ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Ina yinku ABDUL JALAL group da sauran masoya wannan Novel irin sosai din nan fa ???????????? inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing, gashi nan na muku dogon page, in banga ruwan comments inna shura takalma na posting se rana ita yau ????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
What’s app only 07063065680.
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

             *ABDUL JALAL*

Story and writing
By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girls)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A*✍️


PART 2         
                      _PAGE  3️⃣9️⃣92

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

      _MY FIRST NOVEL _

Jalal nagama magana yasakarwa Maama hannunta, Jawwad kam mamaki da bacin rai ya hanashi magana, Maama bata taba marinsa ba, lokacin yaji yakara tsanar Naja, juyawa Jawwad yayi ya nufi part dinsa zuciyarsa tana suya, da sauri Jalila tabi bayansa ta bar su Agurin a tsaye, Jalal ma bin bayansu yayi, ita kanta Maama jikinta yayi sanyi da marin da tayiwa Jawwad, yadda taga ya sunkuyar da kai ya tafi bece mata komaiba da kuma maganganun da Jalal yayi, Amma ta maze ta cigaba da banbami.

Jawwad na zuwa ya zauna ya dafe kansa yayi shiru yana saka abubuwa daban2 a ransa, da sauri Jalila ta karaso ta zube agabansa tana kuka amma takasa magana se sheshsheka, dagowa Jawwad yayi ya zuba mata ido amma yakasa magana, Jalal ne yakaraso ya tarar dasu a haka, yasamu guri ya zauna a kusada Jawwad, ya kalli Jalila yace

“kidena wannan kukan haka, kikoma gida komai ze wuce Insha Allah”
Shiru tayi tacigaba da kukan a hankali cikin kuka tafara kokarin furta “Am sorry Yaya Jawwad,….”
Maganar ta sarke takasa karasawa, Jawwad yace “Jalila ke yakamata abawa hakuri, tashi kije kidena kuka, nasan abunda kikeji akan yadda akemiki a gidan nan but am really sorry komai ze wuce kinji” gyada masa kai kawai tayi, tace “Yaya Jawwad karka canza lokacin tafiyar nan, kayita tanada mahimmanci”

“zanyi Insha Allah”
yabata amsa jiki a sanyaye, ta mike zata fita ta juyo ta kalli Jalal tace “Ilham! Ilham…. Sekuma tacigaba da kuka ta fice da sauri ta tafi cikin gidan da yanzu takejinsa kamar prison.
Nana batasan me akeba, tana can tana manne da Mahmud a waya, dan haka koda ta fito palour Maama ta tarar tana sababi, ita zuwa yanzu lamarin Maama har tsoro yake bata, kullum cikin fada take, takoma halin ‘yar uwatta na masifa ko gajiya batayi, Nana batabi kan maganar da Maama takeba ta wuce kitchen tadora girki.
Jalila ta shigo palour, Maama na kokarin shiga dakinta se hararta takeyi tana tsaki, sannan ta shige Naja ma wani tsaki tayi tace
“hmm nidake naga wanda ze Nasara, duk wani iyayinki da iya munafurci da kinibibi na kafirai da kuka iya sedai kiyi kigama dan nafi karfinki wallahi kar nake kallonki nafiki iya tashanci, banza ‘yar Arna kawai, wadda uwarta ta yasar ta tafi gararinta”
idon Jalila yayi jawur dan kuka, cikin matukar bacin rai da masifa Jalila tace
“Naji nakuma yadda kinfini iya tashanci, tunda kin tsotsa a Nono mana, nagode Allah har mahaifina ya koma ga mahallicinsa ba’akamashi da ‘yar waniba, naki uban fa? Shekararsa biyar a prison da kyar aka karboshi, tashanci gashi nan ke kinayi yayarki da ďan uwanki nayi, sannan kinfini tashanci nikuma nafiki kai da iya wasa da hankali, ki kiyayi ranar dazan miki tonon silili, kuma Aure ne da yardar Allah baza’ ayi shiba, saboda nagama shirina akanki, lokaci kadan ya rage kifada tarkona”
Nana data fito daga kitchen bata taba jin wannan labarin na mahaifin Su Naja ba, itakuma Naja daskarewa tayi a gurin dan mugun mamakine yakamata, dan ta girmi Jalila kuma tun kafin a haifeta abun yafaru bakowa yasani ba, Amma ita ya akayi tasani.
Jalila tuni ta shige daki, ta nufi bandaki ta dauro Alwala tazo ta hau sallaya tafara gabatar da sallar magariba.

Jalal yanata rarrashin Jawwad
“Jawwad tun asalinka me biyayyane da hakuri ba kamar niba, dan Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalinka, kasan iyayenmu mata daukar ziga baya musu wahala, ka kwantar da hankalinka kayi hakuri”
Wata irin Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace “Jalal Abunda yafaru naji babu dadi, amma abunda yafi batamin rai halinda wannan marainiyar Allah keciki, Jalal hakurin Jalila yakai a yaba mata, duk fitinarta tanada kawaici da hakuri, kuma tanada biyayya, duk abunda Maama take mata bata taba nuna mata bacin ranta ba, akan Jalila nasan Abba ze iya rabuwa da Maama, amma bata taba gayamasa abunda ke faruwa ba, Jalal inajin tausayin yadda rayuwar Jalila ke kasancewa daga wannan se wannan, nasan yau kwana zatayi kuka, kuma Jalal abunda Ilham tayi bata kyauta ba, be kamata tayiwa Jalila hakaba, son zuciya ba halinta bane”
“Nasani Jawwad, komai zezo da sauki zan dau mataki akan hakan, kaji ka kwantar da hankalinka”
“Shikenan Jalal, ka shirya jibi Insha Allah zamuyi tafiyar nan”
“Allah ya kaimu”
Jawwad ya amsa masa da Ameen, Jalal ya tashi ya fito, a harabar gidan yaci karo da teddyn Jalila da sweet dinta a kasa, yasa hannu ya dauka teddyn ya tafi dashi.

