ABDUL JALAL PART 2

Share please
More Comments…………
????️ ????️ ????️ ????️ ????️ ????️
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART 2
PAGE 6️⃣/59
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
_MY FIRST NOVEL _
Abun takaicin, ya kwanta da bacin ran Jalila, zuciyarsa har wani tafasa take dan bacin rai, amma abun takaicin yauma kwana yayi yana mafarkin Jalila, cike da shaukin soyayya da kauna, a yanayi irin na ma’aurata, mafarkinsa na karshene me ban tsoro, ya firgita kwarai ganinshi yayi wasu mutane sun daureshi akan dutse, maza da mata suna saransa da wasu dogayen wukake, Jalila ta bullo daga wani guri ta taho da sauri ta rungumeshi, tana tare masa saran, yayinda sukuma mutanen suka dinga saranta jikinta yana zubar da jini, ta rungumeshi gam itakuma jini na zuba a jikinta a hankali take kiran sunansa a cikin kunnensa ABDUL JALAL. Juyi ya dingayi yana kokarin ya tashi, A firgice ya tashi daga baccin dayakeyi, yana haki, a hankali ya daga kai ya kalli agogo karfe takwas da rabi na safe, tashi yayi zaune yai shiruu yana nazarin mafarkin dayayi na karshe, jujjuya abun ya dingayi a ransa yana tuno yadda take furta sunansa, tunani yake meye alakarsa da wannan mutanen haka suke saransa, dan gutun tsaki yayi, “komeyema na bata lokacina akan wannan shirmen mafarkin” mikewa yayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet don yayi brush yai alwala kawai ya tuna se yayi wanka, sannan zeyi salla wani dogon tsaki yayi “Jarababbiyar yarinya ta addabawa rayuwata, tazomin a farke ta dameni, dan jaraba har cikin baccina ma seta biyoni, ji yanzu ga rana tayi amma senayi wanka zan salla komeye hakan oho” haka yaita mita yai wanka yafito yai sallar asuba.
Bayan ya idar da sallar ya tafi cikin gida, kai tsaye part din daddy ya nufa, ya tarar daddy ya tashi har yana breakfast Shida Mummy suna hira, sallama Jalal yayi, daddy yadago yana kallonsa yafara murmushi, Jalal yaje kusa dashi ya zauna, cikin girmamawa yace ” good morning daddy” ba Mummy ba har Daddy seda ya kalli Jalal, rabon da ya gaida daddy haka da safe cikin girmamawa tun kafin ya lalace dan sedai daddy ya gaida Jalal amma badai ya gaisheshi ba, dama Mummy ba a maganarta itadama baya ta tata, amma abun mamaki yau hada sallama, daddy ya fadada murmushinsa yana shafa kan Jalal yace “Morning yarona katashi lafiya?” “Lafiya kalau daddy, ya gajiyar ka?” “Ba gajiya Jalal, kayi breakfast ne? Ko Jawwad din kake jira?” “No daddy Jawwad nasan ya tafi makaranta” “taho muci nawa to” girgigiza kai Jalal yayi, “kaci Abincin ka daddy, ni zanci nawa daga baya, dama zuwa nayi in gaisheka, sannan in kalleka inajin dadi, kasan na dade ban ganka ba nayi kewarka daddy”
Mummy tace “Hmm wannan soyayya haka, lallai Jalal” daddy yai murmushi yace “to ya ranki, nima kllonka yana sani farinciki yarona, idan na kalleka ina jin daďi, wannan gudan jini nane, babbar kyauta daga Allah, ina alfahari da godewa Allah dayabani kai” dan shiru Jalal yayi cike da damuwa yace “daddy yanzu har farinciki kake da kasancewata danka, kalleni fa daddy kalli rayuwar danake yi, mutane dayawa na kyamar halayena, yayinda wasu suke gudun a dangantani dasu a matsayin danginsu saboda munin halayyata, mutane kalilan ke kaunata suke son farincikina daddy kai da Jawwad bansan wani irin so kukeminba, kai mahaifina ne amma Jawwad da rana ďaya be taba kyamata ba”
“Jalal ko a yaya kake kai Allah yabani, kaine nawa ko halinka yafi haka muni inamaka fatan shiriya, amma ni a haka nake sonka, sannan lamarinka da Jawwad soyayyace daga Allah wanda samunta a wannan zamanin abune me wahala, shiyasa nake maka fatan samun mace tagari, Jalal ba abunda yafi zama da wanda yake kaunarka daďi”
