ABDUL JALAL PART 2

Maama fa hankalin ta ya kai makurar tashi, idan tace zata tsananta maganar nan zata iya rasa Aurenta, dan haka ta nufi part din Abba dan ganin ta inda Zata bullowa Al’amarin, Amma ta tarar yayi ficewarsa, takoma daki tanata nazari, daga baya ta yanke shawarar gayawa Naja halin da’ake ciki, takira Naja dakinta ta sanarda ita abunda ake ciki, Amma bata gaya mata batun Abba yace tabar masa gidansa ba Aikuwa take Naja tafara ruwan bala’i “Harni za’a ciwa mutunci dan tsabar wulakanci da cin fuska, Akaimin kudin Aure in fara shiri sannan ace anfasa saboda tsabar rashin ilimi, wannan ai halin banzane da Jahilci” Maama na kokarin yiwa Naja bayani amma taki saurararta tayi ficewarta, taje ta kira Yaya mairo a waya tana kuka gaya mata, ai tun daga wayar Yaya mairo tafara surfa zagi ta inda ta shiga bata nan take fita ba ta cewa Naja gata nan zuwa gidan.
Jalila test kawai tayi ta dawo gida, dan har yanzu bata jin karfin jikinta sosai tanata nazari akan Jalal, mutumin daya mallaki wannan dukiyar mezeyi da wannan Aikin? Amma akwai ayar tambaya game da Al’amuran nasa, wani lokacin har mamaki yake bata in yana abun Arziki kaman bashi ba, kuma babban abun mamakin dukda yadda Jalal yake wasa da ibasa, yake shaye2 hakan besa dukiyarsa rashin habaka ba, haka taketa tunani harta koma gida,
Amma abun takaicin tana zuwa gida ta tarar da wannan rigimar da akeyi, Hakan ya tabattar mata dasu Jawwad sun dawo, muryar Yaya mairo data jiyone yasa gabanta faduwa, dan sam bata kaunar matar nan, Jalila tana ta Addu’a ta shiga palourn, ta tarar Naja tanata kuka, yayarta sa’ada tana rarrashin ta, Maama tayi zugum Yaya mairo tana sirfa mata bala’i, Jalila tayi sallama ta maze zata wuce, Gaba daya suka dawo kanta da zagi da cin mutunci da tsinuwa, ai kawai tayi kamar kujeru ne kawai a palourn ba mutane ba, ta shige daki ta canza kaya abunta, tayi tunani a ranta muddin tacigaba da zama a yanzu, zasu cigaba da zaginta ne itakuma bazata hakura ba, dan ba shiru zatayi musu ba mussaman in aka hada da cin mutuncin iyayenta, dan data san abunda zatazo ta tarar kenan da bata dawo gidan yanzu ba, ta mike tasa hijjabinta, takuma zuwa ta ratsasu a palour tayi ficewarta tana jinsu suna ita ta haddasa komai ita tayi munafunci batabi takansu ba takara gaba. Tana fita motar Abba ta shigo layin dan haka tayi murmushi aranta tace “yau gidanmu akwai drama” ta tsaya tana jiran karasowar Abba, ya karaso kofar gidan yayi parking cikin fara’a tace
“Abba saukar yaushe?”
Shima cikin fara’a yace “Ai tun karfe goma muka dawo, na dan fitane nayi wani uzuri”
“Masha Allah, sannunku da Hanya, amma tunda na dawo ko Yaya Jawwad ban ganiba”
“Ina zaki ganshi dama? Yana can farinciki ne ya hanashi fitowa Jeki aiken da’akayi miki ki dawo Akwai albishir masu yawa, babyn Ummi”
Cikin murmushi tace “to shikenan bari inyi sauri in dawo” tafada cike da zakuwa, Abba ya shiga gida, se yanzu tafara tunanin ina zata? Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Mummy taji laifin da tayi mata, dukda Jalal ya gargadeta akan yin hakan.
Tana shiga gidansu Jalal ta tarar da motarsa, abun ba karamin mamaki yabata ba, Anya kuwa yaje interview din? Ta tambayi kanta, taga moyar Mummy dasuka fita dazu alamar sun dawo, haka tayita wasi2 harta shiga cikin gidan, palourn ba kowa tayi sallama amma shiru tasamu guri ta zauna akan kujera, wata yarinya da take musu aiki tacewa dan Allah tayiwa Mummy magana, seda Jalila tayi kusan mintuna goma shabiyar sannan taga Mummy ta fito, da fara’a Jalila tace
“Mummy ina wuni?” Mummy tace
“rike ina wuninki, na baya da kikayi ma sun isa, Allah ya amfana” nan take Jalila ta sha jinin jikinta, Mummy tasamu guri ta zauna ta dubi Jalila a wulakance tace
“Dama na kiraki naki dan inyi miki kashedi akan ďana, sannan in soke haramtacciyar alakar da take tsakanin ku” cikin rashin fahimta Jalila tace “Mummy haramtacciyar Alaka kuma?”
