amma dan Allah yana cikine gurinsa nazo, inason ganinsa” kaidajin yadda Hannah ke magana kasan babu Alamun tarbiyya a tareda ita daddy yace
“Meye alakarki dashi dakike nemansa, baki bani amsa ba”
“Akwai alaka me girma tsakanina da Jalal, sanin Alakar bata da amfani a gareka, babu abunda sanin Alakar ze kara maka banda bacin rai da tashin hankali, dan haka bekamata ayi tone tone ba, amma ina neman Alfarmar ka dan girman Allah kasaka baki Danka ya Aureni, hakan ne kadai hanyar tsira da mutuncina”
Mummunar faduwar gabace takama daddy, hasashensa yazama gaskiya kenan, yanzu lalacewar ta Jalal harta kai ga fara neman mata Innalillahi wa inna ilaihi raji un juyawa daddy yayi da sauri ya rike kansa ya shige cikin gida yana hada hanya.
Hannah kam murmushi tayi tace “koda banganka ba Jalal, nayi abunda nasan dole ka nemeni, na fuskanci bakajin rarrashi kafiye taurin kai, gara in fito maka a Hannah ta.
Ilham na palour tana harabar gidan tana waya daddy yazo ya wuce rike da kansa, mamakine yakamata, yanzun nan fa yake sauri ze fita to shida waye, sauri tayi ta nufi gate ta leka, amma taga anja mota batagane waye ba.
Gida ta dawo taje tagayawa Mummy, da sauri Mummy ta fito ta nufi part dinsa yana zaune ya dafe kai akan kujera, zama tayi kusada shi tace
“meyasameka hakane? Habibi lafiya kuwa yanzufa kake cikin walwala kafita meke damunka ne?”
Dagowa yayi idonsa jawur yace “Khadija Jalal”
“meyasami Jalal din? Bashida lafiya ne?”
“ba wannan ba, ina kyautata zaton Jalal yafara neman matan banza” dan zaro ido tayi “Kamarya ya’akayi kasan haka? Kodayake ba abun mamaki bane ba, tunda duk wanda yake shan giya koya kwana a club ba abun mamaki bane amma gaskiya bana zaton Jalal yana neman mata amma”
“Enough!!! Baze yuwu ba khadija, iya sanina ďana ba manemin mata bane ba, ban san ya’akayi haka zata faruba, kinga yarinyar datazo gurinsa yanzu kuwa? Kinsan metace min ne? No baze yuwuba dole in dau mataki, Zina bala’i ce, dole inyiwa tufkar hanci”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button