ABDUL JALAL PART 2

Koda Abba ya dawo beji motsin yaran nasa ba, dan yasaba yazo yatarar da Nana da Jalila suna kallon ko wani abun a palour, dan haka yake tambayar Maama
“wai ina yaran nan ne? Banga kowa a cikinsu ba, Jawwad har ya rufe kofarsa, sukuma ‘yan matan banga kowacce ba lafiya dai ko?”
Maama tace “lafiya kalau, sun kwanta da wurine kawai” dahaka suka bar zancen.
Washegari da safe yakasance Asabar, Jalila tana baccin dole, dan kwanakin naan bata iya bacci, ga matsanancin ciwon kai saboda kuka, wayartace tafara ringing Hanan ce dan haka ta daga, amma da mamakinta taji Hanan tana kuka, nan da nan hantar cikin Jalila ta kada tace “Hanan lafiya kuwa?”
Cikin kuka Hanan tace “Jalila dama Haidar Aure zeyi kuka boyemin?kuka kyaleni naketa masa wannan makauniyar soyayyar?”
“Haba Hanan, waya gaya miki haka?”
“ya zakice waya gayamin? Jiya muna waya da kunnena naji, muna waya dashi wata tana cewa wai ankusa bikinsu yake waya da wata, Jalila am so disappointed, meyasa kukayumin haka?”
“Hanan bazaki ganeba, yanzu haka cikin rikici muke dagani har Yaya Jawwad”
“Jalila duk rikicin da kuke ciki bekamata kumin haka ba, amma nagode”
Jalila na kokarin yimata bayani amma Hanan ta kashe wayar ta, dafe kai Jalila tayi ta marasa dame zataji, Hanan, Jalal, Jawwad kokuma wannan tashin hankalin.
Jawwad ya gayawa Abba zeje kaduna, Abba be hanashi ba, ya fuskanci Jawwad baya walwala, amma Abba yabarshi a stress ne na shirye shiryen biki da kuma tunanin rabuwa da gida ze tafi wani gurin aiki.
Jalal yakira yagayawa Abdallah cewar zasuzo,
Hanan kam tasha kuka, Abdallah yazo mata da labarin Jawwad zezo, amma sam batayi murna ba, Mummy se rarrashinta take, amma kuka kawai takeyi.
Daddyn Hanan yasan da zuwansu Jawwad dan haka befita ba yana gida.
Shabiyun rana su Jalal suka iso kaduna garin gwamna, sunsami kyakyawar tarba a gurin iyayen Hanan. Har cikin gida Abdallah ya kaisu Jawwad suka gaida Mummy, Abunda ya daurewa Mummy kai be wuce yanayin abubuwan Jawwad sak Yusuf dake bauchi, boye mamakin ta tayi suka gaisa sosai, har cikin ranta ta yaba da hankalin Jawwad, har ranata takw Addu’ar Allah yasa Jawwad ya auri Hanan.
Abdallah yaje dakin Hanan yasameta a daki idon nan jawur ta sha kuka, yace mata “to uwar kishi gashi can yazo, yakamata kije ya ganki tunda danke yazo, amma fa naga shima kaman bashida lafiya ne, naga ya rame sosai”
Da sauri ta mike zaune tace “dan Allah bashida lafiya?”
“hmm magulamaciya, da kikace haushinsa kikeji, keda a rayuwarki ba kya uzuri, inkin ga dama kicigaba da kukan karkije” ya fice yabar mata dakin, bayansa tabi da harara, tayi zamanta taki tashi, seda Mummy ta biyo sahunta taita mata mita sannan ta mike, jallabiya tasaka baka se mayafinta ta tafi palourn da aka sauki su Jawwad.
Kallo daya zakayi mata kasan tasha kuka, tana zuwa tasamu guri ta zauna ta takalli Jalal tace “Yaya Jalal sannu da zuwa ya hanya?”
Murmushi Jalal yayi yace “lafiya kalau Hanan, ga Jawwad din na kawomiki”
Kallon Jawwad tayi kawai tafara kuka, Jalal yace “Ikon Allah, su mata komai nasu na kukane, hakama Jalila takeyi, mikewa yayi yafita yabasu guri.
Jawwad ya tashi daga inda yake yazo gabanta ya zauna ya dan zuba mata ido sannan yace ” dama zaki iya fushi dani haka? Haba My i don’t expect this from you, Hanan bakiga na rame ba, ina cikin damuwa komai yayi min zafi narasa ya zanyi” nan ya kwashe komai ya gaya mata, gaba daya tausayinsa yakamata tace
“Am sorry Haidar kishinka yasani nayi maka haka, dan Allah kayi hakuri, Amma yaya Jawwad bazan iya jure ganin ka Auri wata baniba, Jawwad zan iya hakura ka auri wata ka hadamu amma banda wannan yarinyar”
“Meyasa?”