“Eh haramtacciya mana, ko ta halatta ne? Tunda yake jin maganar ki fiye da tawa ai dole akwai abunda ke tsakanin ku, da kike masa Ilham ma sheda ce”
Nan Mummy ta ware ta kwalawa Ilham kira, Ilham ta fito tana ganin Jalila ta ya mutsa fuska kaman me shirin yin amai dan taga kashi, Ilham tazo ta zauna tace “Mummy gani”
Mummy ta nuna Jalila tace “gata nan nace Akwai haramtacciyar alaka tsakanin ta da Jalal amma ta karyatani”
“Mummy ai kinsan ba mutunci ne da ita ba tunda bata san darajar manya ba, tarbiyya ta mata karanci”
Mummy ta gyara zama tace “Ina bukatar duk wata alaka dake tsakanin ki Da Jalal tazo karshe a yau, kiyi nisa da dana, ba ruwanki dashi kome ze aikata, ai ba fina sonshi kikayi ba, a palourn nan agabana kinsha kiransa mara tarbiyya, lattace, kuma dan rashin kunya seki lallaba kina kokarin kara lalata min shi bayan abaya duk fitinarsa ba Ruwansa da mata, Amma kina kokarin kizama se abunda kikeso shi zeyi ni uwarsa ban isa dashi ba seke?” Jalila shiru tayi ta sunkuyar da kai ko tari kasa yi tayi
Ilham tace
” Wallahi Mummy na sha ganinsu suna rungume juna, kuma har part dinsa take zuwa dakin sa, in karya nayi ki karyatani mana munafuka, Kuma…… Setayi shiru takasa karasawa, sakamakon saka idonta da tayi a na Jalal dayake tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa, ba Ilham ba hatta Mummy seda ta tsorata, cikin is da Izza yace “Kuma me? Karasa mana”
Zazzaro ido Ilham tafara yi, jin muryar sa yasa Jalila daga idonta sukayi ido hudu takuma sunkuyar da kai.
Yakara so cikin palourn ya kalli Mummy sannan ya maida idonsa kan Ilham yace
“ki karasa maganar ki ina jinki, ke dan baki da kunya har kin manta ke abunda kika dinga yimin abaya ko danni bana zuwa ina fada, wato kin manta lokacin da kike kawomin kanki har part dina in dare yayi ko?” zare ido Ilham tayi tafara kokawa da numfashi, bata taba tsammanin ze iya fadar hakan ya tona mata asiri ba
Ya kakkafe Ilham da, ido yace
“koba ayi bane?” kasa magana tayi se wani gumi data dinga jinsa yana ratsa cinyoyinta, ya maida idonsa ga Mummy yace
“Kinji kunya, ‘yar cikinki cefa, yarinyar data dingayi miki biyayyar dani da kika haifa ban miki ba, ita kikewa wannan bakaken maganganun, meye da ďannaki da za’ a dinga, binsa, niba hankali ba niba tarbiyya ba, sedai abini ko asoni dan dukiya ta amma bani da abunda mace kamar Jalila zata bini sedai irinsu Ilham dabasu san ciwon kansu ba” gaba daya suka zubo masa ido, da sauri Jalila ta mike tayi hanyar fita, jin yana kokarin janyo mata bakin jini tana fita ya rufa mata baya,
Ilham tace “Wallahi Mummy Jalal karya yakemin, ni ban taba kai masa kaina ba, Mummy dan Allah kisa baki ya Aureni, wallahi Asiri tayi masa”
“ke dalla rabu dani niba wannan ne ya dameni ba, kina gani yake gaya min magana akanta, ashe har an samu uwar data haifi wadda zata mallakemin da, ya gayamin magana akanta? Baze yuwu ba wallahi, se na dau mataki akansa da ita kanta”
Ilham ma mikewa tayi tabi bayan Su Jalal dan ganewa idonta meze faru, ayita ta kare a yau.
Har suka fito harabar gidan yana kiranta taki tsayawa, seda yasa hannu ya fizgota sannan ta tsaya
“Jalila meye haka? Ina miki magana kina jina kinki tsayawa, uban me yakawo ki bance karki zoba dama?”
Cikin kuka tace “Dan Allah malam kadena min shouting, meye Amfanin abunda kayi? Zaka sa mahaifiyarka da kanwarka su kara tsanata, Mahaifiyarka tace batason ganina tareda kai, ko a hanya karka kara nuna ka sanni, bani ba kai, kayiwa mahaifiyarka biyayya kanemi Aljannarka, dama ba wani abune tsakaninmu ba mutunci ne da girmamawa tunda bata so shikenan “
Gaba daya idon Jalal yayi Ja, a hankali yace
“kince kowa yaje yayi rayuwarsa ko? Kinfison in kara komawa cikin harkar shaye2 kenan kaman yadda nake abaya? Ke Garkuwa ce a taredani me kike tunani idan kika barni, sanadiyar kasancewar ki tare dani yasa ina kara kokarin yaki da shaye2 da nake abaya, kina tunanin inkika min haka kin min adalci? “
” Kayi Rayuwarka inyi tawa, yafi adinga min kallon mazinaciya, zancigaba dayi maka Addu’a a duk inda kake, Amma bani ba kai ko a hanya balle a cigaba da zargina”