ABDUL JALAL PART 2

Baya kaunar wannan gaddamar ta Jalila dan haka be tsaya bata lokaci ba ya danko hannunta da karfi, hakan yasa ta saki wani uban ihu saboda zafi, hannun dayake mata ciwo ya rike, a tsorace ya cikata yana kallon yada tuni ta rike hannu tana Hawaye
“Meye haka? Sekace wadda nayiwa wani abu” ya fada adan gigice
“eh dole kace haka mana, jiya ba kai ka hankadeni na fadi akan hannun ba, yana min ciwo shine ka famamin” Jalila gaba dayanta shagwababbiya ce
Dan shiru yayi yana kokarin tuna abunda ya faru shi gaba daya ya dauka a mafarki abun ya faru ba gaske ba yace “Ok naji amma yanzu zauna”
Guri ta samu akan kujera daya ta zauna, yace “zan iya ganin hannun?”
“Bazaka gani ba” ta fada tareda janye hannunta
“Shikenan tunda kimce bazan ganiba, am sorry, ban san nayi miki ba, a tunanina mafarki ne, idan kinga na shiga wannnan yanayin kidena zuwa inda nake, kome zanyi karkiyi kokarin hanani, in bahakaba wataran zan iyayi miki illa”
Dan kallonsa tayi tace
“to meyasa kake hakan?”
“Nima ban saniba, haka kurum nake tsintar kaina a wannan yanayin, Jawwad ne kawai ya damu da halin da nake shiga, Mummy da ba damuwa tayi daniba, tana ganin kawai shaye2 danake ne ya janyo min hakan, dayawa idan nayi kokarin dena shaye2, kokuma raina ya baci, se in shiga wannan yanayin “
yayi maganar cike da damuwa, cikin tausayawa tace
” Ka dinga yawaita Azkar, kuma ka kulada ibada zaka dena jin abun insha Allah”
“bazan iya ba” ya fada kai tsaye
“Meyasa bazaka iyaba?”
“Har yanzu baki gama sanin waye ABDUL JALAL ba dukda yanzu kinsan abubuwa da yawa akaina fiye da iyayena, just keep praying for ABDUL JALAL, and I really appreciate your efforts on me, Thank you, Allah ya jikan Abee”
Jinjina kai tayi amma takasa magana,
Can tace “dan Allah me nayiwa Mummy? Na gaisheta dazu da kyar ta amsamim tace inje tana son ganina, Allah yasa ba laifi nayi mata ba?”
“meyasa kike tunanin laifi kikayi mata?”
Hawayene ya zubo daga idonta, shi Jalal har mamaki take bashi, kaman shan ruwa haka take kwararar da Hawaye, basa mata wuya sam tace
“Yanzu duk lokacin dana motsa ko nayi wani abu se ansamu wanda zasuce na musu laifi, kowa ya tsaneni komai nayi laifine, mutane kalilan ne suke sona A duniyar nan, daga masu kirana munafuka, se makira, barauniya, karuwa, Arniya se masu cewa uwata ta gudu ta banni, ba ataba barina inyi awa24 cikin farinciki se an samu me batamin rai”
Takarasa maganar cikin kuka muryarta na sarkewa, tasa hannunta biyu ta rufe fuskarta tana kuka me tsuma zuciya, Jalal jin kukan nata yake a kahon zuciyarsa, yaji gaba daya komai ya kwance masa, yace
” Kidena kuka mana, kin manta ke kikemin nasiha amma yanzu kike kuka, Allah baya mantawa da bawansa, Allah yasan halinda kike ciki, ni da nake gabanki a yanzu na isheki misali na isheki darasi, ba’a nasara ba tareda an sha wahala ba, kisawa ranki matakin nasarar kine kike takawa, duk wanda yayi miki gori a rayuwa ko ya cutar dake kisa a ranki kinfi shine, Allah yana son bayinsa masu hakuri, semene dan duniya batayi dake in har ubangijin da yayiki yanayi dake shikenan, kiran da Mummy tayi miki karki sake kije, bashida wani amfani na gaya miki”
Ya mike ya nufi wata katuwar drower ya bude, ya duba ya debo wasu takaddu yazo gabanta ya zube su yace “dauki wannan takaddun, ki dubamin abunda za’a iya nema a gurin, zanyi breakfast yanzu”
Yakoma kan kujera daya yazauna ya fara cin Abincin sa daya siya dazu, Jalila tasa Hannu tana duba takaddun, duk na makarantun da Jalal yayine, abun mamaki results dinsa sunnuna shi din kwarone, kuma duk an masa kyakykyawan yabo a jikin results din, daga ido tayi tana kallonsa yana cin Abincin sa hankali kwance, ba ita yake kalloba amma taji yace
“Ya dai kike kallona? Ko zakici ne?” girgiza masa kai tayi alamar A’a, tareda maida hankalinta kan Takaddun gabanta
Yace “Au Ashefa bazaki iya cin Abincin hannun dan iska ba, karkije na zuba kwaya a ciki ko?”
Shiru tayi masa yagama ciye ciyensa, ya mike yana kuma duba wasu takaddun, yaji muryar Jalila tace
“wai Inane nan?”
