ABDUL JALAL PART 2

Jalila ta tsaya ta kalleshi tace “to ni zan shiga gida, Amma kabawa daddy hakuri”
“Hakurin me zan bashi? Jiya da daddare ya tafi U.K ai”
“to Mummy fa?”
“mezan mata, akanta nake kokuma wani abun nayi mata? “
“Ohh God kanada taurin kai, Just recently kace you want change, kuma yanzu kana wata magana, she’s your Mother, komene halinta kuwa, Aljannarka tana karkashin kafarata, ko kanaso kashiga wutane?”
Tayi masa tambayar kaman tana tambayar karamin yaro
Kallonta yayi amma bece komai ba
“Kadinga zuwa inda take, kayi hakuri da duk yadda take, kadena bata mata rai, kaji dan gidan daddyn sa, your Mum is so kinda, she loves you, you have to show her love too, batun Ilham kuma babu dadi kace baka son mutum agabansa kaji”
Tai maganar tana murmushi sannan ta shige gida.
Sumar kansa ya shafa yayi murmushi shima.
Gida ya shige yayi wanka ya ci Abinci ya tafi gurin Jawwad, Jawwad na ganinsa yafara dariya “mutanen Dubai ya akayine?”
Jalal ya dan hade rai “naga alama da hadin bakinka kanwarka tasa aka hanani tafiya”
“niba hadin bakina, amma nasani daddyn Hanan tagayawa, tun a lokacin nasan za’a soke visa dinka, amma nayi shiru ban gaaya maka ba, Amma ya akayi kasan itace tasaka, ina fatan zakayi hakuri karka hukunta ta”
“Hmm Jawwad kenan, yarinyar nan nasan halinta sarai, tun ana gobe zan tafi take dariya tace taga ta inda zan tafi, kaga inba itaba babu memun haka, akwai abunda tayi da har yanzu yake bani mamaki shiyasa akwai abubuwan da idan tayi bazan mamaki ba. Sannan yazan mata ta riga tayi, ban mata komaiba tare muka dawo ma”
Murmushi Jawwad yayi yace “zoka bani Labari, yaushe kuka dena fada ne? Ya akayi ka sakko da wuri haka? Nazata inka gano itace semunzo ban hakuri kar a hukuntata hukunci me tsanani”
“ta fini gaskiya ne, a da dinma abubuwan da take fada akaina gaskiya take fada, nina nake fadan rashin gaskiya, sedai tafiya tsiwa a gadarance take gayamin magana abunda yake harzikani kenan”
“to yanzu fa?”
“Bansaniba babana kasani agaba se antayamin tambayoyi kake, sekace EFCC, kaje ka tambayeta mana”
Dariya Jawwad yayi tareda dan jan kunenen Jalal dake cin Abinci ta sigar wasa yace “Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade nidai tunda baka hukunta taba kagama min komai”
Murmushi Jalal yayi sannan yacigaba da cin Abincin sa.
Sunata hirarsu shida Jawwad gwanin sha’awa,
Naja tana gaban mudubi, tasha kwalliya kaman zata gasar rawa, duk tabi ta tsuke jikinta, ta feshe jikinta da turare se taunar chewing Gum takeyi
Nana tace “Ehemm su hajiya Naja ko anyi sabon kamune wannan wanka haka?”
“bawani Sabon kamu, gurin Masoyina zanje tunda shi bezoba ai gara inje inda yake”
Jalila kallin Naja take kawai dan ba karamin tausayi take bata ba yanzu, rashin sani yafi dare duhu, da Jalila zata fadi wani abu data rusa duk wannan rawar kan da farincikin Naja har karshen rayuwarta, abunda ita kanta Najar bata san dashi ba “Allah ka kiyayemin Yaya Jawwad dina ka tsaremasa Imaninsa tareda dukkan Musulmi, dan a wannaan shigar da Naja tayi tana wannan masifaffen Kamshin indai Lafiyayyane namijine da wuya ya iya shallake wannan mugun tarkon na shedan.