“hakane daddy, Jawwad na musamman ne, naso a ce ciki daya muka fito dashi, amma daddy dagaske bana sauke nauyin dayake kaina a matsayin danka ko? Yadda nake treating dinka bahaka ya dace ďa nagari yayiwa mahaifinsa bako? Kayi hakuri daddy zan dena Insha Allah”
“waya gaya maka haka kai yaron kirkine, kana kokarin farantamin karka damu lokacine wataran se Labari, Allah ya shirya min kai” “Ameen daddy”
“Jalal ta mahifinka kawai kake, a tunaninka shikadai yake da hakki akanka, ni ko oho ko, da inyi farinciki dakar inyi baka damu bako?” hade rai Jalal yayi, yaiwa Mummy wani kallo me cike da ma’anoni, ya tashi ya fita ya bar dakin gaba daya, daddy ya dan dubeta ” Hadiza sam bahaka yakamata ki dinga treating Jalal ba, ko kina manta kece me laifi a gurinsa, yakamata kiyi tunanin hakan. “haba daddy Jalal, shikenan shi abu baze wuceba a gurinsa, kullum da laifina zetamin hukunci” “hadiza ke kike ganin laifinki karamine, banga laifin Jalal ba lokacin danake jan hankalinki, baki saurareniba se yanzu data kwabe miki, seki nemi daidaito da ďanki”.
Jalila tana tafe akan varander na class dinsu ta ga captain dinsu da takaddu a hannunsa, yanata sauri da alama class zeje, wanda tayi Imanin takaddun hannunsa tests dinsu ne, sauri takara ta hada da dan gudu ta tana kiran sa, tsayawa yayi ya waigo, mamakine ya kamashi yaukumashi wannan yar kwalisar takewa magana ya tsaya suka gaisa da ita “Captain wannan tests dinmune ko?” “Eh sune, me yafaru” “yawwa dan Allah alfarma nake nema, sonake kabani tawa anan” “amma meyasa?” “bakomai kawai inason kabani tawa anan ne, banaso sekaje aji” yadda ta kafeshi da ido yaga tayi masa kwarjini matuka dan haka yace “to shikenan ya sunan naki, se in duba miki” “A a bani in duba tawa da kaina, karka damu ba ta wanda zan duba tawa kawai zan dauka” ba musu ya mika mata takaddun an faďi test din nan sosai, kuma gashi over 40 ce duk an faďi tunda test din be fadi zeyita ba, Jalila tana ganin tata ta zare, tana kokarin mika masa takaddun taga wani suna Samira Kabir Idris, Tunawa tayi Kabir Idris shine sunan dake dauke ajikin katin da baban faruk yabata a banki, mika masa takaddun tayi tace” Thank you very much “
” You are welcome ” tunani ta dingayi waye me irin wannan sunan a ajinsu, maybe ma kawai sunane yazo ďaya, da sauri ta tafi class taje gurinta ta zauna, Captain yana raba takaddu tanajin ya ambaci sunan Samira Kabir Idris, ta juya dan ganin kowace, wadda tai tsammanice Samira kawar saleema, se yanzu taga tsananin kamaninta da Alhaji Kabiru, kenan ‘yarsa ce, ajiyar zuciya Jalila tayi, barewa bata gudu danta yayi rarrafe, ba a banza ba Allah yabashi irin wannan yar, Alhamdilillah bincikena zezo da sauki, sena gane alakarsa da Jeje, tana cikin tunanine taji captain yana cewa
“Yan class kunga munyi test, ga a yadda tazo dan haka se mudage a exams, sannan muyita addu’a dan banga wanda ya ci talatin bama, amma yace yanason ganin Jalila Aliyu Imam, in taji tasan kanta taje yana neman ta, danni ban santaba” zahra ta kalli Jalila,” bake ake nema ba? “
“nice”
“Naga ba abaki naki test dinba, ni dai kinga wai 19 na samu” “kigode Allah ai kinyi kokari, yawwa zahra dan Allah samira sunawane yan gidansu” “Su biyune kawai yayanta faruk, sekuma ita sukenan” “Kuma a gidansu ansan me takeyi? “
“Gaskiya bansaniba babansu dai yana da zafi, wataran yana kawota makaranta, mamansuce dai ance ba ruwanta da tsanani akan tarbiyya”
“Mene sana’ar babansu?” “Kai Jalila sekace wata lawyer wannan tambayoyi haka” “yi hakuri akwai abunda nakeson ganewa ne” “gaskiya ban saniba, amma naji kaman ance dan kasuwa ne” “shikenan nagode sosai”.
