ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Jalila kullum dare setayi salla takaiwa Allah kukanta haka take raba dare, gata gwana gurin yawan tilawar Alqur’ani, shiyasa Jalila ta yadda da duk wani abu da take aikatawa a rayuwarta take Nasara tasan dogaro ga Allah, riko da ibada da nacewa Alqur’ani shine matakin dukkan wata Nasara a rayuwarta, duk abunda ta tinkara setaga bayansa, ta taba duk wanda takeso komai matsayinsa amma babu abunda ze faru da ita, ta yadda da dukkan abunda ta roki Allah intaga bata samu ba to lokaci ne beyiba, ta yadda wannan shine matakin Nasararta a rayuwa wadda Umminta da akewa kallon tubabbiyace ta dorata a wannan tafarkin.

Tunda Jalal yace zeyi tafiyar Nan Mummy hankalinta yakasa kwanciya, gashi tasan yadda Jalal yakejin haushin nan nata baze saurareta ba, Amma yazama dole Jalal ya Auri Ilham dan cikawa Saudat Alkawarin ta wannan ne kawai abunda zatayi ta wanke laifin ta a gurin Saudat.
Mummy tayiwa daddyn Jalal magana akan yayi wani abu ya hana Tilon danta tafiya ya yabarta amma amsar daya bata ta mata ciwo
“da lokacin danake miki maganar ki hakura da tafiya karatu kikula da tilon danki da kinji magana ta da koba duka ba ko yaya da Jalal yaji maganarki, ko kin manta watansa bakwai kika dena bashi Nono, a wata bakwanma se lokacin da kika gadama, niba abunda zan iya ki kyaleni”
Ba karamin ciwo maganar daddy tayi mata ba amma ba yadda ta iya.

Ilham ta shirya taje dakin Jalal don jarraba ganin ko ze saurareta amma kusan ya kwashe komai nasa dake dakin nan se abunda ba’a rasa ba, tasan yana gidansu Jawwad dan tunda abun nan ya faru yakoma can dan haka ta bishi can gidan.
Jalila ta kaiwa Jawwad Abinci amma baya nan, se Jalal a palour, bata kulashi ba ta shiga tana gyrawa Jawwad bedroom. Tagama ta fito palour yana zaune inda Tabarshi yana daddana waya, ta fito tazo ta zauna a teburin dake gabansa, tana fuskantar sa, dagowa yayi ya kalleta, kallon dayake mata dukta tsargu, basarwa tayi tace
“Abokin Yaya wai dagaske tafiya zakayi?” A ranshi yace lallai yarinyar nan sekace bata san sunansa ba, nikam nace ai kaima haka kake cemata kanwar Jawwad ????,
Sauke idonsa yayi sannan yace “Kafin kiyi tafiya ai nagaya miki ko?”
“Aini ban zaci dagaske kake ba” dagowa yayi yana kallon ta karo na biyu yace “na taba yimiki karyane? Ko Ba kya son in tafine?”
“to inma ka zauna mekake karamin inka tafi hutunane ai, dan ba karamin wahala nake sha saboda kai ba, da inka tafi na huta banga abunda kayiba balle inji haushin ka, amma ni Su Mummy nake dubawa da Yaya Jawwad”
Ilham ce ta shigo dakin da Sallama Amma abunda ta gani zata iya kiranshi da mummunan gani, Amma ta dake tunda sulhu take nema, gaba daya suka daga kai suna kallon Ilham, tattara nutsuwarta ta boye damuwar ta ta tako a hankali tazo gaban Jalal ta tsuguna tace “Yaya gurinka nazo”
Bece mata uffan ba itama Jalila bata tashi daga gabansa ba, Ilham tace “Yaya Jalal san girman Allah dukda kace baka sona, dan Allah karkayi tafiyar nan, bana son ka tafi, Mummy ta shiga damuwa sosai bata iya cin Abinci se kuka takeyi dan Allah kayi hakuri nikaina zan shiga damuwa sosai, Jalal so fa ba karyane ba ni ganin gilmawarka a cikin gidanma ya isheni farinciki amma bansan dalilin dayasa kake kina hakaba “
Wani kululun bakinciki ya tokarewa Jalal rai a fusace yace ” dalla malama ki tashi kibani guri, ai bakinku daya Mummy karkinemi ki rainawa kanki hankali, bana sonki bana kaunarki kifita daga rayuwata tun kafin inyi miki Illa, babu wanda ya isa ya hanani tafiya ba kukan Jini ba ko Hawayen karfe zatayi ba ruwana, ta manta sanda nake mata magiya take tafiya tana barina, lokacin danake matukar bukatar ta, kinga dalla bacemin daga nan ko in ballaki” yakarasa yana zazzare ido gaba daya jikinsa bari yake

“wai dan Allah wace irin zuciya ce da kai, baka yafiya baka mantuwa, koma metayi maka ai ita takawowaka duniya, tana sonka shiyasa bata so ka tafi, Yaya Jawwad ya dena zaman gidan nan saboda bayason ya dinga tuna zakayi tafiyarka ka barshi, kalli yadda Ilham take kan gwiwoyinta tana kuka amma kai ko a jikinka meye hakane?”
Kafe Jalila yayi da idanuwansa da ita kanta wani lokacin suke bata tsoro, gashi yakara hade rai sosai.
Wani bakinciki yakara tokare kirjin Ilham kamar zuciyarta ta fito waje.