Nana ko cewa tayi” kekam dan rashin aji dan yaki zuwa ke sekije inda yake, Sannan kalli shigar ki bata daceba kayan sun matseki”
“A’a ke kyaleni, A haka zanje irin wannan shigar da ita ake kama zuciyar masoyi kuma tana kara kusanci da kauna”
Itadai Jalila batace komai ba har Naja ta fice, sedai girgiza kai datayi tana cigaba dayiwa Jawwad addu’a.
Jalal yagama cin Abincin sa ya dakko system dinshi yana dubawa yace
“Jawwad next month fa zaka tafi Abuja gurin Aikinka”
Da sauri yace
“Saboda me?”
“Saboda nima haka na shirya maka kafin intafi, dan haka seka tafi”
“haba Jalal meyasa, Abba na kokarin bude mana store ne muyi ruining dinsa da kanmu kaga base nayi aikin gwamnati ba mun huta”
Dan tsurawa Jawwad ido yayi a ransa yace “mezanmaka a rayuwa Jawwad in biyaka kauna da alherinka, Sarai Jawwad yasan Jalal yanada tarin dukiya a kasa, Amma bayason ya kashe masa zuciya kar ya nemi na kansa”
“Kaga idan ka tafi nika barni da harkar kasuwancin zanyi mana, Amma seka tafi fa”
“Amma Jalal hakan……
” Salam Alaikum “
Muryar Naja ta katsesu gaba daya suka juyo suna kallonta
Wato har wani pink take saboda tsabar bleaching, saboda daganin wannan farin banata baneba, ga gaba daya dakin ya gauraye da kamshin turarenta tareda karnin mayukan da take Amfani dasu, tasaka riga da skirt na material dasuka kama jikinta matuka duk saman kirjinta a waje.
Dauke Kai Jalal yayi, yacigaba da danna system dinsa
“Masoyina gurinka nazo fa”
Tai maganar tana kokarin zama a kusada Jawwad, Jalal kam mikewa yayi ya shige bedroom din Jawwad, yana tunanin meyasa wasu matan basuda kunya basu san ciwon kansu ba, ace mace budurwa kaman wannan amma tana nanikar namiji haka ba kunya ba tsoro, hakama Ilham take masa wani lokacin, To Amma meyasa ita Jalila bata haka? Shidai yasan ba ruwansa da mata hasali yana gudun taba macen daba maharramarsa ba, Amma ita Jalila bayajin komai dan ya tabata, yana jin kaman hakan shi a gurinsa ba laifi bane, sannan duk lokacin da hakan tafaru a tsakanin su yana ganin matukar tsoro da rikicewa a idonta. Haka yacigaba da zancen zuci yanata tunani daban2.
“Haba masoyin, Meyasa baka zuwa inda nake Yaya Jawwad, wallahi banajin dadin abunda kakemin sam baka nunamin soyayya”
Matsawa yayi daga kusada ita yace “Naja soyayya daban Aure daban a yanzu keba halalina bace ba meyasa zakimin irin haka? Ke ko kunya ta bakyaji ne haba Naja kidinga kama kanki mana”
Matsowa takumayi jikinsa tana kashe murya tace
“meye wani kama kai, Aurena fa zakayi dan Allah kasaki jiki ka nunamin soyayya haba Jawwad” takai hannu tana shafo fuskarsa
Gaba daya jikin Jawwad rawa yakeyi Tsaki yayi yana kokarin mikewa, tunda ya fuskanci bazata ganeba
Riko hannunsa tayi tana kokarin Rungumeshi, A fusace ya hankadeta kasa yana kokawa da numfashi,
Tashi takuma yi tace “bazanyi zuciya ba” sekace mayya take kuma shanye ido kamar tana maye, ta rungume shi.