Bayan antashi daga school Jalila tai tafiyarta gida bataje kiran sir hafiz ba, tanata tunanin yazata bullowa lamarin Alhaji Kabiru, dan tana zargin mutumin nan sam bata yadda dashiba, wayarta ta dakko ta duba what’s app dinta, taga lambarsa tayi appearing a contact dinta na wats app, dan bayan dawowarta gida ranar tasaka lambarsa a wayarta hotonsa ne akan dp dinsa tayi sa’a yana online, dan haka tayi masa sallama, seconds kadan ya amsamata, suka gaisa yace mata be gane me maganaba, rasa me zatace tayi, kawai ta kashe datarta ta ajiye wayar tai shiru tana tunanin anya haka yakamata tayi, ko kawance zata kulla da samira, amma in tayi haka itama za adingayimata kallon ‘yar iska, lambar hanan ta kira amma taki shiga dan haka ta hakura.
Hanan kam tana kwance, tana trying lambar Jawwad amma a kashe, ta ajiye wayar ta dafe kanta, turo kofar dakinta, dan dago kai tayi da mamakinta setaga Siyama, zumbur Hanan ta mike tana murmushi “oyoyo Siyama matar Yaya yauke kika kawomin ziyara” murmushi Siyama tayi “yau nina kawomiki tunda kin mance dani nace bari inyi surprising dinki” “amma naji dadi” Siyama ta zauna, Hanan taje ta kawomata ruwa da lemo da snacks suka zauna sunata hira, Hanan ta kalleta “ta Yaya Abdallah gaskiya Siyama, kin rike wuyan yayana over, komai ke ni ya manta dani gayamin meye sirrine” “haba Hanan waceni rike wuyan Yaya, shiya rike nawa wuyan, wallahi Hanan Abdallah ya iya soyayya shiyake tabarani, bana tunanin akwai namijin daya kai yaya Abdallah iya soyayya da kula da mace” dariya sukayi gaba daya “Siyama ya bakyacin snacks dinne?” “A a ni snacks be dameniba dama chocolate ne” “Ahh sekace queen J, kinsan inkinaso ki birgeta kibata chocolate, gaskiya ina missing Jalila ina kaunarta har cikin raina, amma alakarmu na shirin samun matsala wanda hakan bazemin daďi ba, amma nakasa samun mafita, dama kobakizoba ina son zuwa siyama” hanan ta karasa maganar cikin damuwa,
“Amma Hanan bangane mekike nufiba, kamarya alakarku na shirin samun matsala kamar yaya?”
“Siyama Jawwad nakeso, da farko na dau abun wasa, inayine domin Jalila ta maida hankali akan Jalal, saboda sunfi dacewa amma yanzu nagane wallahi son gaskiya nake masa kota ina yaya Jawwad ya hadu” zare ido Siyama tayi “Hanan kin san irin soyayyar datakewa Jawwad kuwa?” “Siyama soyayyar dake tsakanin Jawwad da Jalila na yan uwantaka ne, amma da Jalal ta dace shike bukatar taimakonta, ina kaunar Jalila amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba” Hanan ta riko hannun Siyama, idonta taf hawaye tace “Siyama babu wasa a zancena, wallahi dagaske nake inason Aliyu Jawwad, so na gaskiya, sannan ina kaunar Jalila ina jinta kaman wani tsagi na rayuwata, amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba” Ajiyar zuciya Siyama tayi, ta gogewa Hanan hawaye “For now kiyi hakuri ki dan bani lokaci, zanyi tunanin mene mafita, amma kidena kuka” gyada kai Hanan tayi kaman karamar yarinya, daga nan suka shiga wata hirar