ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Ta fuskanci haushi yaji, amma ta basar dan itama ranta a bace yake Befi 5 mintues ba ya dawo da leda a hannunsa, ya kunna motar suka cigaba da tafiya, yana tuki tana goge hawaye, sekace kurame, baya son ya kalleta yaga tana kukan nan, kukanta yanasa shi tuna lokacin da Umminta ka gudn abunda ze sashi kuka shida Jawwad, gani Jalila tayi ya canza hanya dan haka da sauri tace “A’a yanaga ka canza hanya?”
Be kalleta ba yace “Wani guri zaki rakani”
Zare ido tayi “saboda me makaranta fa zani, zanyi test”
“Nasan makaranta zaki, amma tunda kika shigo motata sekinje, don’t mind club zamuje kawai, zan danyi caji”
(???????? tab ba ruwana, yan ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP, kunji Jalal dinku da rigima,)

Abba sunga “yan uwa sunga dangi, Abba be taba tunanin suna da wannan dangin ba, a hakanma sunada ‘yan uwa a wasu garuruwan, A yau Abba yace lallai zasu koma kano saboda yanada ayyuka dayawa, se sun dawo ziyara ta musamman dan kara sanin juna, ba karamin farinciki akayi ba ganin Inna ta samu zuri’ar Kanwar ta, Ashe ba a banza ba Jalila da Hanan suke wannan kamannin.
A ranar su Abba suka dawo gida, tun Asuba suka taho, basu baro bauchi ba seda aka yanke watanni hudu, a matsayin lokacin Auren Jawwad da Hanan, sedasu Abba sukayi maganar Ahmad, Abba yace duk abunda daddy ya yanke dai2 ne, daddy yace “se Jalila ta kammala Makaranta ze bawa Ahmad, saboda yanayin karatunta dakuma aikin Ahmad
Su Abba se karfe shadaya suka sauka a kano, Suka sauka da matukar farinciki.
Abba na shiga cikin gida yaci karo da Naja, a palour tana waya, bece mata komaiba ya wuce part dinsa,
Maama haushinsa takeji akan yace Naja tabar masa gida dan haka tana jin sun dawo taki zuwa inda yake, ya shiga part dinsa yai wanka ya canza kaya, da kansa yaje ya sami Maama a daki Yace
“kina jin mun dawo amma kikasa fitowa kiga yamuka dawo? Shikenan ina miki Albishir Anbawa Jawwad Auren ‘yar wajen Captain Abdurrasheed wato Hanan nan da wata hudu Insha Allah”
Wani mugun kallo tayiwa Abba tace “kamar yaya? Yaza’ ayi akaiwa Naja kudin Aure dan munafunci kuma aje akaiwa wata, mata biyu ze Aura kenan, Jawwad din kwaya nawa yake daze auri mata biyu?”
“mace ďaya ze Aura wato Hanan, maganar Naja na soketa an barmusu kudin Auren, zanje da kaina in samu iyayenta, Sannan kije ki sallami yarinyar nan tabarmin gida, tun kafin raina ya baci, bana kaunarta a cikin iyalina, kema yakamata kuje ku kara binkice akanta”
“Impossible” Maama ta fada da karfi

Masoya kaunar da nake kumu tasa nai muku dogon page gashi nan, senaji Comments dinku love you all
????????????????❤️❤️❤️????????????????

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

              *ABDUL JALAL*

         _Story, writing and edited _

                        By
              AISHA HUMAIRA
              ( _Daddy's girl_) 

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

        PART 2         
                      _PAGE  4️⃣2️⃣95

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

         _MY FIRST NOVEL _

Cikide fusata Maama ke fadin “ni zakayiwa haka? Ka watsamin kasa a ido, a kai kudin Auren yarinyar mugama gayawa duniya za’ayi biki sannan kazo min da wata maganar banza, wallahi baze yuwu ba Jawwad bashida matar data wuce Naja
Abba yace
“Shikenan tunda ke zaki daura masa auren ai seki aura masa Najar in gani”
Ya juya ze fice tace
“Kuma wallahi bazata bar gidan nan ba, in dai Naja zata bar gidan nan to Jalila ma seta bar gidan nan”

Cak Abba ya tsaya ya juyo yace
“gida nawane, duk wanda yake ciki a karkashin ikona yake, idan yarinyar nan ta kai magariba a gidan nan to Wallahi zaku tafi tarene, ta tattara tabarmin gida nagaya miki, Jalila nan gidansune, nine mahaifin Jalila, Jalila bata da uwa ba uba seni, ita kuma wannan tanada iyaye dan haka ta koma gidansu, kowa ya zauna a gidansu” yana gama fadin haka ya juya ya fice.

