ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Washegari da safe Jalila bata tafi makaranta da wuri ba, seda tagama gyara gidan dan kusan kwana biyu Naja bata gidan, Halima dama Maama ta dade da sallamarta, Manu direba be dawo daga kai Nana ba, tunda ita Nana da wuri ta tafi school yau,
Taita gyaran gida, da kokarin dora girki saboda dawowar su Abba, be kamata abar gidan bakowa ba gashi ba’ayi girki ba.
ta fito ta leka part din Jawwad, taga inya tashi ta kaimasa Abinci, Amma ta hango Jalal yana shan sigari, Jawwad kuma baya palourn, da niyyarta ta fadawa Jalal bakar magana amma tafasa ta shiga palourn. Batayi sallama ba unexpected ya daga kai ya ga Jalila, hade rai tayi sosai taki kulashi shima be kulata ba, ta duba ta kalleshi tace “Ina Yaya Jawwad?”
“ki duba mana” yabata amsa a takaice
“Ina zan duba?” ta tambayeshi a ransa yace “lallai yarinyar nan kyaleta yayi bekuma kulata ba yanata shan sigarinsa, tambayarsa takuma yi
” wai yana ina? “
“Zoki duba rigata kona sashi a ciki”
Bude baki tayi tana kallon sa, Jalal dan rainin hankali ne, amma ta shareshi ta dakko wayarta takira Jawwad be dauka ba, tsaki ta danyi taje tayi knocking kofar bedroom din Jawwad amma ta tarar yana bacci. Mayarwa tayi ta rufe ta juyo zata fita, Amma Jalal bashida niyyar dena shan taba, gashi yana kallon boom TV ne music ne kawai yake tashi, yana shan sigarinsa yana lumshe ido, ya jingina a jikin kujera. Dan girgiza kai tayi tazo gabansa ta tsaya ta dauki remote ta mayar saudi qur’an, bude ido yayi ya kalleta sannan yace “Meye haka?”
“Abunda ka gani” ta bashi amsa
“mayarmin inda take da farko”
“Bazan mayar ba” dago Jan idonsa yayi yana kallon ta, wani tunani tayi a ranta, ta fuskanci fitsarar da rake masa baya sashi dena abunda yakeyi, dan haka tace
“Ka karyane? Da safiyar nan kake shan sigari, kamanta me likita yace maka ne? Kobaka son lafiyar kane?”
Shiru yayi ya dauke kai, ba karamin haushi takeji tana masa magana ya mata banza ba amma ta dake tace
“Am talking to you, kamanta you said you want change, and i promise to help you out, please badanni ba a kashe sigarin nan please, na zata dena mu’amalarka da wannan jakin Jejen zesa ka canza kadena shaye2, amma meyasa har yanzu baka dena ba?”
Juyowa yayi yana kallonta, tayi kalar magiya, a hankali yace
“ba lokaci daya nafara shaye2 ba, don’t expect me to stop it at once, Jeje ya dade yana cutar dani, na dade ina shaye2 bazan iya dena wa lokaci daya ba”
Tausayinsa ne yakamata, dan haka tace “I understand, kadena sha dayawa, a hankali zakaga ka dena” gyada mata kai kawai yayi, ta dan kalleshi maganar zahra ta tuna, “wani handsome guy”
Ba karya Jalal yanada kyau, inama ba ya wannan shaye2, da seyafi haka kyau, Amma tana fatan Allah yasa abunda ta shirya akansa yayi tasiri ya dena shaye2.
“inaso kamin wata Alfarma”
“fade ta Allah yasa zan iya”
“zama ka iya, ba me wuya bace ba”
“inajinki”
“Dan Allah kadena saka sarkan nan, you are Muslim, bekamata ace kana yawo da itaba, da dinma nasan saboda Jeje ne kaima ka kwaikwaya please ka cireta”
Kallonta yakeyi amma bece komai ba, can kuma ba tareda ya cire sarkar ba yace
“meyasa idan aka kirani da dan shaye2 kike jin haushi bayan kema kina gayamin? Dan shaye2 mara tarbiyya wanda ya raina iyayensa, idan wani ya gayamin kinajin haushi, Amma kekina gayamin”
Gaba daya taji jikinta yayi sanyi, har bataso ta tuna irin bakaken maganganun datake masa abaya, musamman idan ta tuna labarin Rayuwarsa tabbas tayi wauta, amma tace
“Waye ya kiraka da dan shaye2 naji haushi?”
“mutane dayawa, bari in tuna miki daya, Oga KB mahaifin Faruk, ban taba tunanin yadda kika tsaneni a wannan lokacin ranki ze baci dan anci zarafina baa”
“har yanzu kanajin haushin abunda nayi maka abaya ko?
” ko kadan gaskiya kika fada ai, banida tarbiyya, ban cancanci zama
Abokin yayanki ba kaddararsa ce tareda tawa shi…….
