ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Maama ta cazawa Jawwad kai akan Naja, yana zuwa dakin ta shiga yi masa fada “Wallahi Jawwad ka kiyayeni tun ban bata maka rai ba, shine ka hada kai da wannan makirar yarinyar take kokarin ziga mahaifinka akan Auren nan ko? To wallahi ka kiyayeni akan Auren nan zan iya cimaka mutunci, kuma in har muna raye baka isa ka kuskurewa Auren nan ba, indai zanyiwa yayata biyayya kai waye da bazaka yimin ba? “
Sunkuyar da kai Jawwad yayi yace” kiyi hakuri Maama, niba ina kokarin kuskurewa Auren nan bane, kiyi hakuri dan Allah “
“ni rufemin baki, se anyi magana kadinga wani ayi hakuri, Naja tagayamin wulakancin dakake mata, ka fifita waccan yarinyar akanta shima ka kiyayeni Aure zakuyi da Naja, dole ka dinga janta a jiki ku fuskanci juna”
“to Maama yadda kikeso haka za’ayi insha Allah” duk abun nan Naja na gefe a zaune tana tauna chewing gum, tana hararsa, da Nana tana dakin Maama itama, amma bacin rai yasa tabar dakin.
Har Jawwad ya yunkura ze fita yabar dakin, Naja tayi karaf tace “Yaya Jawwad dan Allah zan shirya zaka kaini anguwa” shiru yayi bece komai ba, Maama tace “kobazaka kaita bane?”
“zan kaita bari inyi sallar la’asar”
Haka ya taho ransa babu dadi, yarasa me yake masa dadi, gaba daya Maama ta canza yaya mairo kullum cikin zigata take kansa har wani sarawa yake yi, ya nufi dakinsa amma yana zuwa dakinsa abunda ya tarar ya bashi mamaki, kunnuwansa suna jiye masa kira’ar Jalal, yana karanta qur’ani , wanda rabonda Jalal ya karanta Al’qur’ani baze iya tunawa ba, to mutumin dabe damu da salla ba, ina zeyi karanta alqur’ani.
Jalal yana cikin biyawa ya kakare, Jawwad yakarasa masa, tuni Jawwad ya manta da bacin ran dayake yi yace “Jalal yau kaike karatu haka? Amma naji dadi, yaushe rabo”
“kanwarka ke kokarin ta kureni, nace mata na manta tace senayi shine nake tunowa naji ashe da saura, haddar bata gama zubewa ba”
Jalila tace “niba kureka nake ba, aiba takura maka nayiba”
Jawwad yace “Baby kinga Jalal, wallahi ba karamin kwarone ba da muna yara, kwakwalwar sa tana kawo wuta, duk lesson din daza’ayi a kansa yake daukewa, gaskiya yau kinciri tuta baby, yanzu dai mu cigaba da tilawar nima ayi dani”
Murmushi Jalila tayi, Jalal yabata mamaki yau sosai, da Jalal yacigaba da karatu da al’umma zasu amfana yanada kwakwalwa sosai, Jalila tace “to kucigaba ni zanyi Alkalanci”

dariya Jalal yayi wadda take masa kyau dan be fiyeyiba yace “Jawwad kai zaka fara, nifa babu haddar ta zube, shekaru Ashirin baya da yin haddar kuma kaga bayi nake ba”
Jawwad yace “hakan ma ka yi kokari fa, amma dan cigaba zan na tuna maka, nayi missing din karatun ka” murmushi Jalal yayi, yafara kokarin dorawa, yana cikinyi ne kawai yafara tari, jikinsa yana rawa, Jawwad yace “lafiya meyafaru Jalal?”
Tari sosai Jalila ta dakko ruwa Jawwad ya karba yana kokarin bashi amma yasa hannu ya make ruwan, ya fadi kasa, nan take idonsa yafara juyewa jijiyoyin kansa dana fuskarsa suka mimmike, nan take fuskarsa tayi murtuk yakoma Jalal dinsa na ainihi dan shaye2 wannan murmushin da Annurin na fuskarsa ya dauke gaba daya, tashi yayi daga kan kujerar dayake yakoma kan doguwar kujera ya kwanta ya rufe idonsa.
Jalila tace
“Yaya Jawwad meyasameshi kuma?”
Ajiyar zuciya yayi yace “Jalila haka yakeyi wani lokacin, ko yana cikin nishadi inka fara masa nasiha gaba daya jikinsa ze hau rawa, ya canza Amma ze ware Insha Allah”
Jinjina kai tayi takarasa aikinta tana mamaki sannan ta fice.
