ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Ilham ta dade tana Nazarin me Jalila take nufi da Jalal baze tafi ba, danta fara karaya da lamarin Jalila yarinyar sekace Aljana idan tayi niyyar abu setayi shi.

Jawwad sam yaki kula Jalal gashi gobe in Allah ya kaimu karfe biyu na Rana ze tafi, yanzuma da Jawwad yadawo daga sallar isha’i daki yayi tafiyarsa ya kwanta, Jalal yabishi dakin ya zauna kusa dashi yace “Haba nawan yanzu fushi kake dani haka?”
Mikewa zaune Jawwad yayi yace
“Jalal dan Allah ka kyaleni, kace zaka tafi gaka nan ga hanya seka dawo”

“Jawwad nima inajin abunda kakeji a ranka, A tunanin ka rabuwa da kai abune me sauki a gurina, shekaru Ashirin da bakwai muna tare idan ban manta lissafin ba, Jawwad tafiyata shine samun saukinka, kaima ja maida kai karasa gina rayuwarka, bazan iya barin Nigeria gaba dayaba saboda ku biyu daddy zamu dinga haduwa a can dubai dashi”
“Jalal wannan ba uzuri bane ba, ni na gaba gayamaka na gaza da kai menakeyimaka na wahala, Allah ne ya hada jinina da kai bani da dan uwa Namiji kaidin nan dai tare muke faduwa mu tashi tsawon wannan lokacin, sannan lokaci daya kace Zaka barni tayaya zanyi farinciki Jalal”
“Am sorry Jawwad nasan babu dadi, kuma kana tunanin Wace irin Rayuwar zanyi a inda zanje, Jawwad Ina kokarin dena shaye2, A sanadinka a tsatsonka nasamu me haskamin bakar hanyar danakebi, dama lokaci dayawa kadaici da bacin rai dakuma miyagun abokai kesani kara kaimi gurin shaye2, Amma yanzu an janye miyagun abokai daga jikina, Jawwad idan na tafi inason in koma makaranta “
Sa sauri Jawwad ya kalleshi yace” dagaske kake? Da kanka kake fadin zaka koma Makaranta? “
” Kwarai kuwa zankoma Insha Allah “
Rungumeshi Jawwad yayi yana cewa” naji dadi dan uwana amma naso ace kana nan kusa dani, Amma dukda haka ni zan dinga biyoka Dubai din”
Kasan zuciyar Jalal ba wata makaranta kawai dan hankalin Jawwad ya kwanta ne
“kobakazo bama nizan dinga zuwa akai2”
Haka suka cigaba da hira.
Da wuri Yau Jalila ta shirya manu driver ya kaisu makaranta, ‘yan ajinsu Jalila sunyi murnar dawowarta nan aka dinga nunawa wanda basu santa bama, hatta malaman dasuke tsangwamarta suke ganin bata iya komai ba tabasu mamaki kwarai dagaske, saboda ba’a mata tambaya ta amsa a Aji, se lokacin data ga dama take zuwa lectures, wataran ma bata Attending, bata handout sedai in malami zeyi lectures ta dakko jotter, idan malami yayi ba dai2 ba bazatayi shiruba setayi magana, wannan bakin nata kesawa a koreta daga Aji, Akwai malamin da har test ya hanata yi, Amma a haka babu wanda yake da points dinta a kaf department din nan, hakika wasu mutanen ‘yan baiwa ne, shiyasa har Abada karka wulakanta mutane dan kowa baka san irin baiwar da Allah yayi masa ba. Ba iya dalibai ba hatta malamai sunyu mamakin Jalila ce takeda wannan kwazon.
Amma ita Jalila abunda yafi daukar hankalinta be wuce yadda har yanzu ake surutu akan abunda yafaru da Saleema da mahaifinta, Saleema ta warke amma bata iya shiga cikin mutane dan gaba daya ta dena zuwa makarantar, Sameera kam da farko ta tausayawa kawarta abunda yasameta Amma daga baya tunda aka sakesu daga police station tacigaba da abunda takeyi.
Jalila a ranta ta dinga jin anya kuwa ta kyauta abunda tayi, yanzu tayiwa Saleema dalilin dena zuwa makaranta, ta kunyata ta a idon duniya itada mahaifinta, Amma data tuna abunda Alhaji Kabir ya aikatawa Jalal, dakuma yadda ya dinga takuramata se yayi lalata da ita, da yadda ita kanta saleema suka addabi makarantar se taji hakan shi ya dace dasu.

Tun safe Jawwad ya bar gida sukayi sallama da Jalal yabar gidan.
Wajen sha biyu na rana Jalal yagama shirinsa tsaf, ya tsaya ya duba passport dinsa don yasa a karamar Jakarsa, Amma passport yace daukeni inda ka ajiye, ya duba ya duba amma be ganshi ba, hankalin sa ya tashi sosai ya duba kayansa be ganshi ba, gidansu yatafi ya duba dakinsa amma be barshi acan ba, yana kokarin fita daga dakin ne Mummy ta shigo dakin.
Ya tsaya yana kallon ta,
“Yanzu Jalal tafiya zakayi ka barni, laifina har ya kai ka kauracemin gaba daya, Haba Jalal koba komai nifa mahaifiyarka ce, kai kadai nake da baka tunanin halin dazan shiga inka tafi ka barni?”
Maganganun Mummy sam basuyi tasiri a zuciyarsa ba, seda yabari tagama gaba daya, kawai yaraba ta gefenta ya fice, danshi mugun haushin ta yakeji.
Mummy tarasa abunda yake mata dadi, ta zauna ta rushe da kuka a gurin, Abunda yakara bawa Jalal haushi be wuce yadda yana fitowa yakuma cin karo da Ilham ba, itama magaiyar take masa amma yai biris yai ficewarsa.

