ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL (2020)
Story and written by
AISHA HUMAIRA (daddy’s girl)
PART 2
_PAGE 3️⃣7️⃣90
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
MY FIRST NOVEL
“wakenan?” ya tambayi Mummy yana kallonta
“eh da ita yarinyar daka dawo dan ita mana, tunda tana maka abunda bana maka, wallahi kaji tsoron Allah, ba irin Magiyar da banyi maka ba, Amma kayi biris amma yanzu dayake tafini ai gashi kadawo”
Tsyawa yayi ya zubawa Mummy ido tagama, Yayi tsaki ya tashi ya fice yana masifa.
Haka yakoma dakinsa yana mita yana tunanin meyasa ma yaje inda take.
Jalila tanata lissafi gobe su Abba zasu dawo, dan haka ta tsananta Addu’a Allah yabata sa’a yasa Abba ya janye batun Aurawa Jawwad Naja.
Yauma Jalila taje school, sun kammala lectures, sunfi to itada Zahra, Zahra tace
“Yawwa nikam Jalila naji Wata suna hira tace wai jiya wani hadadden gaye yazo yasaki a mota ya tafi dake, amma wai dagani dan shaye2 ne dan wuyansa hada sarka, ga wani irin Aski akansa, ina fatan lafiya ba wata matsalar bace?”
Dan karamin tsaki Jalila tayi aranta tace”
dan jaraba da masifar mutane komai kayi idonsu akanka
“Eh haka akayi, seme kuma?”
“A’a ba komai dama nayi tunanin ko mutanen baban Saleema ne”
“basu bane, Yayana ne” Jalila tabata amsa a takaice, Dan zare Ido Zahra tayi
“dama kinada yaya dayake shaye2, na zata Yaya Jawwad ne kawai Yayanki”
“Akwai wani to, kuma akansa nayiwa Alhaji Kabiru baban Saleema, abunda yanzu yana daf da zuwa prison shida ‘yan tawagarsa”
“Amma Jali….
” Ke zahra kin isheni wallahi, nagaji ga yunwa ina ji se faman tambayoyi kikemin, sekace wata likita, haba se Allah ya kaimu gobe”
Inda sabo Zahra tasaba da halin Jalila, tanada saukin kai Amma tanada tsari a komai nata, in bakasan halinta ba zakace batada kirki ne kawai, bata da san yawan tambaya.
Mummy ta bawa Ilham kudi tace ta kaiwa Nana ta ajiyewa Maama in ta dawo a bata, Ilham ta karba harta shiga gidansu Nana wani tunani ya fado mata a rai, dan haka tayi murmushin mugunta tashi. Tana fitowa hakan yayi dai2 da dawowar Jalila daga makaranta sukayi karo a kofar gida. Ilham ta tsare Jalila da ido tana mata kallon zaki gamu dani ne.
Jalila tace “Ilham wai kin manta maganar danayi mikine? Ki dawomin da Al’qur’anina tun muna sheda juna dake”
Ilham ta rike kugu ta kalli Jalila “idan naki fa? Me zakiyi?”
“Aimeyi baya fada se dai kigani a aikace, zakiga matakin dazan dauka, ki kawomin abina na gayamiki”
“ina jiran ganin matakin dazaki dauka din, amma kafin ki dauka ni ki saurari nawa”
“banida lokacin saurarar duk wani shirmenki, ba abunda kika isa kiyi min, nagama magana Ilham”
Jalila tasa kaii ta shige gida.
Kwana hudu kenan basu kara haduwa da Jalal ba, haka nan yaji yana kewarta sosai. Koba komai yayi missing neman maganar ta.
Sannan tunda abun nan yafaru tsakanin sa da Mummy be kuma shiga cikin gidan ba. Mikewa yayi yafito zetafi gidansu Jawwad.
Yana kokarin fitowa daga part dinsa Ya hango Ilham a jikin mota tanata boye kudi a jikinta, yana ganin haka yasan bata da gaskiya amma bebi takanta ba ya fice.
Jalila tana zuwa ta dire Jakarta ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar Azahar ta kwanta bacci, se la’asar ta tashi, tayi sallar la’asar sannan taji tana jin yunwa.
Jalila tana zaune akan dadduma kafin tabar kan daddumar ta, Ahmad ya kirata suka dinga hira har kusan 40 minutes, Nana kallon ta kawai takeyi seda tabari tagama sannan tace
“Jalila wai dan Allah ina kika samo wannan Ahmad din, iya sanina ba kya son duguwar waya amma kalli yadda kika zage kina waya”
Jalila tayi murmushi sanna tace
“Nana a Bauchi na samo shi, yanada kirki sosai”
“kinga niba wannan ba magana nakeso muyi masu mahimmanci”
“inajinki amma ki hanzarta inajin yunwa”
“bawani in hanazarta, ki zauna kigama wayar se yanzu zakiji yunwa?
Jalila dan Allah ki gayamin hakikanin meke tsakanin ki da Yaya Jalal?”