Jawwad yayi mamakin yaushe suka shirya haka har take sashi abu yayi, Amma da ya tuna kokarin da Jalila ke tayi akan Jalal, da kuma Alkawarin data taba yi masa akan zata taya shi addu’a da kokarin ganin Jalal ya shiryu, murmushi yayi yace “lallai baby kinada sa’a mace ta farko daya ji maganar ta tun bayan lalacewarsa”
Jawwad sam ya manta da batun wata Naja, seda Maama ta kirashi a waya, haka ya tashi ransa ba dadi ya dakko key din motarsa ya fito.
Shigar data saba yice yauma tayi, jikin nan duk a matse se wani dan ficicin gyale, ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga gaba daya motar ta bule da kamshin turarenta dayake hawa ka, ya kunna motar yace “Ina zaki?”
“Shopping zaka kaini zan sayi kayan kwalliya”
Bekuma ce mata komaiba ya kunna motar yaja, ya kaita kofar wani store ya ajiyeta, ta kalleshi “to muje mana”
“Ba inda zani, in bazakiba inada abun yi” yafada a hasale
Tsaki tayi ta bude motar ta fita, tana fita ya kashingida ya kira Hanan, seda ta kusa katsewa ta daga cikin muryarta na shagwababbu tace “My Haidar am sorry bana kusada wayarne” murmushi yayi yace
“gaskiya ban hakura ba, seda ta kusa katsewa za’a daga wayar”
“ni gaskiya kayi hakuri ko inyi kuka”
“No don’t cry, Ya kike?”
“Lafiya kalau sedai ina missing dinka”
“Insha Allah zan shigo Kaduna next week zanzo in ganki, na kusa tafiya lagos Daddy ya samo min Aiki a can”
“masha Allah can’t wait to see you my dear, wallahi naji dadi Haidar, Allah ya kawomin kai lafiya, ina yayana kuma sirikina?”
“Wake nan?” ya tambayeta
“Yaya Jalal mana”
“Eh ina sa ran tare zamuzo dashi, Amma yaushe yazama sirikinki?”
“Yacemin yabani kai yazama sirikina, nikuma zan masa tukuici da Jalila dan ita zan bashi shine tukuicin dazan bashi” dariya Jawwad yayi yace
“ba ruwana kunfi kusa keda su”
Sosai ya manta da batun Naja, yaketa murmushi, Kuruciyar Hanan tana birge shi, yanzu duk wata kunya ya ajiyeta, She’s so kind
Har Naja ta dawo motar wayarsa yakeyi da Hanan.
Naja ta fusata matuka a hargitse tace “wannan wane irin rashin mutunci ne? An samana rana Amma kana waya da wata wannan ai wulakanci ne kuma a gabana”
Karaf a kunnen Hanan, Jawwad kashe wayar yayi dan yasan yanzu kome zece Hanan bazata saurareshi ba yanzu, dan taanada matukar kishi, ya kalli Naja yace
“Ke zabin Maama ce” wannan kuma zabina ce, dan haka ki kylaeni”
“ni kake gayawa haka ko? Wallahi zakaga rashin mutunci, kuma ko bakaso seka Aureni, kacigaba da yimin wulakanci, nikuma zancigaba da hadaka da mahaifiyarka”
Bece mata komaiba ya kunna motar yatafi, shi gaba daya hankalinsa da tunanin sa yana kan yaze shawo kan Hanan.
Suna zuwa gida yafita ya barwa Naja motar, daya koma daki ya tarar Jalal ya tashi, yazo ya zauna kusada shi yace “Sannu ka tashi kenan?” Jalal ya jinjina masa kai
Jawwad yace “Jalal dan Allah sati me zuwa, inaso inje kaduna” murmushi Jalal yayi yace “Zakaje gurin Hanan kenan?”
“Eh amma tare zamuje da kai, zaka rakani”
“meyasa sena raka ka?”
“kaima naka zuwan yanada mahimmanci, dan Allah ka rakani”
“to naji, amma senayi shawara”
Jawwad yace “ba wata shawara da zakayi, Akwai damuwa ne?”
Jalal yace “damuwar menen?”
Nan yagayawa Jalal yadda sukayi da Naja, har Hanan taji, Jalal yace “tun farko bekamata ka boye mata halinda ake ciki ba, Amma yanzu ka kira kanwarka ka gayamata, tafara yimata bayani kafin kaje kaduna” Jawwad yace “Hakama za’ayi ka kawo shawara, kai Amma Inajin kunyar Jalila sosai”
“meye kuma Abun jin kunyar? Kirata ni zan gaya mata” ba musu ya kira Jalila a waya yace tazo farfajiya yana kiranta.
Befi 3 minutes ba sega Jalila tazo, Hannunta dauke da wani karamin teddy da kuma wayarta, bakinta kuma dauke da alawa me tsinke, Jalal kura mata ido yayi aransa yake zancen zuci in be manta ba, saura watanni shida Jalila tacika shekaru gome sha tara Amma har yanzu bata dena halin yarinta, kana kallon ffuskarta zaka san yarinyace, sedai Kwakwalwarta ba kowane babbane ze iya lissafin da kwakwalwarta takeba tasamesu akan fararen kujeru a harabar gidan, tayi mamakin ganin Jalal kaman bashine dazu ya canza gaba dayaba.
