ABDUL JALAL PART 2

Jawwad ko sallama basuyi da Jalal ba suka tafi bauchi shida Abba.
Maama kam a sukwane take tambayar Jalila “me Abba ke nufi, me kika gaya masa haka? Sannan wa zeje nemawa Aure?
“niba abunda nagaya masa, yaushe rabon da in zauna dashi balle ince masa wani abu, nibansan waze nemawa aure ba be gayamin ba”
A fusace Maama takoma dakinta tana tunanin yazata bullowa lamuran.
Jalila takoma daki suka dinga murna itada Nana, Jalila tace “Nana ban taba zaton Abba ze yadda da abunda nagaya masa ba”
Dan bata rai Nana tayi tace “Jalila nayi mamakin abunda ya fusata Abba haka, har yayi fushi yake ikrarin abar masa gida, nayi mamaki sosai be taba hakaba fa”
“to yanayi na rayuwane Nana, tunda kikaga haka akwai abunda ya bata masa raine, sannan akwai dalilin dayasa yayi haka”
Nana ta dan numfasa tace “Jalila nifa damuwata naji Abba yana batun akawo kudin Aurena, Allah yasa ba dana Yaya Jawwad za’a hadamin ba, nan da wata hudu da ‘yan kaifa kenan”
Nana takarasa maganar kaman zatayi kuka
Jalila tace “to meye aciki? Keda rabin rankine fa Mahmud zaku kasance inuwa daya”
“To Jalila karatun fa? Kinsan Mahmud a kasar waje yake nasa karatun tayaya abun ze yuwu?”
“ze yuwu mana, kicigaba da naki karatun a can riba biyu, Allah sarki Rayuwa hajiya Nana za’a zama matan Aure, bari in lissafa yaushe zaki haihu”
Hade rai Nana tayi “Ke Jalila komai sekin sako wasa a cikine? Inamiki maganar serious kinamin wasa, ke yanzu akace za’ayi aurenki nan da watanni hudu kin shiryane? Ni yanzu ma meyasa Abba bece a hada dake ba”
Dariya Jalila tayi tace “gidan Ahmad yana bauchi, shi yana aiki a maiduguri, ni ina karatu a kano tayaya kike zaton inyi Aure yanzu, se nagama tukuna”
Wayar Jalila tafara ringing, ta kalli Nana tace “Excuse me, let me pick the call”
Nana ta daga mata kai, Jalila ta amsa wayar tareda yin sallama
Amsamata yayi sannan ya dora da “Babyna kwana biyu kin gujeni you are not picking my calls, ina fatan ba laifi nayi miki ba?”
Cikin siriyar muryarta na shagwaba tace
“Ohh no ni bakamin laifi ba, bana dan jin dadine kawai, amma yanzu Alhamdilillah naji sauki”
“Ya salam amma baki gayamin ba, yau zan shigo kano dama shiyasa na kiraki, in kin amince zanzo in ganki”
“Babu damuwa my one, ina fatan in ganka nima am missing you”
“Like serious, karkisa inyi Ihu attention din mutane ya dawo kaina”
Murmushi tayi tace “ba sekayi ihuba, aini yakamata inyi, kwana nawa zakayi a kano?”
“zanyi sati daya Insha Allah, zanyi wani assignment ne”
“Shikenan Allah yakawo ka lafiya”
“Ameen my queen, bazaki tambayi Antynki ba?”
Dan yamutsa fuska Jalila tayi tace “Ainasan tana lafiya tunda najika haka”
Murmushi yayi yace “Queen da alama kinada kishi sosai, anyway sena shigo, idan nazo da wuri zaki ganni yau, in ban shigo da wuri ba se Allah ya kaimu gobe”
“to shikenan Allah ya kaimu, take a good care of your self”
“Ok Baby i will Insha Allah” ta katse wayar, Nana ta zuba mata ido tana kallonta, Jalila tace “Madam lafiya kuwa?”
“Lafiya mana, nina kasa gane inda kika dosane, gane lamarinki se Allah mutum baya taba ganeki, gaba daya rayuwarki zigza ce”
Sosai Nana tabawa Jalila dariya tace “rayuwartawa ce zigza, lallai ma Nana bakida dama, Rayuwata normal ce kaman ta kowa”
“A’a ban yadda ba, Allah yasa ayi miki aure kafin ayiwa Yaya Jawwad”
“Ba Ameen ba, back to sender muguwa kawai”
“eh amma ni kikayimin fata saboda son kai”
Wayar Jalila ce takuma daukar ruri, ta kai hannu ta dauka tana dubawa taga Hanan ce dan haka ta kashe wayarta.
Tunda suka fara tafiya Abba beyiwa Jawwad wani gamshashen bayani akan wannan tafiyar ta bazata ba, yanason yayiwa Abba magana amma yakasa duk sunyi shiri Jawwad na driving,
“Dama Aliyu akwai wadda kakeso kaki ka gayamin kabari ake kokarin auramaka wannan yarinyar?”
Tambayar tazowa Jawwad a bazata, kuma idan yaji Abba ya ambaci sunansa na gaskiya kai tsaye haka, alama ce ta he is so much serious.