Jin maganar tayi wani banbarakwai, batayi zaton jin wannan tambayar ba
“kamar yaya? Kinga wani abune da baki yadda dashi ba? Meyasa kikamin wannan tambayar”
“Jalila ruwa baya tsami banza yadda Ilham ke takura tsanarki tabbas wani abun tagani, tana claiming kuna soyayya ne, nima da nayi wani nazari zancenta yana kusada gaskiya”
“Mtseww niban san yakuke so inyi ba, da muna fada da shi, ance banida kunya inamasa rashin kunya, yanzu na dena ance ina sonsa to ya zanyi, Nana niba son Jalal nakeba, ina tausayinsa ne musamman danaji labarin waye shi, Nana a baya nikaina nasan na bata masa rai dayawa, yadda nake masa rashin mutunci da bakaken maganganu, naga ban kyauta ba sannam ba’a gyara da barna, muddin kanaso ka temaki mutum ya dena aikata laifi indai zakayi masa hayaniya baze dena ba, zaka kara tinzira shine, na fuskance shi yanada mataukar saukin kai, na gane hakanne a zuwan dasu Hanan suka danyi, Hanan gashi sa’ata ce, tafini tsiwa amma yana sakarmata fuska har yayi mata wasa, ita bata masa rashin mutunci kamar ni, shiyasa nima na sassauta yi masa wulakanci,
Amma babu soyayya tsakanin mu, ina fatan kin gane”
Mikewa tsaye Nana tayi tana shirin fita ta waigo tace
“Naji amma ban yadda ba” Nana ta fice daga dakin, tunani Jalila ta dingayi kozata gano wani dalili ne yasa ake kallon soyayya ce tsakanin ta da Jalal amma bata ganiba share wannan tunanin tayi ta mike ta fito itama domin neman abunda zataci dan ba karamin yunwa takeji ba.
Koda ta duba kitchen ba’ayi girki ba bakomai tayi tsaki ta fito daga kitchen din.
Daki takoma ta hado goldenmorn dinta ta fito farfajiyar gidan domin shan iska, tasamu kujera ta zauna tana cin Abincinta, Abba takira a waya yakara tabattar mata da gobe Insha Allah ze dawo, ji take kaman ta Jawo gobe Abba yadawo dan ta kagu ta dau mataki akan Naja.
Tanata wannan tunanin aka kira wayarta, A zatonta Ahmad ne amma se taga bakuwar lamba dagawa tayi tasaka a kunnenta tareda yin Sallama
Caraf taji matar ta Ambaci sunan ta “Jalila yakike ya gida?”
“lafiya kalau Alhamdilillah”
“Antyn Jalal ce, nasan baki gane me maganar ba”
Murmushi Jalila tayi tace
“yi hakuri Anty ban dau muryarki bane, ya gida ya kukaje gida ranar”
“lafiya kalau nasan baki dauki muryata bane, Jawwad nakira nace ya turomin lambarki mudinga gaisawa, ya mutan gidan naku?”
“lafiya kalau Anty, yasu Mahmud?”
“Ahha Mahmud Nana zaki tambaya shi, muntafi da kwana uku yakoma U.K”
“Allah sarki, aikam kullum suna tareda Nana a waya”
“Aikam naga shi can nasa hankalin ya karkata, se fatan Allah ya tabattar da alkhairi”
“Hakane Ameen ya Allah”
“Jalila ya Amanata dana bar miki?”
Dan murmushi Jalila tayi tace
“Yana nan Anty”
“Kundena fadan dai ko?”
Murmushi Jalila takumayi tace “Anty kenan”
“Au kunya na baki? Jalila bamuda kalaman dazamuyi Amfani dasu gurin gode miki akan namijin kokarin da kikeyi keda Jawwad akan Dan uwanmu mungode Allah yasaka maki da Alkhairi”
“Haba Anty meye wani abun godiya kuma? Ni banga wani abu da nakeyi ba”
“inke baki ganiba mu mungani ai, ko iya yanzu kin taka rawa gurin canza abubuwa dayawa a tareda shi, munyi waya dashi yacemin daze bar kasar nan kika hanashi”
“hmm sa’a kawai nayi, nazata ma ze min duka, Allah yakara shirya shi, nima nagani ya rage Abubuwa sosai”
“Ameen Jalila, haba baze iya dukanki ba ai, he respect you fiye da yadda kike tunani, ki kulamin da amanata Jalila, inaji a jikina abubuwan da Jalal yake zezama tarihi sanadinki”
“Allah yasa, Munagodiya Jalila, Allah ya jikan magabatanki”
Jalila ita bataga me tayi ake mata wannan godiyar ba, Jalal din da banda fada ba abunda ke hadasu, dan haka Tace
“Anty yaushe zanzo abani turaren maiduguri ne? “
“Kibari in Aurenki yazo har kano zanzo in hadaki, kamshi sekin gaji, Allah ya nunamin Aurenki”
Dariya Jalila tayi ta kashe wayar, Antynsa tanada saukin kai, gata da abun dariya, Amma ita bataga me tayiba daza’ayita yimata wannan godiyar ba.