Bayan Jalila ta idar da salla, Nana tace “Jalila dan Allah meya faru kikewa Naja wannan maganar? Abun yabani mamaki ni bantaba jiba fa, kodai fushi ne yasaki”?
Jalila idonta Jawur ta kalli Nana tace “Nana duk bacin raina banawa mutum kazafi, kuma bana gori yauma raina ne ya kai makura a baci, sannan ba karya nayiwa mahaifin Naja ba, kuma na fada ne kozan samu sassauci akan bakanta min da ake, kullum aka tashi gori sedai ace uwata Arniya, kawai saboda…… Kasa karasawa tayi, maganar ta sarke saboda kuka
“Am really sorry sister, i feel your pain nasan ba dadi abunda yake faruwa dake amma kiyi hakuri dan Allah”
Wayar Jalila ce tafara ringing Ahmad ne Amma bazata iya dagawa ba ta kashe wayar.

Jalal na zuwa gida ya ajiye teddyn Jalila akan gadonsa ya tafi cikin gida, a palour ya tarar da Mummy amma ya shareta ya nufi dakin Ilham, tana kwance akan gado tana chatting ya fado dakin, zumbur ta mike zaune dan tasan indai taganshi a dakinta toba Arziki, ya kureta da jajayen idonsa yace “Tambayarki zanyi, idan kikamin karya sena shakeki, yaushe kika kaiwa Jalila kudi tabawa Maama?” hade rai tayi
“Na kaimata kudi, nace ta ajiyewa Maama inji Mummy”
“karya kikeyi”
“niba karyanake ba”
“zan tattakaki wallahi, karya kike”
“wayyo Allah mummy, kizo ki temakeni” ganin tana ihu ya harzuka Jalal jikinsa yafara rawa ya janyota daga kan gadon ya zuba mata mari
“Nizaki rainawa hankali? Nizakiyiwa ihu uban me nayi miki?”
Mummy kam a sukwane takaraso dakin
“lafiya meye haka metamaka?”
Banza yayiwa Mummy yace “waike wace irin dabbace ne? Ranar akan idona kike soke kudi a jikinki, naganki da idona amma saboda baki da mutunci kin dorawa yarinya kinsa se kuka take, wace irin zuciya ce dake haka?”
Se yanzu Mummy tagane inda ya dosa dan haka tace “to mara mutunci, dama saboda waccan yarinyar kazo kake wannan zare idon kake kokarin shaketa, kaji kunya wallahi ka fifita wata banza can bare akan ‘yar uwarka”
“Karki kara dangantani da wannan shedaniyar niba’ yar uwata bace ba, tanemi ‘yan uwanta can baniba, kuma kicigaba karki fasa, indai wannan yarinyar ce you know what she’s capable of doing, ba’ a tabata ta hakura, kuma wallahi kika kuma yi mata wani abu makamancin haka sekin bar gidan nan tunda ba gidan ubanki baneba”
Mamakine yakama Mummy suka bude baki suna kallonsa gaba daya,
A fusace Mummy tace “kai ka kiyayeni, akan waccan banzar yarinyar zaka ci zarafin Ilham, kuma har kake nema ka gayamin bakar magana haka? Jalal kanayiwa kanka hisabi kuwa?”
“Karki kara ce mata banza, ga banza nan agabanki” ya nuna Ilham
“tayimin abunda ko raina nabata bazan biyata ba, bashida amfani yimiki wani bayani tunda son zuciyarki kawai kikasani, amma lokaci ze bayyana komai” har ya juya ze fita daga dakin idonsa ya sauka akan Alqur’ani nan a saman rio, zuwa yayi yasa hannu ya dauka ya duba tabbas Alqur’anin ne, Amma me yakawo shi hannun Ilham? Be tsaya tambayarta ba yai waje abunsa.
Yana fita Ilham ta dora hannu aka tace “Nashiga uku mummy, wannan wace irin masiface? Wace irin kiyayya yaya Jalal yakemin haka?” Mummy tace
“kinga dan Allah darene, kidena min ihu, hankalina ya karkata wani gurin, tabbas yaron nan yana sonta, kenan seta juyamin ďa, yadda yake wannan masifa kanta, har yana wannan kumfar bakin akanta ina baze yuwu ba wallahi, ba’a haifi yarinyar dazata juyamin ďa ba, koya fifitata akaina ba”
(su Mummy amanta lokacin da ake juya ďan wata????)
Ilham cikin kuka tace “Wallahi bawani sonta dayake, tana bashi kanta ne kawai, nikuma bazan iyaba shiyasa baya sona se ita dan Allah Mummy kiyi wani abu”.
“ke rufemin bakini, yanzu ba wannan issue dinne agabana ba” ta juya tabar Ilham da sakakken baki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button