ABDUL JALAL PART 2

Jawwad yaje gurin daddy, sun dan dade suna magana da Jawwad sannan yayi musu sallama yatafi.
Tunda Jalila ta koma gidan Naja take habaici tana yada magana
“ko anki ko anso, koda dariya koda kuka seta Auri Jawwad, Jawwad ba mijin kafura bane”
Jalila tabawa banza ajiyarta, duk yadda Naja taso ta tsokani Jalila, Jalila taki kulata.
Bayan daddy ya tafi, bayan la’asar Jalila ta tafi dakin Jawwad domin tana son yin magana dashi matuka, dakin ta shiga da sallama amma bakowa a palourn, bedroom dinsa taje tana knocking sannan ta bude dakin, ta hango Jawwad yayi rigingine ya lumshe ido kaman me bacci, sallamar Jalila ce tasashi ya bude ido, mikewa yayi zaune a hankali tareda kakalo murmushi yace “Babyn Ummi, ya gajiyar hanya? Na zata by now kina can kina hutawa”
“ina batun hutawa Yayana ba lafiya, ya jikin naka?”
“lafiyata fa kalau”
“A’a ni ban yadda ba ina zuwa”
Jalila takoma cikin gida ta hadawa Jawwad tea ta kawo masa, ya karba ya shanye yace “Nagode Jalila”
“meye kuma na godiya? Yaya Jawwad magana nakeso muyi da kai”
Gyara zama yayi yabata dukkan Attention dinsa Jalila tace
“Yaya Jawwad meyasa ka amince da Auren Naja?”
Ajiyar zuciya yayi ya danyi shiru sannan yace “Jalila Maama ta takura na rasa yadda zanyi ne”
“Yaya Jawwad, tun tasowarmu bantaba son wani sama da kai ba, amma ganin Hanan tana sonka, kuma Maama bata son Alkarmu tare, banason tayi fushi da kai, bana son ta fadi wani mummunar kalma akanka dazeyi tasiri a rayuwarka, Yaya Jawwad ba dan nadena sonka nakoma gefe na zuba maka ido na barwa Hanan kai ba, ina ganin kona barka Hanan zata maye maka gurbina, Amma meyasa zaka yadda da Auren Naja, Na tabattar Abba besan komai game da Wacece Naja ba, ita kanta Maama akwai abubuwan da bata saniba game dasu Naja” Jalila takarasa maganar idonta taf Hawaye,
“Yaya Jawwad, Hanan zata shiga damuwa sosai, tana maka so bana wasaba shiyasa na yadda da soyayyar da Hanan take maka ne dan samun nutsuwa da daidaituwa tsakaninka da mahaifiyarka, amma meyasa zaka Amince da Auren Naja?”
“Jalila bijirewa Auren Naja ze kuma jawomin wata damuwar ne, Har Yanzu Maama takasa gane Yaya mairo ba kaunarta take ba, ta riga ta zigata idan nace banason Auren nan komai ze iya faruwa, Amma ni kaina bana son Auren nan Jalila, Jalila na hakura da kene kawai saboda nasan idan har na Aureki bazaki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ta fannin dangin mahaifiyata ba, Jalila bayan tafiyarki Maama ta kirani akan maganar Auren tace Abba zemun zancen Auren muddin na bijire nace ke nakeso” sekuma yayi shiru yakasa cigaba
“Ina jinka bakomai karasa”
“Jalila Maama cewa tayi muddin na bijirewa maganar Auren Naja nannunawa Abba ke nakeso bata yafemin ba”
Zare ido sosai Jalila tayi, ta danyi shiru sannan ta girgiza kai
“Yaya Jawwad ka kwantar da hankalinka kayita Addu’a komai zezo da sauki Insha Allah, Allah ya ganar da Maama, Amma zaka iya Auren sister na ko Yaya?”
Shiru yayi bece komai ba
“Yaya Jawwad nida Hanan duk dayane, tana sonka sosai Zata kulamin da kai yadda yakamata, Insha Allah zanyi duk kokarin da zanyi amma bana son kacigaba da damuwa”
“To Babyn Abba na dena Insha Allah”
“Yawwa Yaya Jawwad dina, kamanta da wannan batun gaba daya, Mutum managarci kamarka be dace da mace irin Naja ba, kadena damuwa kar ciwo yakama ka”
Gyada mata kai yayi yana murmushi. Jalila ta mike ta fito daga dakin tanajin wasu Hawaye, harga Allah tana kaunar Yayan ta a zuciyarta babu macen dazata so tarasa managarcin mutum kamar Jawwad, harzata fita ta hango abu akan center table, dan haka ta dawo da baya ta tsya tana dubawa.
Jalal yana dakinsa yakuma tattar dukkan wani abu dayake bukata, ya hadesu guri daya sannan ya fito ya tafi cikin gidansu, dakin daddy ya tafi ya tarar dashi yana Aiki akan system dinsa.
