ABDUL JALAL PART 2

“Shikenan daddy naji na gode, Jalal danka mashayi kuma manemin mata,
Daddy da ina neman matan banza da lalacewar da zanyi tafi haka, da ba tun yanzu ba matan banza sun dade suna zarya a gidan nan, dukda Jawwad yana rufamin asiri a abubuwa da dama bana tunanin ze yadda ya zauna da mazinaci, shikenan nagode amma kusani Wallahi bazan Auri wannaan shedaniyar yarinyar ba”
Mummy tace “dalla rufemin baki, kai har kanada bakin dazakace bakason Ilham? Ba rufamaka asiri zatayi ba, kanada bakin kiranta shedaniya ka…..
“Enough Mummy!!! Karki kara zagina waye silar komai, natsani Ilham natsani me sonta” yakarasa yana Zazzare ido, daddy yace “Jalal ya isheka haka, danme zaka dinga cewa ka tasani yarinya metayi maka haka? Lokaci yayi dayakamata kadinga dagawa mahaifiyarka kafa”
“Daddy kayanke min hukunci bakayi bincike ba, kasan bana maka karya, nidai fatana kayi bincike kadena zargina, daddy kanamin uzuri a abubuwa da dama ban taba zaton haka daga gareka ba, sannan maganar Ilham wani abune daba lallai in gaya maka meyasa nace bana sonta ba, duk ku kwantar da hankalinku Insha Allah a satin nan zanbar muku gidanku, in bar muku kasarma gaba daya ku huta”
Ya juya a mugun fusace yafito daga part din daddy, gaba daya jikin daddy yayi sanyi tausayin Jalal ya kamashi, ya juya ya kalli Ilham yace “Ilham mekika yiwa Jalal ne yake miki haka?”
Ilham cikin kuka tace “daddy ni bansan menayi masa ba, yakemin wannan muguwar kiyayya”
Mummy ta dinga rarrashin Ilham.
Jalal kam tunda yafito yaji wani abu ya tokare masa kirji, dakin Jawwad ya tafi yana zuwa yatarar da Jawwad kwance akan gado ido a rufe, Jawwad yana kwancene zuciyarsa ba dadi yarasa yadda zeyi da matsalar ke damunsa, jin Jalal ya shigo ne yasa Jawwad ya bude ido, ya tashi zaune ya dake ya boye tasa damuwar ya kalli Jalal yace “Lafiya kuwa naganka haka meya farune?”
Kasa magana Jalal yayi, sedai jijiyoyin kansa da suka mimmike idonsa jawur, se huci yakeyi kai dagani kasan akwai damuwa sosai.
Jawwad yace “ka gayamin mana meke faruwa?”
“Jawwad zan nemi visa, dole zan bar Nigeria a satin nan, kuma wallahi na tafi bazasu kara ganina ba”
“meyasa Jalal, meyasa zakace haka?”
“Jawwad nagama yanke hukunci, wannan karon karka cemin komai dan mutuwa ce kawai zata hanani tafiyar nan, zan bar Nigeria idan na tafi wallahi bazan kuma dawowa ba”.
A kwanakin nan sam Jawwad be gayawa Jalal shikuma tasa damuwar ba, sedai kokarin lallaba Jalal dayake yayi hakuri ammma fafur yaki se shirinsa yakeyi, sannan sam yadena shiga gidansu ya kashe wayoyinsa dan karma anemeshi.
Hanan da Jalila suna zaune suna hira da Inna a dakinta, Hanan tanata chatting ta dan dago ta kalli Jalila tace
“queen Haidar baya daga waya lafiya kuwa?” tai maganar a shagwabe
Jalila tace “kunfi kusa ai, nima bamuyi waya ba”
“nifa duk na damu a satin nan sam banji muryarsa “
Inna tace “waye kuma haidar, da kike kula dashi haka”?
“Sirikinki ne, kwanan nan zezo kiganshi kyakyawa dashi in gayamiki yafi mijinki Alhaji kyau, kai kaf family dinku babu me kyansa”
Inna tace “ke tafi can, anya akwai me kyan mijina, ai Imamu mijin Mairona ce kawai na yadda yafi mijina kyau”
Jalila da sauri tace “Imamu kuma, shine mijin kanwartaki?”
“Eh shine shima dan uwanane, dan Autan su Imamu shine baban Hanan”
Jalila tace “Inna to wai ina suke yanzu ita kanwartaki”
Inna ta danyi shiru tace “bari yarinya ta, Mu ukune a gurin babanmu nida mairo da yayanmu magaji, ni na Auri Alhaji dan yayar Innarmune, itakuma mairo ta Auri Imamu, dan kanin babanmu ne, yana son mairo sosai, ‘yan fashine suka addabi garinmu, watarana suka shigo suka harbi wasu, sukayi Garkuwa da wasu, akayiwa wasu daga cikin matan fyade aka kora dabbobinmu sannan aka sakawa bukkokinmu wuta, kafin hakan tafaru yayanmu magaji ya saida wasu daga dabbobin gadonmu nida mairo yarabamana kudin, to lokacin da ‘yan fashi suka shigo garin mairo da mijinta basu dawo daga kiwo ba, A wannan harin aka kashe yaya magaji, nida Alhaji da matar Yaya magaji, da yaranta da nawa yaran muka gudu abun be ritsa damu ba, haka muka baro garinmu muka taho nan bauchi, lokacin duniya na kwance akabamu masauki, muka cigaba da rainon yaranmu, bayan wasu shekaru A hankali bayan wasu shekaru muka dinga haduwa da wasu daga cikin ‘yan uwanmu, duk inda mukaa hadu sesu sedawo nan gurin mu su zauna, a haka har mukayi wannan yawan, Amma har yanzu danake miki wannan zancen bansan inda mairo da imamu suke ba, ni ko bangansu ba inga zuri’arsu, Hanan tana matukar kama da ita, amma dana ganki senaga kunfi kama da ita, komai naki irin natane, Allah yasa ke irin zuri’arta ce” Inna ta fashe da kuka,
Jalila tace “Allah sarki inna, kiyi hakuri kinji Insha Allah zaki ganta ko ‘ya’ yanta, amma ni ban san kakannina ba inada kanan shekaru suka rasu, maybe da Yaya Jawwad ne ze iya sanin wani abun amma ni bansan komai akansu ba”
Suna cikin maganar Yusuf yayi sallama ya shigo, su Jalila suka gaiaheshi ya amsa, ya nemi guri ya zauna ya kalli Jalila yace “‘yar Baba kije palourn kasa, second floor kinada bako” gaban Jalila ne yai mummunar faduwa da sauri Hanan ta mike zaune tace “Bako kuma?”