Taja kujera ta zauna tace “gani Allah yasa ba lefi nayi ba?”
Jalal yace “ke tunda kin saba lefi, duk lokacin da aka kiraki bakya kawo komai a ranki se laefi kikayi, kodayake ke ai aikata laifi a jininki yake”
Bakinta yayi jawur saboda Alawar datake sha, kallonsa tayi ta harareshi ta dan murguda baki tace “Eh tunda kullum ‘yan sanda sesunzo sun tafi daniba, aidole kace laifi a jinina yake”
Yadda bakinta yayi jawur din nan tana juyashi ba karamin birge Jalal yayi ba, Jawwad yayi murmushi yace “Allah yabaku hakuri, dazu gwanin sha’ awa naji dadin yadda naganku, Amma yanzu kuma zakuyi fada”
Jalila cikin shagwaba tace “toba shine yace ina laifi ba”
“to kice ba kyayi mana? Shekarun baya ina seda kikasa Abba zuwa kaduna kin tabo ‘yar gidan masu bullet”
gaba daya sukayi dariya, saboda Jalal da sigar tsokana yayi maganar” gaba daya Jalila mamakin Jalal takeyi, ya iya barkwanci da tsokana, Amma inbaka zauna dashiba bazaka gane hakan ba, kuma abun mamaki lokaci daya seya birkice yakoma Jalal dinsa mashayin giya.
Jawwad yace “Baby wani taimako nakeson kiyimin”
Ta gyara zama takara rungume teddy tace “with due respect, ina jinka babban yaya”
Ya yunkura zeyi magana suka jiyo hayagagar Maama ta nufosu itada Naja,
“saboda ka cimin mutunci kake gayawa Naja wai baka sonta kanada wadda kakeso, Jawwad yaushe kakoma haka? Yaushe kafara bijirewa umarnina? Ya koyamaka ko? Zama da Jalal yasa kafara bijiremin, har kake waya da wannan shedaniyar yarinyar a gabanta, na samaka ido tsakanin ku kar mahaifinka yakawo wani abu aransa amma duk baka ganiba ko? “
Jawwad yace” Maama nifa bahaka mukayi da itaba, kuma ba ruwan Jalila bada ita nake waya ba, na gayamata ita zabinkice, nima inada zabina”
Tas Maama ta dauke shi da mari, gaba daya sukayi tsit dan ba karamin mamaki abun yabasu ba,
Shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai ko tari beyiba, cigaba tayi da zazzga masa masifa Jalila tace
“haba Maama, biyayyar da Yaya Jawwad yake miki in baki gode masa ba bekamata ki zageshi ba, kuma da ze canza hali da ya dade da canzawa dan Allah karki kuma dukansa”
“rufemin baki kasurgumar munafuka kawai, bake kike zigashi ya bijirewa umarnina ba, jarababbiya wallahi zanyi maganinki, kuma baki isa ki hana Auren nan ba, jarababbiyar banza”
“Kuma makira barauniya ba, mara usuli gata barauniya abun kunya itace ke kokarin kusheni wai kar a Aureni, ai garani da dangina uwa da uba, kekuwa fa, dangin uba babu, na uwarma ba wanda yasansu, kodayake ina wani dangi daza’a nuna tunda Arnane” Naja ce take wannan maganar tana jujjuya ido da kebe baki kamar uwatta. Jalila tace
“Naja, nina godewa Allah da yadda ajiyeni, da naso rushe Aurenki lokaci daya zan bata komai wallahi, Maama Niba barauniya bace ba, Ilham bata bani kudinki ba, akira Ilham din gani gata tafada miki lokacin data bani, sannan ni bazan ziga Yaya Jawwad ya bijirewa Umarninki ba, Amma kijawa Naja kunne wallahi takuma zagina, sena ambaci uwatta na zageta, nagaji da abunda kukemin Maama menayi miki, kullum ba damar inyi motsi se anciwa uwata mutunci? “
A fusace Maama ta daga hannu zata mari Jalila, Jalal da tun dazu beyi magana ba yai sauri ya shiga tsakani ya rike Hannun Maama, ya girgiza kai yace
“A’a Maama, Jawwad ma dana san zaki mareshi bazan bari ba, gaskiya Jalila tafadi, uwa batafi uwaba, sannan in baki godewa Jawwad kiyiwa Allah godiya da samun da nagari ba, be kamata ki butulce ba, ya miki biyayya akan abunda bayaso amma baki ganiba, mahaifiyata misali ce a gareki, nikadai ta haifa amma nakasa yimata biyayya, karkiyi kuskuren da Mummy tayi a rayuwarta, kizo kina da nasani, dan Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button