ABDUL JALAL PART 2

“Yadda kace haka za’ayi daddy”
Abba yace “General wannan ma ‘yar wajenka ce?, tana kama da Hanan”
“‘ yar wana ce, gaba dayansu yaran ‘yan uwanane, Aini Hanan da Abdallah kadai Allah yabani, sekuma diyata Autar mata Jalila, Zuma kenan ga zaki ga harbi”
Gaba daya sukayi dariya, daddy yace su ci Abinci, Amma gaba daya Jawwad yakasa sakewa yaci Abincin nan saboda kunya “Sekace wani mace????, (ya kuke gani in goga Jalal ne? ???? yaseen cin abunsa zeyi)
“
Daddy yace “Jawwad baka cin Abincin nan fa, nifa banason fulatanci, ka saki jiki kaci Abinci”
Jawwad murmushi kawai yayi yakuma sunkuyar da kai.
Bayan sun kammala, Abba ya gyara zama sannan yace
“to Captain ni dai da farko Jawwad be gayamin yana soyayya da Hanan ba, har nayi masa zabin matar Aure nida mahaifiyarsa, Amma yanzu nagane akwai matsala a dangane da zabin da mukayi masa, kuma Kanwarsa Jalila da Dan uwansa suka sanar dani halin da’ake ciki har kaima ka kirani a waya kazomin da wannan zance na Jawwad ya fito in dagaske yake”
Daddy yace “Hakane, nima mahaifiyar Hanan dince ta sanar dani halin da’ake ciki, kuma gaskiya yarinyar tanada manema dayawa kuma ta nuna shi Jawwad din takeso, shiyasa nima nayi maka magana”
Abba yace “Hakane, Amma zangaya maka wani abu, inkaga zaka bawa Jawwad ‘yarka a haka to shikenan, inkuma kaga baze yuwu ba semu hakura”
Daddy yace “ina jinka fadi muji”
Abba yace “kaga maganar gaskiya a yanzu a bangaren mahaifi Jawwad bashida kowa se Allah sekumani, sedai bangaren mahaifiyarsa, banida wa bani da kani, kani na ďaya shine mahaifin Jalila kuma Allah yayi masa rasuwa tun Jalila nada shekaru biyar, kuma daga ni har mahaifinta babu wanda yasan suwaye dangin iyayenmu sakamakon suma gudun hijira sukayi daga garinsu, in kana ganin zaka iya bashi ‘yarka a haka shikenan “
” Haba Alhaji Usman, Ai Jawwad ko ďan tsintuwa ne babu abunda ze hana in bashi’ yata indai yana sonta, yanada hankali ga nutsuwa da tarbiyya wannan ba abun damuwa bane ba, bari muje ku gaisa da Mahaifiyata semu karasa gidan Yayana, shi ze karbi kudin Auren”
Abba yace “Nagode kwarai da wannan karamcin naka general, Allah yasaka da alkhairi”
Daddy yace “tsakanina da kai babu batun godiya, bari muje”.
Jalila takoma gida ta fara baccin dole saboda azabar zugin da hannunta yakeyi, se kusan la’asar ta tashi, shima hayaniyar Naja ce ta tasheta dayake ita Naja wani lokacin kaman banza haka take bata magana a hankali, ga hauma hauma kamar rainon gabuwa, wannan hargowar ce ta tashi Jalila.
Sannan da alamu har yanzu Maama bata gaya mata sakon Abba na tabar masa gida ba, dan har yanzu tana giginta da rawar kai, Jalila ta tashi tayi sallar la’asar tanemi abun zubawa a cikinta.
Shikuwa Jalal tunda yaje ya sha giyarsa yayi tatul wani nannauyan bacci ne ya kwashe shi be farkaba se magariba, ya shiga yai wanka yai sallolinsa, bayan ya idar ne ya dau wayarsa yakuma kiran Jawwad, wannan karon Jawwad ya dauka Jalal yace “wai dan Allah ina ka shiga ne haka? Tun safe ban ganka ba, na tambayi kanwarka tace bata san inda kake ba”
“Aiba bata nayi ba, kuma ba saceni akayi ba kaganni tareda Abba muna Bauchi”
“Bauchi kuma? Me ka keyi a Bauchi?”
“bazaka gane ba, sena dawo kawai akwai Labari”
Murmushi Jalal yayi, yadda yaji muryar Jawwad yasan yana cikin farinciki, Jalal yace
“To seka dawo din, amma tafiya ba sallama haka?”
“Nima ban san da tafiyar ba, babu shiri Abba yace inzo mutafi”
“to shikenan Allah yadawo daku lafiya”
“Ameen ya Allah” sukayi sallama
Bayan sunyi sallamane Yusuf ya shigo palourn daddy, Sallama yayi suka amsa gaba daya, Yusuf ya kalli Abba ya durkusa ya gaisheshi ya amsa masa cikin sakin fuska, ya juya ya kalli Jawwad ya mika masa hannu suka gaisa.
