ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Tunda suka fara tafiya Abba beyiwa Jawwad wani gamshashen bayani akan wannan tafiyar ta bazata ba, yanason yayiwa Abba magana amma yakasa duk sunyi shiri Jawwad na driving,
“Dama Aliyu akwai wadda kakeso kaki ka gayamin kabari ake kokarin auramaka wannan yarinyar?”
Tambayar tazowa Jawwad a bazata, kuma idan yaji Abba ya ambaci sunansa na gaskiya kai tsaye haka, alama ce ta he is so much serious.
Jawwad ya dan sosa keya yayi shiru
“yaka sosa kai kayi shiru? Kamin bayani mana”
Cikin kame2 Jawwad yace”Amm.. Dama Abba, ai…”
Abba yacce ” Jawwad da farko sister dinka Jalila tagayamin inyi bincike akan yarinyar nan Naja, tacigaba da gayamin hakan, sannan taki gayamin komai game da Naja, sedai cewa inyi bincike, tacigaba da nunamin cewa kunyarka da kawaicinka baze bari ka nuna abunda ke ranka ba, na dauki maganarta serious nafara kokarin bincike, ina kan binciken ne, Mahaifin Hanan ya kirani yamin magana akan in dai dagaske kana son ‘yarsa yabaka dama ka fito, wanda ni bansan da zancen ba, nayi kokarin in zauna da kai muyi maganar kafin ta kai ga haka Jalal yazo ya sameni har gurin aiki yamin bayani akan alakarka da’ yar gidan general Abdurrasheed, sannan ya daukeni ya kaini inda aka gayamin komai akan Naja, bantaba tunanin Mamanka zata zaba maka mace irin wannan mara kamun kai a matsayin mata ba, Jawwad meyasa baka gayamin abunda ke ranka ba, kabari nakusa gangancin saka rayuwar ka a hatsari? “
“Abba nasam bazaka zabamin abunda ze cutar dani bane, banason bijirewa umarninka dana Maama, shiyasa na amince”
“Nasan da wannan Jawwad, amma dukda haka a matsayin mu na iyaye yanada kyau mudinga baku zabi, ba wai bin son zuciyarmu da tirsasamuku akan abunda bakwa ra’ayiba, yana da kyau kadinga faďan ra’ayinka ba laifi bane naji dadin kokarin yimana biyayya dakayi, Allah yayi maka Albarka yakara haďamin kanku, Allah ya shirya mana ABDUL JALAL dukda kasancewar halinsa amma yadamu da lamuranka sosai, yadda yazo ya sameni kaman zeyi kuka, Alhamdilillah nayi mamaki naga abubuwan sa sun fara raguwa, yafara dawowa hanya, ya rage rashin ji”

“hakane ya rage sosai makuwa, abokiyar fadansa keta kokarin sashi a hanya ai”
“Wa kenan?” Abba ya tambaya
“Jalila mana, tanata kokari akansa, kuma naga inga masa nasiha koba duka ba yana ďan dauka”
Abba yace “masha Allah, at least kaga an samu improvement, itama General Abdurrashed yamin magana, yace akwai abokin ďansa dayake sonta, wai Ahmad sunansa kowaye?, yabiyo ta hannunsa a nema masa Aurenta, amma nace na bashi wuka da nama shima babanta ne, duk abunda yaga dace yayi”
Jawwad yai murmushi yace “hakane Abba, lokacin da mukaje kaduna yamin zancen nima, yace shima mutumin sojane yana da kirki sosai”
“Hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi yamuku zabi da abokan zama nagari” Jawwad a zuciyarsa yace Ameen.

Hanan taita kiran wayar Jalila amma Jalila taki dagawa, saboda bataji dadin abunda Hanan tayi mata ba, sako Hanan ta turimata kamar haka

"Assalamu Alaikum, Am very sorry my twiny, nasan na miki laifi kiyi hakuri dan Allah, Yaya Jawwad yazo kano shida Jalal, yamin bayanin komai abunda ke faruwa, kiyi hakuri so dakuma kishinsane yasa namiki haka, sannan naji Yaya Abdallah yana maganar Ansamawa Jalal aiki za'a gama interview ranar laraba amma har yanzu bejeba, you have to take action"

Jalila nagama karantawa ta kira Hanan, seda Jalila ta kira sau biyu sannan Hanan ta dauka tace
“‘yar rainin hankali inata kiranki kinki ďagawa, amma da kikaji batun ABDUL JALAL harkin kirani”
Jalila ta hade rai kaman Hanan na ganinta tace “ke banason wulakanci, ai banji dadin abunda kikayimim ba sam wallahi”
“Nasani amma ai nace kiyi hakuri, you won’t understand how far my loves go on your brother, inasonshi ina kishinsa shiyasa na shiga damuwa, inata addu’a dai amma ina cikin damuwa Queen”
Tausayin Hanan yakama Jalila tace “ki kwantar da hankalinki kinji my twiny, komai ze wuce kece zaki zama matar Yaya, ina nan ina tayaku da Addu’a”
“Masha Allah, Allah yabiya ki da mafificin Alkhairi Jalila, bazan iya biyan kaunar da kike nunamin ba”
“bakomai Sister na, nace are you serious Jalal beje interview din nan ba?”
“Wallahi dagaske nake miki, hala aikinma kekisa aka samo masa?”
“to meye naki aciki nason kisani, nice nagayawa Daddy ya samo masa, kuma be isa ya watsamin kasa a ido ba zan sameshi, seyaje interview din nan”
Dariya Hanan tayi tace “wai zaki sameshi irin Mum din nan tasa, kai lamarinku din nan yana birgeni wallahi, kowa da guntun taurin kansa dan Allah duk yadda kukayi ki gayamin dan wallahi….
Katse wayarta Jalila tayi jin Hanan zata fara mata bare2.