“Kamfanina ne?” ya bata amsa
Zare ido tayi, ya kalleta yace
“kina mamakine? Nawane mallakina, akan wannan dukiyar ne aka halakar da rayuwata, dukiya mugun abu me halakar da mutane, me haddasa gaba da kiyayya, me tafiya da Imanin ma’abota kwadayinta, Akan dukiya Mummy tayi cin amana tayi yaudara ta auri daddy,
Akan dukiya Mummy ta ajiyeni tayi tafiyarta lokacin da nake bukatar taimakon ta,
Akan dukiyar akabada kwangilar ruguza rayuwata, Akan dukiya Mummy ta rabu da mutane dayawa, Akan dukiya da daukar fansa aka halakar da rayuwata,
Ilham da mahifiyarta suna son su dauki fansa akaina ne su gaje dukiyar dana mallaka, itakuma Mummy takasa fahimta, tunda suka kyalla ido sukaga Daddy yasayi kamfanin nan yabani, suka kasa nutsuwa, ke sheda ce, Kinsha kama Ilham na kokarin samin magani a Abinci, kuma ta dade tanayi min hakan saboda dukiya, Akan dukiya…….
Sekuma yayi shiru ya dafe teburin gabansa yayi shiru, gaba daya Jalila ta zuba masa ido, jin yadda yake sarrafa magana daki daki ta sigar rarrashi da wa’azi, ko a mafarki in wani ya gaya mata Jalal ze haka karyatawa zatayi.
Yacigaba da cewa “Ban taba kukan babu a rayuwata ba, babu innemi abu in rasa ban taba ba, bansan talauci ba, Amma nidai wannan dukiyar da taza memin bala’i, gara ace talaka futik Mummy ta aura in tsira da mutuncina, A rayuwa bazan manta da mutanen dasuka soni dan Allah ba, family dinku mutane ne masu mahimmanci a rayuwata, kinga Jawwad na yadda in rasa duk abunda na mallaka saboda shi, Yana sona badan dukiya ta ba, duk abunda zamuyi baya sako lissafin dukiya ta, bayan Umminki da Jawwad ban taba zaton zan samu wanda ze tsaya akan lamarina ya damu dani kamar ki ba, bana manta Alkhairi, kinmin abunda banida abun biyanki, dukda bakida kunya, ga taurin kai da tsaurin ido, ga rashin kunya da iyayi, bazan manta yadda kike putting rayuwarki a risk saboda dan iska mara tarbiyya me kama da ‘yan daba, dan daba yana godiya” ya karashe maganar yana kashe mata ido,
Murguda masa baki tayi ta dauke kai, ya danyi murmushi yace “Ai bazaki taba canza hali ba”
Ya kwashi takaddunsa ya mayar da sauran yace mata “Tashi mu tafi” ta mike tayi gaba yazo ya bude kofar suka tafi, sosai Jalal ya dingayiwa ma’aikatan nan barin kudi kaman besan ciwonsu ba.
Suna cikin tafiya Jalila tace “Amma meyasa baka zama a kamfanin, at least you will keep yourself busy zaka manta da wasu abubuwan” dan shiru yayi sannan yace
“Ta yaya ina cikin wannan halin zanzo inyi aiki, Akwai manager kamfanin nan dan abokin daddy ne shike kulada komai, duk lokacin danazo na zauna da sunan zanyi Aiki se wannan abun yasa meni, idan na birkice senayi barna sosai kafin in bar gurin, wani lokacin har illa nake wa wasu, shiyasa wasu ke kallon ko inada tabun hankali, kokuma illar shaye2 ne, rabona da gurin nan nafi shekaru goma, yanzun ma saboda takaddun nan nazo, kuma abun mamaki naga nashiga na fita lafiya yau saboda muna tare da ke”
“To Allah ya baka lafiya, Amma yakamata kanemi magani sannan ka dinga Addu’a”
Tasa hannu ta cire farin carbin counter dake hannunta ta ajiye masa tace “ka dinga Amfani dashi, ze temaka maka” Be iya cewa komai ba se kallon ta da yakeyi, har Jalila manta data bashi sekuma taji yace
“Thank you” itama banza tayi dashi taki kulashi.
Haka suka cigaba da dan taba hira har sukazo makarantar, zata bude tafita yace “tsaya, wai ke wannan ce jakar makarantar?”
“Eh mana” ta bashi amsa
“wannan ba jaka bace sekace Jakar tara kudin bara, ina litattafan karatun?”
“Jakar tara kudin maulace bata bara ba” Ji yayi kaman ya tuntsire da dariya amma ya fasa, yasa hannu ya dau Jakar ya bude jotter ce se biro da kudinta dari biyar se waya, yasa hannu a Aljihunsa ya dakko kudi yasamata ya mika mata, ta kalleshi “Ni inada kudi cire abunka”
“Fitarmin daga Mota ko insa lock inyi gaba dake wallahi” Hannu tasa tana kokarin cire kudin ta ajiye masa yace
“Bana kyauta amayarmin, karki bari raina ya baci fita ki barmin mota, mara kunya”
Ikon Allah yanzu suka taho girma girma cikin mutunci amma se wani korarta yake kaman rokarsa tayi, ta hade rai ta bude motar sannan tace masa “Allah yabada sa’a”
“Ameen” ta rufe masa motarsa tayi gaba.