“sister dinkace, nibazan fadi komai ba, Amma zancigaba dayi mana Addu’a”
Jawwad yaayi ta rarrashinta harta saki jikinta suka fara hira
Koda Jalal yafito Abdallah ya janye shi dakinsa suka dinga hira, bayan sunyi Sallar Azahar, suka tafi part din daddyn su Abdallah.
Daddy ya karbesu da fara’a ya kalli Jawwad yace “barka da zuwa sirikina ashe kuna tafe”
Sunkuyar da kai Jawwad yayi saboda kunya kodan karamcin nan da sukayi masa zenemi alfarmar Abbansa ya barshi ya auri Hanan.
Matsana suka zauna a kujerun dake palourn suka gaisa, ya tsaida idonsa akan Jalal ya lura da yadda bayason magana sosai, sedai in anyi abu ya danyi murmushi
Daddy yadubi Jalal yace “My son, Kaine Jalal kenan?” Jalal yayi mamaki dan yasan daddyn Hanan besanshiba, amma ya akayi yakama sunansa haka? Jalal ya gyada kai yace “eh nine”
Daddy yace “Ai ina ganinka naganeka, ammm nace bakaga tex message da’aka turamaka ba?”
Jalal ya dan dirirce yace “Wane message?”
Daddy yace “Eh akwai hukuma dasuka turomaka message na daukar aiki mana, zakaje screening”
Shiruu Jalal yayi sannan yace “Ammafa daddy nima ina shaye2, tayaya NDLEA zasu daukeni aiki?”
Tausayinsa ne yakama Jawwad yace “haba Jalal aiba a haka, ka amince mana, sun san kanayi suka daukeka ai”
Daddy yace “ABDUL JALAL don’t mind kaji, ai munsan kana shaye2, karka damu you are my son dukda bansanka abaya ba amma yanzu nasamu ďa, dama yaran sunmin kadan, nayi magana da daddynka ma, An riga an baka aikin, ba wani abu ai zaka iya, Jajircewarka akeso sannan kaikuma kayi kokarin denawa, zaka temakawa hukuma, ni yadda naganka din nan with good body structure aida a soja nasaka kaima”
Gaba daya sukayi murmushi tunda daddy cikin sigar zolaya ya karasa maganar banda Jalal daya shiga tunani yayi shiru,
Daddy yakuma cewa “Am sorry munmaka laifi nida diyata ko? Tasani nasa an soke maka visa, tuba muke bamuyi hakan dan bata maka ba”
Murmushi Jalal yayi ya sunkuyar da kai suka cigaba da hira, bayan Azahar suka daura haramar komawa gida, sukayi sallama dasu sannan suka nufo kano, daddyn Hanan duk ya lurada yadda Hanan take nan nan da Jawwad ya yadda ba karamin so takewa Jawwad dinba.
Bayan tafiyar su Mummyn Hanan tace “Daddy ka lurada yaron nan Jawwad kamarsa daya da Yusuf, wallahi hatta murmushinsa irin na Yusuf din Baba sagir ne”
“Na gani nima, Amma kamnin twins girl dina yafi fitowa, tun lokacin dana ganta nakeji ajikina kaman akwai alaka tsakaninmu, Amma ni yanzu abunda yake raina inason tuntubar mahaifinsu, indai Jawwad yana sonta yafito kawai, tunda naga hankalinta yafi karkata gareshi”
Kaman Mummy tayi masa bayanin yakusa Aure, amma tafasa tace “To Allah ya tabattar da alkhairi amma gaskiya ni na yaba da hankalin sa, gashi nutsatse”
Tunda suka taho hanya Jalal yayi shiru yakasa magana, Jawwad ya dubeshi yace
Jalila sosai take rashin lafiya, bata ko cin Abinci zuciyarta a cunkushe bata sha’awar komai, ga wani matsanancin ciwon kai dayake hanata bacci, ko makaranta bata iya zuwa, Nana tayi2 taje Asibiti tace mata ba wani matsala bane damuwa ce kawai take damunta,
Ta yunkura ta mike zata shiga toilet, kawai taji jira gaba daya garin yayi mata baki kirin, aikuwa ta fadi a gurin tana fidda numfashi da kyar, Naja na kan gado tana kallon Jalila tace ” ahaka bakinciki da mugun abunki zasu hadu su kasheki, ki barmu a duniyar nida Jawwad muyi Aure, Allah yasa ki mutu shegiya”
Jalila tanajin Naja amma bazata iya motsa ko dan yatsanta ba Nana data dawo dauke da kofin tea ganin Jalila a kwance yasa ta jefar cup din tazo kanta da sauri tana girgizata, Jalila tasa hannu ta dafe kanta tace “Nana kaina ze fashe”
“Sannu Insha Allah ze dena ina zuwa”
Taje ta dakko youghurt a fridge tazo tana bawa Jalila danta fuskanci hada yunwa ke damun Jalila,
Naja ta kallesu tayi tsaki “Aikin banza wahalallu”