Daddy na ganin Jalal ya ture system din yana murmushi
“Welcome my son”
“Thank you dad”
Jalal yasamu guri ya zauna sannan yace “Daddy naga bazan iya tafiya ba tareda nayi maka sallama ba, ina kaunarka fiye da tunani dukda kamin abunda bazan manta ba, amma bazan iya rabuwa da kai ta har Abada ba, daddy duk inda zan kasance a fadin duniya muna tare, Dubai zan tafi zamu dinga haduwa in kaje can, zan dinga zuwa Nigeria saboda wasu mutane, Amma Mummy taje ta riki Ilham a matsayin yar data haifa “
“My son nibana farinciki da wannan tafiyar taka, nafison ka kusada mahaifiyarka, Jalal idan katafi ba idon kowa akanka babu mece maka bari, bam san wace irin Rayuwar zakayi a can ba, Dan Allah Jalal
” Ya isa haka daddy karka rokeni dan Allah ????, Mummy bata sona bata kaunata, bata son farinciki na kanta kawai tasani, damuwarta ce kawai damuwa damuwar wani bata ta bace, daddy kasan yadda zuciyata takemin idan nasan cewa uwata na raye amma bana tareda soyayyar ta saboda wani dalili nata, kalli Rayuwar danakeyi saboda son zuciyarta, daddy Jawwad yayi yayi yaga nakoma mutumin kirki amma abu ya gagara, Amma wani dalili da ban taba tunani ba yana kokarin sani in rabu da shaye2, daddy idan har na cigaba da zama a kasar nan Mummy tanamin abunda takemin to bana tunanin bakin ciki ze bari in rabu da shaye2″ Hawaye sosai Jalal yake kaman mace
Jalal yakamo hannun daddy ya rike a cikin nasa, Sannan yadanyi murmushi yace “Daddy na kasan wani abu? Inada Ajiya a Nigeria bazan iya barinta gaba daya ba, in kaga nabar Nigeria gaba daya to Ajiyata na dauka, kamin fatan Alkhairi daddy na”
Yana gama maganar ya sumbaci hannun daddy ya sakeshi ya juya ya fice, daddy yarasa abunda yake masa dadi, idan Jalal bayaji ta wani fannin baya ganin laifinsa saboda tabbas rayuwarsa cike take da kalubale daban2.
Jalila takoma daki sukayi waya da Hanan amma batace mata komai akan Batun Auren da za’ayiwa Jawwad ba, sannan tacigaba da kokarinki kwantarwa da Jawwad Hankali tareda bashi karfin gwiwa,
Jalila sam taki kula Naja, ta maida ita kamar wata mahaukaciya, tayi zage zagenta da habaici amma Daga Nana har Jalila sukaki kulata.
Ilham ta shirya takuma zuwa gidansu gurin ummanta, domin din yadda sukayi da malaminsu,
“Ilham malam ya tabattar min Jalal baya neman mata, Sannan aikin da’akayi masa har yanzu yana nan ajikinsa, amma akwai matsala”
Da sauri Ilham tace “matsalar menene kuma?”
“Malam yace aikin da’akayi masa ya rage tasiri akansa, saboda akwai wanda yake ta kokarin rusa komai”
Girgiza kai Ilham tayi tace
“Umma wallahi wannan yarinyar ce da na nunamiki a Asibiti, hatsabibiya ce ta gaske ni Jalal yaciwa mutunci agaban iyayensa yace ya tsaneni ya tsani me sona”
Zare ido Umman tayi “Yatsaneki ya tsani me sonki dan Iskanci, kan bala’i ai wallahi daga shi har khadija basu isaba senaga abunda ya turewa buzu nadi”
“to ai Umma ba wannan bama, akan case din nan na zargin yana neman mata, yace kasar nan ze bari wai inyaso Mummy ta rikeni ni ta haifa bashi ba”
“Yabar kasar nan saboda me? Ke Ilham akwai aikifa baki kirin agabanmu, idan yaron nan ya tafi be Aureki bafa? Ita khadija me tace?”
“me kuwa zata ce ranar kaman ze rufeta da duka”
“tsinanniya ni dama ya daketa ta mutu in yaso yakare rayuwarsa a prison”
“Ahha umma akan me? Ta mutu akaishi prison bamu mallaki dukiyar damuke Hari ba?”
“to ai Ilham tsawon zamanki a gidan nan ba wani kokari da kikeyi, ace duk wannan shekarun ko kallon kirki baya miki sema tsana”
“to Umma yazanyi? Ni tun farko sonayi inyi me gaba daya kowa ya huta, kuma kiris ya rage amma ina shegen taurin kaine da shi kamar dutse ne a kirjinsa ba zuciya ba”
Umma ta numfasa tace “Munyi maganar da maman Yaseera, tacemin akwai wani malaminta a can Nijar, munyi da ita zanje ta rakani shima mu jarraba irin nasa Aikin mugani”
“to Amma Umma tayaya? Kasar fa ze bari”
“Dan ubanki kije kiyi duk yadda zakiyi, ki lallabashi in ta kama hada kuka akan bakya so ya tafi, ni nama rasa dalilin dayasa ya tsaneki haka wallahi, keba muniba to kodai yasan abunda mukeyine?”
“Haba dai yaza’ayi yasani? Ni dai Umma dan Allah ki kai Sunan yarinyar nan kawai intakama a kasheta, dan wallahi yanzu ba zargi nake ba, na tabattar ita yakeso”
“tayaya kika sani?”
“Umma ninake ganin abunda nake gani, wallahi Umma idan kinga Jalal ya tabani to bisa kuskure ne, koda wasa baya bari ya tabani, bama ni kadaiba kinsan halinsa bayason mata su rabe shi, amma ganin idona naga ya rungumeta, itakuma makirar tsinanniya tayi luf a kirjinsa, Allah ka dai yasan abunda sukeyi wallahi na tsaneta kamar mutuwata, kuma bakiga yadda baban Jalal din yake mutunta ba, keba shi kadai ba har Mummy bakiga yadda take mata ba”
Jinjina kai Umma ta shiga yi sannan tace
“kyaleni da ita, zata gane kuskurenta, nasan yadda zan bullowa lamarin zata gane bata da wayo, kafin inje gurin malamin, zan gayamiki yadda zakiyi kowa se ya tsaneta”
Haka sukayi ta hirarsu su saka wannan su kwance wancan.