“Kece Jalila?” Yusuf ya tambayeta shiru Hanan tayi tana tunanin waye wannan kuma, ya biyo takan Yaya Yusuf, jiki a sanyaye Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi zata biyo Jalila, Yusuf yace
“ke dawo nan ki zauna, koke nace kije?”
Hanan tadawo ta zauna ta zumbura baki, tana nazarin waye kuwa wannan”
Jalila taje daki ta dakko hijjabinta har kasa tasaka, ta tafi a hankali ta tura kofar palourn ta shiga kanta a sunkuye tayi sallama.
“wa’alaikum salam warahmatullah” dan daga kai tayi ta kalleshi ido hudu sukayi tai sauri sunkuyar da kanta
Yace “karaso mana queen” Jalila a ranta too queen kuma iyayi, ta karaso ta zauna a kujerar da take facing dinsa,
“barka da dare”
“yawwa barkanki dai my queen fatan kina lafiya?”
“Am not queen Jalila sunana”
Murmushi yayi yace “to ai duk daya, koba haka Hanan take ce miki ba, kuma aini ya cancanta in fadi wannan sunan koba hakaba?”
Shiru Jalila tayi, “to ya gajiyar biki?”
“Gajiya tabi lafiya Alhamdilillah”
“Masha Allah, ni sunana Ahmad nasan kinganni a bikin Yusuf, kobaki ganni ba nina ganki kuma kinyimin Jalila, nagayawa Yusuf ya nemamin izinin zuwa gurin ki a gurin daddy, daddy yabani damar inzo, sannan yace inmuka cika wasu sharuda sannan kin amince ze bani ke” ya danyi shiru sannan yace “Jalila harga Allah kinyimin inasonki Aurenki nakeson yi tsakanina da Allah, amma bazan miki doleba se abunda kikace”
Shiru Jalila tayi tana wasa da yatsun hannunta
“queen kice wani abu mana” still ahiru tayi
“ko banyi miki bane? Ki gayamin ba komai, bazan miki dole ba”
Girgiza kai tayi alamar A’a yace “to gayamin abunda ke ranki”
Fafur Jalila taki magana yai murmushi yace “dago ki kalleni”
Noke masa kafada tayi kaman yanda yara sukeyi sannan tace “to ni me zance?”
“wow muryar ki da dadi Jalila, gaki shagwababbiya” murmushi ta danyi
Wayartace tafara ringing, ya kalleta yace “daga wayar mana”
Ta daga wayar tasaka a kunne Nanace tace “Baby ya kike dan Allah yaushe zaki dawo”?
“kai Nana wai yaushe zan dawo ba rana sena gama hutawa” Nana tace
“department dinku sukoma tun last week, nai shiru ban fadawa Abba kun koma ba, karyayi miki fada, sannan an kafe exams dinku yau”
“dagaske menasamu?”
“nidai nasamu upper credit, but Baby wallahi you are the most luckiest girl i ever seen in my life, kaf department dinku babu me points dinki, se zancenki ake, wasu sun sanki wasu basu sanki ba, lectures sunata a nuna musu ke”
“Alhamdilillah yanzu ina Yaya Jawwad kwana biyu baya daga waya?”
“Baby da banyi niyyar gayamiki ba, shiyasa naketa damunki ki dawo, Abba ya yadda Naja ta Auri yaya Jawwad, memakon yaya Jawwad yace masa bayasonta amma yayi shiru kinsan halinsa nan da kwana tara za’a kai kudin Auren sa gidansu Naja”
Jalila ta manta da wani Ahmad a gurin a razane tace “What, Nana dagaske kike dan Allah”
“Wallahi Baby dagaske nake, gashi yanata fama da Yaya Jalal shima wai ranar Asabar ze bar kasar nan, da se wani satin ze tafi, amma wani abun akayi masa a gidansu, yace wallahi inya tafi bazasu kuma ganinsa ba, ke yaya Jawwad yana cikin damuwa, gashi kusan kullum se Naja tasa anyi masa fada”
Mikewa Jalila tayi ta dafe goshinta tace “Nana am coming back this week Insha Allah, Idan har Abba yabari akayi Auren nan an rusa Rayuwar Yaya Jawwad gaba daya, kuma ina tausayin Hanan, zan dawo a satin nan Insha Allah, dole afasa Auren nan”
Sukayi sallama da Nana ta mike zata koma cikin gida Ahmad yace “Jalila lafiya kuwa? Naga kin shiga wani yanayi ko akwai damuwa ne?”
“A’a bakomai”
“Bari in kyaleki, nadawo na karbi lambarki zamuyi waya” gyada masa kai tayi ta fice da sauri.