Ilham shiryawa tayi takanas ta tafi gidansu, domin taji abunda yakamata suyi, dan ita ta riga ta karaya da lamarin nan bata tunanin akwai nasara dan kullum Jalal kara bauďewa yake, babu alamar ze sakko.
Tayi sa’a ummannata tana gida, suka kule a daki kaman yadda suka saba in Ilham ďin tazo.
“Umma nifa najiki shiru ya’ake cikine? Na ďora mata sata amma Jalal bakiga rashin mutuncin dayayi min ba, wallahi son yarinyar nan yake, kincemin zakije Nijar gurin wani malamin amma shiru kullum abubuwan kara tabarbarewa sukeyi”
Umma tace “ke nayi maganar zuwa nijar, munyi waya da mutumin na masa bayanin komai, amma budar bakinsa wai yayi bincike akan yarinyar indai inason a yimin aiki akanta zan bashi dubu ďari biyar, nikuma ina naganta? Banida ita bani da wata kadara da zan sayar in bashi wannan uban kuďin, dan haka nakoma gurin wanda muke zuwa tun farko, shikuma yacemin baze iya aiki akanta ba sedai a kara watsa rayuwar Jalal”
“to Umma batun Auren namu fa?”
“shima za’ayi ne amma yace muďan kara hakuri”
“umma kenan, mu kara hakuri fa kikace? By mistake idan Asirin ya karye gaba ďaya kuma yaya zamuyi?”
“bazeyiba, malamin yabani wannan tabbacin ki kwantar da hankalinki burinmu seya cika, sena wulakanta shi shida uwarsa hada uban nasa, bana yafiya ga wanda yamin laifi”
“to shikenan Umma, Allah yasa, ni bari in tafi, zan ďan tsaya inyi siyayya”.

Dogon wandone a jikin Jalila da riga, dan haka ta ďakko katon hijjabinta me hannu tasaka ta fito part ďin Jawwad taje tana tsammanin ganin Jalal a can amma baya nan, rabonta da shiga gidansu Jalal kuwa harta manta, direct ta nufi gidansu Jalal, amma tarasa ina zatayi tasan dai be dace ta tafi part dinsa nemansa ba, fasawa tayi ta juyo tanufo gate zata fita itakuma Ilham ta shigo.
Tsayawa sukayi suna kallon kallo itada Ilham, haďe rai sosai Ilham tayi tareda yin tsaki tazo zata gifta gefen Jalila ta wuce, caraf Jalila tasa hannu ta riketa ta janyota gabanta suna fuskantar juna, a fusace Ilham tace “ke dalla malama meye haka? Meyasa bakida tunani ne?”
Jalila taja wasu seconds tana karewa kwayar idon Ilham kallo sannan tace
“banida tunani kam, dole ki fadi haka, kinsan ba’a tabani a zauna lafiya, dan haka sekinyi hakuri da duk abunda zaki gani har se kin biya abunda kikayimin”
Hararta Ilham tayi takuma kokarin rabawa ta wuce ta barta, amma Jalila takuma shan gabanta tace
“Ilham nasani tsawon shekaru ina bata miki rai, kinyi alwashi daban2 akan ganin bayana, baki taba nasara ba se wannan karon da kika ďora min sata, to bari kiji in gayamiki wani abu dabaki saniba, babu abunda zakiyi a rayuwa ki rama abunda nayi miki, na riga nagama dake Ilham, kuma Wallahi Jalal baze taba aurenki ba, nagaya miki dama muddin kudirina yayi karo da naki sena watsa naki, kudirinki akansa yaci karo da nawa na watsa shirinki watsawa ta har gaban abada zanso ingaya miki wani abu daya kamata ki sani amma ban saniba ko kinason ji”
Kallonta kawai Ilham take batareda tayi magana ba, Jalila ta ďora tace
“Ranar da Jalal ya kwanta a Asibiti, kukazo duba shi keda Mahaifiyarki kisani idonsa biyu yaji duk abunda kuke faďa, dan haka ki cirewa ranki cewar burinki ze cika, Na riga naganoki Ilham tuntuni shiyasa nayi miki illa inda ba wanda ze gani, na illata shirinki bakida wata dama data miki saura, damarki ďaya shine ki jajirce kicigaba da jarraba sa’arki kozaku daidaita”
Jalila takarasa maganar tana mata wani mugun kallo sannan ta juya tayi ficewarta, gaban Ilham ne ya shiga dukan hamsin2, kaddai Jalila dagaske take, amma to in hakane da yaji aida yaďauki mataki, “kai karyane bejiba, koma yaji wallahi seya Aureni, se burin mahaifiyata yacika”
Ta shige cikin gida da sauri hada tuntube.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button