A hankali yafara motsa baki yace
“Wallahi idan har banyi tafiyar nan ba to bana raye, ba ruwana da halin da wani ze shiga saboda babu wanda ya damu da halin da nake ciki” yafada yana kallon kwayar idon Jalila
Kawai sukaga Jalila tana dariya, wadda ke matukar kara mata kyau tace
“to shikenan Ai seka tafi in gani” ta mike tsaye takuma kallon sa ta kwashe da dariya seka dawo, karka fasa tafiya naga ta inda zaka tafi ai, kekuma Ilham na dawo koki dawo da abunda kika dauka kokuma inzo da kaina”
Kawai ta juya ta fice ta barsu a zaune suna mamakin maganar ta.

Ina yinku ABDUL JALAL group irin sosai din nan fa ???????????? inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing duk bayan kwana biyu, kuna bari ina lalaci posting duk sati ????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
_PAGE 3️⃣5️⃣88

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

      _MY FIRST NOVEL _

Mikewa Jalal yayi ze fice yabar dakin Amma Ilham ta mike ta sha gabansa
“Haba Jalal yanzu bazakaji magiyar
danake maka ba, dan Allah Jalal kayi hakuri, karkayi tafiyar nan, zan shiga mugun yanayi dan Allah Jalal, wallahi ina sonka, tunda kuruciya ta har kawo I yanzun”

“Ke waini sa’an wasankine? Wallahi koki matsa ko in tattaka ki”
Ya tureta gefe ya fice Abunsa, Abun duniya duk ya dami Ilham, Jawwad ne kadai ke iya sarrafa zuciyar Jalal wani lokacin, yanada matukar kafiya da taurin kai, gaba daya tunanin ta ya kwace.

Jalila takoma cikin gida ta tattara abubuwan dazata bukata dan gobe in Allah ya kaimu zata koma makaranta,
Karamar wayartace ta cika dakin da ringing, Jalila taga bakuwar lamba ta share tacigaba da Aikinta, amma still aka cigaba da kira har kusan karo uku, seda ta danyi tsaki sannan taja wayar tasa a kunnenta
Ajiyar zuciya akayi sannan akace “Masha Allah, kin karyamin record bana kiran mutum sama da sau biyu, komai tsananin bukata ta kuwa, Amma ta dalilin son danake miki har sau hudu ina kiranki”
Sarai ta ganeshi amma ta maze tace “ko zan iya sanin da wa nake magana”
“Ohh am sorry dear, bankoyi miki sallama ba, balle mugaisai nafara miki surutu, Ahmad ne”
“Ok Allah sarki yakake ya gida ya iyali”?
“Alhamdilillah queen, kin tafi bako sallama, ban san zaki koma kano ba ai”
“Aikam abune na gaggawa ya tasomin, in ban manta ba ranar agabanka aka kirani”
“Hakane fatan kowa da komai lafiya”
“lafiya kalau, ya na baroku?”
“komai lafiya amma kintafi kin barni da kewarki, duk lokacin danake wani abu kona rufe idona ke nake gani Jalila, kitemaki zuciyar maraya” ya karasa maganar cikin sigar magiya
“Kai karka bada maza mana, yanzu idan abokan Aikinka sukaji wannan aise suyi Maka dariya, babban soja kaman kai kana haka akan mace, macenma wata ‘yar yarinya”
Murmushi yayi yace
“Jalila ai babu wani batun namiji ko soja in ana maganar fage irin na soyayya, ba ruwansa da matsayinka, girmanka ko mukaminka, ba ruwansa da na birni kona kauye, dan haka kidena wani batun maza”
“hmm Wannan bayani haka yakamata ka bude makaranta ka dinga bada darasi”
Murmushi yakumayi yace “Tunda haka kikeso ai se ayi, kece director mukuma dalibanki”
“Tab aini bansan komai a wannan harkar ba”
“Ahh haba dai?”
“dagaske nake fa”
“Aikam zan koyardake yadda yakamata”
“to shikenan seda safe, gobe in Allah ya kaimu zanje school”
“hakane hakan yayi kyau, Allah yabamu alkhairi, zamu hade a dreams zanbiyoki har kano kan shinfidarki”
Murmushi Jalila tayi “Allah yabamu Alkhairi”
Ta katse wayar ta danyi murmushi, can ta hango Nana ta shige bargo ga uban zafi se wani kashe murya take ba’ajin abunda take cewa, Jalila ta mike ta yaye bargon, Nana ta hada gumi amma ko zafin bataji saboda tana soyewa da Mahmud, Jalila tace “Allah ya shiryaki”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button