Daddy yace “Yusuf ga Abban Jalila fa”
Murmushi Yusuf yayi yace “Ai ina shigowa jikina yabani, ina kallonsa naga akwai alakar Jini, wannanne yayanta kenan sirikinmu”
Daddy yace “ya akayi kasani?” Yusuf yace
“Kai daddy yadda yarinyar nan ke fadarsa, ko kunya ba taji ranar inajinta itada Nawwara (matarsa) tanata yabonsa hada yi masa waka, kaf estate din nan ba wanda besan haidar ba ko ince Jawwad”
Gaba daya sukayi dariya, Yusuf yace
“ďan uwa Allah yabaka wuyan ďauka, dan wallahi Autar daddy fitinanniya ce, ga yarinta a cikinta” haka sukaita taba hira Yusuf yajanye Jawwad suka fice zuwa bangaren Inna.
Suka shiga da sallama, kamar kullum tana kan darduma tana lazimi, suka zauna a gefe suna taba hira harta idar, sannan ta juyo ta kallesu dan kura musu ido tayi, Jawwad yace “Sannu Inna”
“Yawwa ďan nan, Yusuf wannan kuma ina ka samoshi, kar in fadi wani abu ace nayi rikici”
Yusuf yace “Inna Yayan Jalila ne”
Murmushin fuskarta ya faďaďa sannan tace “Masha Allah, Nayi farincikin ganinka yarona, Kanwarka me kama da mairota da na dauka itace, ashe ba ita bace ba ina kabaromin me sunan larabawan?”
“Tana lafiya Inna, tace a gaisheki”
“Allah sarki yarinyar kirki me hankali, idan ina basu labarin kanwata se suyita lallabani wai kar in rikice musu da kuka, itakuwa kanwarka zama take muyita hira naita bata labarin wannan kanwartawa”
Yusuf yace
“zaki farako inna, dan Allah kiyi hakuri, kekowa sekin bashi labarin kanwarki, ko labarin tsofaffinki ba kyayi kamar ita, kimsan bakida cikakkiyar lafiya”
Jawwad yace
“A’a kabarta ta fada maybe hakan ze rage mata damuwa, tunda kaji haka akwai kyakyawar alaka a tsakanin su”
Yusuf yace “Ai intana wannan labarin nata daga nana zata fara kuka, kuma in tafada bata iya cin Abinci jininta ya hau sosai”
Sallamar Su daddy ce ta katse musu hirar suka amsa musu Sallamar amma banda inna da ko juyowa takasa yi.
Daddy yakaraso gabanta ya durkusa yace
“Inna ga baban Jalila, kuma sirikinki yazo ya gaisheki ne”
jinjina kai tayi ba tace komai ba, Abba ya zagayo gabanta ya durkusa gaba daya ta zuba masa ido ko kyaftawa batayi, tace
“Imamu ne? Imamu ina Mairona” cikin sanyin jiki Abba yasa hannu yakamo Hannunta ya rike a nashi a hankali ya furta “Innarmu…. Inna Hafsatu, Allah yasa kece, kece wadda Inna take bamu Labari Yayarta”
Fashewa da kuka tayi ta rungume Abba tana fadin
“Alhamdilillah nagaya musu, Amma sunki yarda suna ganin kaman rikici nane kawai, tunda naga yarinyar gurinka nasan tsatson Mairamunace, nasan zuwa yanzu ba lallai tana raye ba, amma ina son inga ahalinta”
Hawaye sharkaf a idon Abba yace
“Na dade ina bulayin neman ki Inna, Allah ya karbesu gaba daya, dasu da tilon ďan uwana, ya mutu yabarmin ‘yarsa Jalila se yarana biyu, ban taba tunanin Allah ze karbi Addu’a ta ba, yau naga dangin iyayenmu”
Gaba daya jikinsu yayi sanyi, kowa seda yayi hawayen tausayi, Abba yasha wuyar bulayi da yawo garuruwa ko Allah zesa yasamu wani nasa ashe suna kusa da juna, alakar yara ta haďa amma basu saniba, Ashe shiyasa kamannin Jalila da Hanan sukayi yawa, hatta yanayin halayensu iri daya.
Abba yasa hannu yana gogewa Inna hawaye cikin zolaya yace “Kamanki daya da Innarmu, sedai duk babanmu yafi ku kyau”
Murmushi tayi tace “Ai shima ďan uwana ne, kuma mairo tafishi kyau, Allah yayi musu rahama gaba ďaya.
Nan hirar asali da tushe ya barke, nan da nan Labari ya karaďe estate din nan cewar ansamo dangin mairo kanwar Inna, nan da nan gidan yafara cika da dangi da ‘yan uwa don ganewa idanunsu hakikatul Amri.
Daddy yace tunda hakane kadasu Abba sukoma yau, su ďanyi musu ko kwana ďayane Inna taji ďaďi kuma sannan suga’ yan uwa.
Haka kuwa akayi, Abba yakira Maama yace bazasu dawo a yauba saboda wasu dalilai, ba wanda suka gayawa abunda yafaru, hatta Daddy be gayawa su Hanan ba.