“Ke!!!” ya daka mata tsawa a fusace wadda seda yasa Jalal fitowa a sukwane yayi jifa da ita
“ki tashi kibarmin dakina, Allah ya shiga tsakanina dake ban taba aikata mummunan sabo ba bazan fara akanki ba, get out from my room ko in illataki” idon Jawwad yayi jawur jikinsa yana rawa, gaba daya ta kasa gane dama Jawwad yana fushi haka? Jalal ya karaso ya rike Jawwad yace
“Jawwad kyaleta yi hakuri, calm down”
“bazanyi hakurin ba ka kyaleni, wallahi takuma zuwarmin daki sena bata mamaki, bata san a bisa umarnin Maama zan Aureta ba, in bahakaba me zanyi da ita? Me take dashi daza’a kalla a ce wannan mace tagari ce ya dace a Aureta? Itada mahaifiyarta sun shiga sun fita sun rabani da kanwata shekara da shekaru suna uzzuramata suna bata mata rai suna cimata mutunci, na hakura, ance sena Aureta na hakura nayi biyayya, be isheta ba seta nemi tasana aikata laifi me muni”
Kallon Naja Jalal yayi, kaddai ace wannan yarinyar ya yadda ze aura, Amma Jawwad hakurin nasa yayi yawa. Naja ba karamin mamakin abunda Jawwad yayi mata tayi ba, ita babban mamakinta bata taba ganin yana fada ba, saboda tasan mutum ne me kunya da kawaici.
Jalal yace “Naji kadaiyi hakuri”
“bazanyi hakurin ba Jalal”
Jalal yace “da nine da yanzu kacemin masifaffe, haba dan uwa Aliyu Haidar zakin Allah, katangar sikari na Hanan kowa ya jingina da kai seya lasa, fari me farar aniya kai a cikin masu sunan ma na dabanne kayi hakuri” Jalal yana lallaba Jawwad ne saboda yasanshi be iya fushi ba, seya shafe shekaru be fushi ba amma idan yayi abun baya kyau.
Naja tace “kagama duk masifunka, wallahi nidin dai ni zaka Aura kuma zaka gane baka da wayo, bari Maaman ta dawo zaka gane ka taka tarkon mace.
Jalal ya hanashi magana, suka kyaleta a gurin yaje ya dinga rarrashin Jawwad, ana haka Hanan ta kira wayar Jawwad, Jalal yai murmushi yace “kaga ka daga wayar nan ayi maka kalamai, zaka huce”
“A’a ka kyaleni, am not in mood”
Aikuwa Jalal ya daga wayar suka gaisa yace “Hanan ga mutumin naki, Amma ransa a bace yake fa”
“Subhanallah dan Allah wayakai min zuciyarsa bango har akasamin shi fushi, dan Allah ka bashi wayar”
girgiza masa kai Jawwad yayi alamar baze karba ba
“kiyi hakuri, baze karba ba fa, ransa a baci yake”
Hanan a shagwabe tace “Shikenan tunda baze karba ba amma zuciya ta bazataji dadi ba, Allah kuka zan tayi duk daren nan, wallahi har naji tawar zuciyar tafara nauyi”
Ai tuni Jawwad ya zare wayar a hannun Jalal yasa a kunnensa yace
“Hello Hanan kina jina?”
“haidar dina me akayi maka?”
“wani little issue ne, kuma yanzu komai yayi settling”
“little issue baze bata maka raiba”
“ki manta kawai, kar inga abunda yasamin ke kuka”
Jalal yaji Jawwad ba kunya anataya masa kalamai agabansa. ya minstili kafar Jawwad yace “dan rainin hankali kawai”
Jawwad yai murmushi
Jalal ya daga masa hannu ya wuce gida.
Yanayin maganar Hanan kaman Jalila, tuno moments dinsu yayi dazu dayake ta dage bilhakki tana masa fada, da yadda take da ido idan batada gaskiya murmushi ya dingayi shi kadai, har ze kwanta ya tuno maganganun Jalila game da Mummy.
Mikewa yayi ya nufi cikin gidan, babban palourn Mummy yasa hannu ya bude kofar. Salla takeyi yanemi guri ya zauna, rabonsa da dakin nan harya manta yana jiranta yana sake2 a zuciyarsa mema ze ce matane?.
Ta idar tagama lazimi, ba karamin mamakine yakamata ba ganinsa a part dinta
Ta kalleshi tace “Lafiya kuwa? Ashe baka tafi ba, uwarka wadda tafini, wadda take baka abunda bana baka ka fasa tafiya saboda ita.
” Wakenan? “
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ???? ????