“Enough dan Allah, wannan abune daya riga ya wuce please”
Kallonta ya kumayi sannan yasa hannu ya cire sarkar wuyansa yace “Insha Allah nayi alkawarin bazan kuma saka sarka a wuyana ba”
Murmushi tayi “Are you serious”
“dagaske nake miki”
“kai gaskiya na yadda you want change, Allah ya shirye ka da gaggawa” murmushi yayi yace
“Ameen ya Allah”
daga nan ta mike tayi waje a ranta tace
“da haka Insha Allah kafin inyi Aure seka dena shaye2 in Allah ya yarda”
Yau fasa zuwa school tayi ta zauna ta shirya Abinci saboda dawowar su Mummy, bayan tagama ta kaiwa Jawwad nasu, ta gyra ko ina a gidan se kamshi yakeyi.
Bayan tagama komai ta zauna tana tilawar Alqur’ani, wajen karfe daya Abba suka dawo gida, ta dinga murna tana musu barka da hanya, duk hassadar mutum yasan gidan nan ya sha gyara amma Abba ne kawai ya yaba, Maama nunawa tayi bataga ma me akayi ba.
Bayan sunyi salla ta kawo musu Abinci. Takoma dakin su.
se la’asar Nana ta dawo daga school nan ta dinga murna su Maama sun dawo, Jawwad seda magariba ya shigo cikin gidan yayiwa Su Abba barka da dawowa, wannan karon kamar kullum Abba yarabawa kowa tsaraba sunata murna, sun hadu a palour ana hira.
Abba yace “Jawwad ranar Asabar Insha Allah za’akai kudin Aurenka kamar yadda Maamanka ta bukata, inda wani shiri da kake ganin zakayi to kaje kayi, Jalal yagama komai next month Insha Allah zakafara zuwa gurin Aikinka”
Wani irin gumi ya dinga tsatstafowa Jawwad, yariga yagama karaya, sannan yana jin matukar kunya da nauyin ya bude baki yagayawa mahaifinsa baya son zabin da mahaifiyarsa tayi masa, Jalila ta kurawa Abba ido alamar bata gamsu da abunda yafada ba, Abba ya kalleta yace “ya dai ‘yar Baba? Kokinada magana ne?”
Juyawa tayi ta kalli Maama data tsareta da ido, magana kam akwaita a bakinta amma ba’ a gaban Maama ba, girgiza kai tayi alamar A’a, ta mike ta tafi dakinsu tanata safa da marwa, tana tunanin ta ina zata fara yiwa Abba bayani, tasan kotayi Maama karyata ta zatayi.
Gajiya tayi da sintirin datake taje ta bude wardrobe zata dau towel tayi wanka, ta bige wata jakar Naja ta fado kayan ciki suka zubo dayake bata zugeta ba, a sama inner wears dinta ta dora a kai, amma kwayoyi ne da kwalaban syrup a cikin jakara, binsu da ido Jalila ta dingayi yayinda tayi mutiwar tsaye.
Da sauri ta durkusa ta tattare mata su ta mayar mata da jakarta yadda ta ganta, nan tunani yakara yiwa Jalila yawa bazata taba bari a Aurawa namiji kamar Jawwad wannan tanbadadiyar ba,ko Nana bata gayawa abunda ta gani ba, tayi shiru da bakinta.

Wasa2 duk yadda Jalila taso ganin Abba personally Maama ta kankane, ta tattare a part dinsa bata matsawa ko nan da can, seda aka kai kudin Auren nan, naira dubu dari Abba yaje ya kaimusu, su Yaya mairo hada kira wayar Maama tana mita wai duk Arzikin da Allah yayi musu amma ace kudin Aure akawo dubu dari, mecec dubu dari a kudin da suke dashi, Maama taita lallabata tace tayi hakuri zasu hade a kayan lefe.
Yayinda gefe abun duniya ya damu Jawwad, begayawa Hanan halin dayake ciki ba, ko Abinci baya iyaci, duk ya rame. Jalila da kanta taje ta dinga bashi kwarin gwiwar yacigaba da Addu’a komai zeyi dai2.
shikansa Jalal abun ya dameshi, meyasa za’ayiwa namiji Auren dole, ko mace be kamata ayiwa ba balle Namiji, shima Jawwad saboda nusaranci da kunya baze iya cewa baya sonta ba, wani lokacin kawaicin Jawwad yana batawa Jalal rai.
Jalal yanata tunanin wani taimako ze iyayiwa Jawwad, dan shima baze bari ayi wannan Auren ba, tunda Jawwad baze iyaba zeje yasamu Abba da kansa yagaya masa Jawwad baya son yarinyar nan, yana wannan tunanin yaji message ya shigo wayarsa,
Koda ya karanta, tsayawa yayi yanata juya message din shidai yasan tabass wannan message bana sa bane saba lamba akayi, dan haka ya barshi a matsayin anyi missing number ne aka turo masa, dan hukumar dasuka turo message din da sun san wayeshi sun san laifin dayake aikatawa da basu turomasa abunda suka turoba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button