ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Tunda su Jawwad suka nufo kano, Jawwad yakejin faduwar gaba dan besan meze tarar ba dan shi yanzu ko zuwa gidan baya so, shikam Jalal se sakawa yake yana warwarewa, shi meye amfanin yin wani aiki, Jawwad yaji shirun yayi yawa dan haka yace “ya dai naji kayi shiru haka? Ko har yanzu baka yadda da aikinbe?”
Jalal ya danyi tsaki sannan yace “Jawwad nifa kaina yagama daurewa a ina Baban Hanan yasanni da harze bani aiki, kuma yana cewa sungama magana da daddy, yaushe akayi wannan zancen bansaniba? Tayaya zan fara hana wasu sha da fataucin miyagun kwayoyi bayan ni inayi? Ka gayamin tayaya?”
“wannan ba abun damuwa bane bafa, kaiba ruwanka da wani tone2 na meyasa aka baka aiki, kuma ai ansan kana shaye2 akabaka ko?”
Shiru Jalal yayi baya tunanin ze iya wannan aikin, tayaya za’ace me hana laifi yana aikatawa.
Haka suka cigaba da shiru kowannensu yana sakawa yana kwancewa har suka iso kano.

Jalila tunda ta danci Abinci tasha magana tasamu nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Koda su Jalal suka dawo, kowa gidansu ya nufa, Jalal ya tafi gida, shima Jawwad ya tafi gidansu.
Kwana uku da zuwan su Jawwad kano, tunda suka dawo Jawwad baya shiga gidan saboda gudun fitina sam baya wuni a gidan.
Jalal yayiwa teddyn Jalila guri akan gadonsa, yana son yaganta yabata abunta sannan ya tambayeta ya akayi Alqur’ani daya bata yaje hannun Ilham? Har yayi wanka ze kwanta yaji kamar ana hura masa wuta a zuciyarsa da kansa gaba daya jikinsa ya dau zafi a sukwane ya nufi fridge dinsa ya ciki cikinsa da giya sannan yaji daidai.
Da safe Jalal yasamu daddynsa a daki yana bacci dayake saukar dare yayi, ba tunanin komai Jalal ya tasheshi, koda daddy ya tashi Jalal yafara jeramasa tambayoyi
“daddy da saninka aka samomin aiki a hukumar sha da hana fataucin miyagun kwayoyi?” daddy yace
“Dafarko dai ban saniba sedaga baya, General Abdurrashed ya kirani a waya, yacemin ‘yarsa tanemi ya sama maka aiki a wannan hukumar inbazan damuba in turamasa CV dinka, shikenan na amince”
Jalal yayi saroro yana kallon Daddynsa “Wace’ yar tasa?”
“kai zan tambaya ai”
Shiru Jalal yayi, kawai ya mike ya sakko daga kan gadon daddy yafice daga dakin.

Jawwad yana dakinsa, Nana tazo tace masa Abba yana kiransa, haka ya tashi gabansa na faduwa, yana fatan Allah yasa ba wani laifin yayi ba, yana zuwa, ya tarar da ‘yan gidan a palour banda Naja, Abba yayi shirin fita, Abba yace masa “Jeka ka canza kaya, Bauchi zamuje yanzun nan”
Cikin mamaki Jawwad yace “Bauchi kuma Abba?”
“Eh bauchi mana, kayi sauri a yau nakeson mudawo”
Cikin Mamaki Maama tace “Abban Jawwad ni nakasa gane meke faruwa haka, tun jiya kake bacin rai, kaki saurarata yaukuma ba zato ba tsammani kace bauchi zaka tafi, mezakiyi a bauchi ne?”
Kallon ta ya danyi yace “ba dole inki saurararki ba, ki shirya munyi magana da baban Jalal, ranar Lahadi shida ‘yan uwansa zasu kawo kudin Auren mahmud da Nana, sannan zanje bauchi inne mawa ďana Auren’ yar mutunci, sannan karki kuskura in dawo in tarar da yarinyar nan Naja a gidan nan, tabarmin gidana a yau”
“Amma meyasa?”
“in mun dawo kyaji meyasa”
Jalila dake gefe tace “Abba Allah ya kaiku lafiya, ka gaishemin dasu, kuma akwai wani albishir dana boye banyimaka ba sekaje bauchi zaka gani”
Abba yayi murmushi yace “to shikenan Baby, kema inason kafin lokacin bikin Nana ki fidda miji ku karasa karatun a dakinku” Jalila ta sunkuyar da kai tana murmushi, Abba kuma yasa kai yabar palourn.