Jawwad yana zuwa ya canza kaya, ya nufi gidansu Jalal amma yatarar baya nan, dan haka ya koma gida ya samu guri ya kwanta dan ya huta

A fusace Jalila tace
“Wallahi bazani club ba, ka tsaya in sauka in yaso kaje inda yafi club be dameni ba”
Shiru yamata ya cigaba da tukinsa, yana satar kallon yadda ta rintse ido tana masifa, ganin yaki kulata yasa a fusace tace
“Magana fa nake maka, wai meye haka?”
Fitooo yafara yi mata yana murmushi, Jalila ta kai karshe a kuluwa, ya dan kalleta yace
“meye kuma na tashin hankali bafa cewa nayi zamuje Kisha giya ba rakiya kawai zakiyi insha mutafi”
Ta fuskanci so yake ya raina mata hankali, dan haka tayi shiru taga gudun ruwansa, ta dauke kanta zuwa ga kallon window tana share kwalla lokaci zuwa lokaci gani tayi tafiyar taki karewa dan haka takara fashewa da kuka me sauti Da sauri Jalal yace “Ke meye haka kuma? Nifa ba Jawwad bane da zakimin shagwaba”

Ido duk hawaye tace “Eh aida Yaya Jawwad ne yasan inada test bazemin haka ba, kuma Allah ya kiyaye in maka shagwaba in maka shagwaba ince nayiwa wa?” tai maganar tana harararsa da kumburarrun idanunta
Dan hade rai yayi yacigaba da tukin ba tareda yace komai ba itakuma tana hawaye.
Wata unguwa suka shiga, wadda kome za’ayiwa Jalila bata san inane ba, wani katon dogon gini ya nufa, kana ganin yanayin ginin da girmansa kasan kamfani ne, yana zuwa aka bude masa wani katon nannauyan gate ya shiga da motar, tundaga bakin gate din ma’aikatan ke durkusawa suna gaisheshi, dagani gurin kamfanine, yaje yasamu guri yayi parking, da sauri akazo aka bude masa motar ya fito, ya zagaya yace mata
“fito”
“ni bazan fito ba, kawai ka maidani inda ka dakkoni”
“Wallahi in baki fito ba zakiyi biyu babu, kirasa test dinki kuma inki zuwa interview”
Kara hade rai tayi sosai ta bude motar ta fito tana zumbura baki, fuskarta tayi jawur, yayi gaba ta bishi abaya.
Babban abunda ya daurewa Jalila kai be wuce yadda taga duk inda Jalal ya ratsa ma’aikata manya da kanana suna girmama shiba, dan wasu har kasa suke zubewa suna gaida shi, Akayi sa’a in suka gaisheshi yana daga musu Hannu, Haka Jalal ya dinga ratsawa da ita tsakanin ginin katafaren gurin daya kayatu yadda yakamata, ko ina tsaf dashi, suna zuwa wata kofa sukaga wani mutum, ya girmi Jalal sosai ya mika masa hannu sukayi musabiha, mutumin yace “Yallabai yau akwai ruwa da kankara kaine a kamfani yau, rabonka da nan shekara nawa?”
Murmushi Jalal yayi yace “Ya aikin?”
“Lafiya kalau anata fama”
Jalal yace “Masha Allah hakan yayi kyau”
Daga nan yai gaba Jalila tacigaba da binsa, wata katafariyar kofa sukazo Jalal yasa hannu a aljihunsa ya dakko key yabude kofar ya kalli Jalila yace “Bismillah” tareda yi mata nuni da cikin gurin, jiki a sanyaye kuma a matukar tsorace ta shiga ta tsaya a bakin kofar tana rarraba ido, Office ne dankarere, sekace na hamshakin sarki ko gwamna, babu abunda babu a ciki, idonta ne ya sauka akan hotunan dake cikin Office din, akwai hoton shugaban kasa, gwamna da na sarki, sekuma hoton Daddyn Jalal, ta juya daya bangaren tangamemen hoton Jalal ne da Jawwad sanye da kaya iri daya sunyi murmushi an rubuta J&J global concept, sekuma hoton Jalal shikadai, ba karamin kyau yayi a hoton ba Ganin da Jalal yayi a tsorace take ta takure a tsaye, ya maida kofar ya rufe yasa mata key, kallonsa Jalila ta tsaya ta nayi a matukar tsorace hankali yace “muje ko?”
“ni ba inda zani, ka maidani makaranta zan tafi fa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button