Jawwad ya dan sosa keya yayi shiru
“yaka sosa kai kayi shiru? Kamin bayani mana”
Cikin kame2 Jawwad yace”Amm.. Dama Abba, ai…”
Abba yacce ” Jawwad da farko sister dinka Jalila tagayamin inyi bincike akan yarinyar nan Naja, tacigaba da gayamin hakan, sannan taki gayamin komai game da Naja, sedai cewa inyi bincike, tacigaba da nunamin cewa kunyarka da kawaicinka baze bari ka nuna abunda ke ranka ba, na dauki maganarta serious nafara kokarin bincike, ina kan binciken ne, Mahaifin Hanan ya kirani yamin magana akan in dai dagaske kana son ‘yarsa yabaka dama ka fito, wanda ni bansan da zancen ba, nayi kokarin in zauna da kai muyi maganar kafin ta kai ga haka Jalal yazo ya sameni har gurin aiki yamin bayani akan alakarka da’ yar gidan general Abdurrasheed, sannan ya daukeni ya kaini inda aka gayamin komai akan Naja, bantaba tunanin Mamanka zata zaba maka mace irin wannan mara kamun kai a matsayin mata ba, Jawwad meyasa baka gayamin abunda ke ranka ba, kabari nakusa gangancin saka rayuwar ka a hatsari? “
“Abba nasam bazaka zabamin abunda ze cutar dani bane, banason bijirewa umarninka dana Maama, shiyasa na amince”
“Nasan da wannan Jawwad, amma dukda haka a matsayin mu na iyaye yanada kyau mudinga baku zabi, ba wai bin son zuciyarmu da tirsasamuku akan abunda bakwa ra’ayiba, yana da kyau kadinga faďan ra’ayinka ba laifi bane naji dadin kokarin yimana biyayya dakayi, Allah yayi maka Albarka yakara haďamin kanku, Allah ya shirya mana ABDUL JALAL dukda kasancewar halinsa amma yadamu da lamuranka sosai, yadda yazo ya sameni kaman zeyi kuka, Alhamdilillah nayi mamaki naga abubuwan sa sun fara raguwa, yafara dawowa hanya, ya rage rashin ji”
“hakane ya rage sosai makuwa, abokiyar fadansa keta kokarin sashi a hanya ai”
“Wa kenan?” Abba ya tambaya
“Jalila mana, tanata kokari akansa, kuma naga inga masa nasiha koba duka ba yana ďan dauka”
Abba yace “masha Allah, at least kaga an samu improvement, itama General Abdurrashed yamin magana, yace akwai abokin ďansa dayake sonta, wai Ahmad sunansa kowaye?, yabiyo ta hannunsa a nema masa Aurenta, amma nace na bashi wuka da nama shima babanta ne, duk abunda yaga dace yayi”
Jawwad yai murmushi yace “hakane Abba, lokacin da mukaje kaduna yamin zancen nima, yace shima mutumin sojane yana da kirki sosai”
“Hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi yamuku zabi da abokan zama nagari” Jawwad a zuciyarsa yace Ameen.
Hanan taita kiran wayar Jalila amma Jalila taki dagawa, saboda bataji dadin abunda Hanan tayi mata ba, sako Hanan ta turimata kamar haka
"Assalamu Alaikum, Am very sorry my twiny, nasan na miki laifi kiyi hakuri dan Allah, Yaya Jawwad yazo kano shida Jalal, yamin bayanin komai abunda ke faruwa, kiyi hakuri so dakuma kishinsane yasa namiki haka, sannan naji Yaya Abdallah yana maganar Ansamawa Jalal aiki za'a gama interview ranar laraba amma har yanzu bejeba, you have to take action"
Jalila nagama karantawa ta kira Hanan, seda Jalila ta kira sau biyu sannan Hanan ta dauka tace
“‘yar rainin hankali inata kiranki kinki ďagawa, amma da kikaji batun ABDUL JALAL harkin kirani”
Jalila ta hade rai kaman Hanan na ganinta tace “ke banason wulakanci, ai banji dadin abunda kikayimim ba sam wallahi”
“Nasani amma ai nace kiyi hakuri, you won’t understand how far my loves go on your brother, inasonshi ina kishinsa shiyasa na shiga damuwa, inata addu’a dai amma ina cikin damuwa Queen”
Tausayin Hanan yakama Jalila tace “ki kwantar da hankalinki kinji my twiny, komai ze wuce kece zaki zama matar Yaya, ina nan ina tayaku da Addu’a”
“Masha Allah, Allah yabiya ki da mafificin Alkhairi Jalila, bazan iya biyan kaunar da kike nunamin ba”
“bakomai Sister na, nace are you serious Jalal beje interview din nan ba?”
“Wallahi dagaske nake miki, hala aikinma kekisa aka samo masa?”
“to meye naki aciki nason kisani, nice nagayawa Daddy ya samo masa, kuma be isa ya watsamin kasa a ido ba zan sameshi, seyaje interview din nan”
Dariya Hanan tayi tace “wai zaki sameshi irin Mum din nan tasa, kai lamarinku din nan yana birgeni wallahi, kowa da guntun taurin kansa dan Allah duk yadda kukayi ki gayamin dan wallahi….
Katse wayarta Jalila tayi jin Hanan zata fara mata bare2.