Mummy tana zaune suna hira daddy a babban palour Jalal yashiga da sallama, suka amsa masa gaba daya, yaje kan Mummy ya tsaya fuskarnan babu alamar walwala ya jefa mata wata jarida a hannunsa yace “ga shi nan yanada kyau ki duba Labari na uku a cikin wannan jaridar, yanada mahimmanci agareki”

Ina yinku ABDUL JALAL group da sauran masoya wannan Novel irin sosai din nan fa ???????????? inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing, gashi nan na muku dogon page, in banga ruwan comments inna shura takalma na posting se rana ita yau ????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????


             *ABDUL JALAL*

Story and writing
By
AISHA HUMAIRA
( Daddy’s girls)

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A*✍️


PART 2         
                      _PAGE  4️⃣0️⃣93

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

      _MY FIRST NOVEL _

Tsayawa Mummy tayi tana kallonsa, yace “ki dauka kiduba mana, kika tsaya kina kallona, ganin da yayi Mummy bata da niyyar taba jaridar yasashi yasa hannu ya bude ya ajiye mata a gabanta,
Hoton Kabir ne da Jeje da wasu mutane da bindigogi agabansu, tittle din ta karanta, da hanzari jikinta na rawa ta dau jaridar tafara dubawa, an yankewa Kabir zaman gidan yari na shekaru goma sha biyar sakamakon saida makamai da fataucin miyagun kwayoyi, sannan an yanke masa shekaru Ashirin a prison saboda Yunkurin kisan kai, da kuma shekaru goma sha hudu sakamakon lalata da kanan yara mata.
Sekuma su Jeje da’aka yankewa hukuncin shekaru ashirin2 a gidan prison.
Daddy ne yasa hannu ya karbi Jaridar shima ya duba, Jalal yace
“Mummy Allah yakawo karshen mutumin da dasa hannunsa a lalacewata, shiyabada kwangilar koyamin shaye2 saboda ya huce takaicin abunda kikayi masa akaina, kalli keda laifi nida karbar hukunci”
Daddy yace
“Jalal kai waya gayamaka shiya bada kwangilar hakan?”
“ba gayamin akai ba, Jeje abokina yaronsa ne, idan nagaya muku wanda yayi sanadiyar kama Jeje da uban gidansa har nasan wannan lamarin kila karyatani zakuyi, sanin hakan bashida Amfani, Mummy yakamata ki zubar da makamanki kikoma ga Allah tun kafin kema ya dankeki, Kabir makiyinane na boye bansan dashiba sedaga baya, nasan makiyana na fili, suma ina nan nasasu a Addu’a very soon Allah ze yimin maganinsu”
Yasa hannu ya dauke Jaridar ya fice.
Daddy yaja ajiyar zuciya yace “Khadija lokuta da dama bana ganin laifin yaron nan, ba wai ina goya nasa bayane ba, amma kinmasa laifuka masu tarin yawa, ba kya duba haka se wanda yakemiki, anyway Ansamosa aikinyi na gwamnati wanda muke saka ran ze dauke masa hankali daga kan shaye2”
Kallon Daddy tayi tace “bangane ansamosa aiki ba, wani irin Aiki? Me Jalal yanema yarasa da zeyi wani aiki, ina kamfaninsa na sarrafa robobi meyasa bazaka bashi abunsa ya rike ba?”
“ba an samomasa aiki ne dan wani abuba, ansamo masa ne dan hakan zesa yayi kokarin dena shaye2, kuma bazan iya cewa wanda yasamo masa din A’a ba, kuma nima naga dacewar hakan”
“wai waye ya samo masa?” ta tambaya cikin kosawa
“General Abdurasheed ne”
Dan zare ido tayi tace “Ina yasanshi daze bashi aiki, sannan wani irin aikine haka? Dan dana baze aikin soja ba”
“Eh ya gayamin Jalila ce tace tanason yasama masa aiki a NDLEA, hakan ze temaka masa wajen dena shaye2”
Hade rai tayi sosai tace
“Baze yuwu ba, baza’a mayar minda ďa bawa ba,
Akan mene? Meye hadinta dashi dazata sa a samo masa aiki, banda cin mutunci tasan yana shaye2 shine zatace yayi aiki a hukumar yaki da shaye2 salon tasaka akama shi, kokuma taji dadin juya shi yadda takeso ko? Dama yanzu na fuskanci maganarta yakeji akanta ba irin wulakancin daba yawa Ilham, to bata isaba da raina babu yarinyar dazata juyamin ďa, baze yuwu in haifi ďa wata ta juyamin shiba”
Mikewa daddy yayi tareda yin murmushi yace “Eyya kin makara khadija, duk abunda kayi se an maka, ki gode Allah da yarinyar ba cutar dashi take ba, dan ta damu da halin dayake cikine hartasa a sama masa aiki, nayi farinciki da hakan, kuma batun kice baza’a juya miki ďa ba daga baya kenan aikin gama ya gama” be jira yaji martanin da zatayi ba ya shige bedroom ya kulle kofarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button