Jalal yayi duk tunanin daze yi amma ya rasa inda Passport dinaa yake, wayarsace tayi kara alamar sako ya shigo, Abuda ke cikin sakon ne ya razanashi sosai yasashi mutuwar tsaye wai an soke visa dinsa.
“Why!!!? Ya fada da karfi ji yayi yana neman ya fadi jikinsa na rawa, yanemi guri ya zauna ya dafe kai yai shiruu to laifin meyayi aka soke masa visa haka? Shidai yasan a Dubai be taba zuwa yayi laifi ba, Meyasa haka kodai Jawwad ne ya dauke masa passport, kai yasan Jalal beze masa hakaba Anya ba daddy ne yasa aka soke visa ba.

“Seka tafi in gani Ai, naga ta inda zaka tafi”
Maganar Jalila ya tuna, “to Amma tayaya Jalila zata iya sawa a soke masa visa, wata sani babba haka dazata saka ayi masa haka? Koma ita ta dauki passport dinsa, kai baya tunanin Jalila zatayi haka”
Amma dayayi shiru ya tuna irin gwaramar data hadawa Jeje da Alhaji Kabir abun ya zarce hankalin sa. Aikuwa a gigice ya tashi ya fito ya nufi gidansu.

Zahra batazo makaranta ba sunyi waya da Jalila tace mata batajin dadi ne shiyasa batazo school ba, bayan sungama lectures din farko Jalila tafita neman abunda zataci, gashi tana son zuwa banki ATM dinta yayi expire, dan haka ta siyi Ruwan jarka da biscuit tasaka a Jakarta ta nufi banki dan taje ta dawo da wuri, wayartace tafara ringing kaman karta daga, ta daga setaji muryar Ahmad, gaisawa sukayi suka shiga hira, Ahmad ya iya hira ga ban dariya shiyasa Jalila take sauraronsa, gashi ya iya soyayya da tattali, tabar department tayi nisa tana tafiya da waya a kunnenta taji Anyi wani jakin parking a bayanta, tsayawa tayi ta waiga a birkice dan ganin wani me kokarin ne haka, Amma wanda taganine yasa gabanta dukan biyar biyar, Jalal ne babu alamun Rahama a fuskar sa, ya tamke fuska sosai kamar be taba dariya ba.
Addu’a ta shiga yi a zuciyarta Allah yasa kar yayi mata tijara a bainar nasi. Ahamd yanata magana a waya amma shiru, Takowa yashiga yi yana nufota, yayinda ita kuma tarasa abunyi, ta kame a guri daya tana zare ido, yana zuwa yasa hannu ya janyo ta, ba musu tabishi ya bude gaban motar ya turata ya rufe, ya zagaya ya kunna motar yafizgeta a guje, tunda suka shiga motar bece mata uffan ba itama haka, Sedai tasaka hannunta ta rike kanta ta sunkuyar da kai dan tana matukar tsoron tukin Jalal, tukine na ganganci yakeyi kamar mara hankali.
Can Jalila taji yawan karar motoci ya ragu, A hankali ta bude ido taga sun doshi wani katafaren gida, yana zuwa masu gadi suka bude masa gate, ya shiga da motar yayi parking, se daga masa hannu sukeyi amma ko kula su beyiba,
bude motar yayi ya fito ya bude mata a tsawace yace mata “fito” ba musu ta fito yakuma fizgarta zuwa cikin gidan dabata san ko inane ba,
A can kasar zuciyarta tana ta Addu’a kuma tanada yakinin Jalal baze cuceta ba.
Suna zuwa wani tankasheshen palour, ya saketa ya kalli cikin idonta da yau ya raina fata take tsuma, a tsawace yace mata “Ina passport dina?”
“Ni ban dauka ba”
“Karya kikeyi”
“Niba karya nakeyi ba, ban dauka ba”
“Jaleela you are lying” jin yadda ya fadi sunan tayi ya tsarga tundaga kanta har kafarta.
“Nifa ba karya nakeba, dan Allah ka maidani, inada lectures fa”
“Ba abunda ya dameni bane, ni kika hana nawa uzurin kike gayamin kinada lectures, kibani passport dina”
“wai waya cemaka nina dauka? A ina zan ganshi?”
“keki gayamin jiya, kuma kika cigaba da rainamin hankali sena kakkaryaki, kibani passport dina ko in babbalaki”
“to Amfanin me zemaka bayan an soke visa?”
“Kekika dauka kenan? Ban abina tunda banaki bane, meyasa kikayimin haka? Akan me? Me nake tsinta a kasar nan banda bakinciki, Wace Rayuwa ce me Amfani nakeyi anan din, kowa yana kyamata da halayena babu soyayyar uwa a taredani ta fifita bukatarta akan farinciki na, se kokarin cusamin yarinyar dake neman halakani take, mahaifina danake da kwarin gwiwa akansa amma shike zargin ina neman mata, zaman menake a Nigeria banda takura da bakin ciki? Kowa kyamata yake akanme? Ba gara inje inda ba’asanniba inyi Rayuwata ba wanda yasanni ba, kibani passport dina” idonsa gaba daya ya koma Ja, jikinsa tsuma yakeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button