ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Seda aka kwana biyu, Jalila bataje kiran sir hafiz ba, captain ne yazo yana kuma shela a aji, danshi besan wace me sunan ba, tashi tayi ta fita tatafi offers dinsa, tana zuwa ta shiga da sallama ta tarar da shi da wasu lecturers a office din ammasu dattawane ba kamanshi matashiba, amsamata sallamar sukayi, kaman yadda yake ďabi’ar Jalila har kasa ta zube cikin girmamawa ta gaishesu, suka amsamata cikin mutunci, shi sir hafiz mamaki ma ta bashi, ya kalleta a fusace “uban mekikazo yimin office, kin fadiko? Ba abunda zanyi miki aidama seda nagaya miki fita kibani guri, dakikiya kawai kisawa ranki kin gama faduwa exams dina” batace komai ba ta juya tai tafiyarta
Malaman nan suka dinga jinjina tarbiyyarta, saboda a wannan zamanin a yan matan jami a asamu me durkusawa har kasa ta gaida malamai abunda wuyar samu “hmm bakusan halinta bane, tsabar iya makircine dakikiyace gata fitsararriya, nayi test ta faďi shine takamo hanya tazo”.
Bayan kwana ďaya sir hafiz yakuma sawa a kira Jalila Aliyu Imam, tareda kashedin in batazoba zesakamata zero a test dinsa, kuma zuwa office dinsa Jalila tayi, yau wasu yan matane a ciki se iyayi suke suna yauki, gani tayi bashida niyyar saurarta dan haka tazo gaban tebur dinsa tace “Sir tunda baka da lokacina karka kara turawa kace inzo, zuwana nawa office din nan kaki saurarata, bayan kaikace inzo” daga kai yayi ya kalleta, yayinda yan matan suka bita da kallo “ni nace kizo? Kizo in miki me” “bakai kace inzoba karka kara tura captain yana shelar wacece Jalila Aliyu Imam dan bazan kuma zuwa ba, kaitasamin zeron inka ga dama kasamin abscent se wani wulakanci kakemin menayi maka hakane? , in akwai abunda be kai zeroba kasamin” da sauri ya kalleta “What kece Jalilan?” zumbura baki tayi “Eh nice” “karya kikeyi” ba tace komai ba ID card dinta ta dakko ta diremasa a gabansa, dauka yayi ya karanta ya kalleta tabbas itace
“Ya akayi kikacinye test dina gaba daya alhalin wani abunma banmuku ba, kaf ajinku ba wanda yaci ko 30,ko satar amsa kikayi? Kallon yan matan dake office din tayi tai ta kalleshi tace
” Sir Hafiz , Never Judge book according to it’s cover, bana satar amsa kuma bantabayiba, kana muzantani agaban yan aji kana cemin dakikiya, abun ba anan takeba, kayi alkalanci, idan baka yadda da wannan test dinba ka canzamin wata, amma karkayi tunanin zaka tambayeni a gaban yan aji in baka amsa” shiru ya danyi, ya kalleta yafarayi mata tambayoyi, a nutse take bashi amsa, gashi ta iya turanci matuka, ga mamakinsa har abunda be koya musuba inya tambayeta seta bashi idea dinta, ajiyar zuciya yayi “shikenan zaki iya tafiya zan nemeki” Jalila ta juya ta fita. Sir Hafiz ya dade yana mamakin kwakwalwarta, gata gentle, amma meyasa tsarin rayuwar ta daban da saura ko maganarta ma daki daki kuma a tsare, kuma ba ruwanta maganar kozatiwa wanda ta fadawa dadi ko a a seta fada kuma ko a gaban waye. haka yaita mamakinta.
Yau weekends dan haka tun sassafe Jalila taketa gyaran wardrobe dinta, tagama tsaf seta ga qura’nin da daddyn Jalal ya taba bata, ta jujjuya qura’nin yana nan kar dashi a cover dinsa “Yakamata in dinga tilawa da qura’nin nan, Allah ya bawa daddyn Jalal ladan” tagama gyaran drower dinta, ta tafi kitchen, wainar masa suka tsiriyi itada halima, a matsayin abincin rana, seda suka gama Jalila taje tai wanka ta dawo ďaki ta zauna tana kwalliya wayarta tafara ringing, tana dubawa taga bakuwar lamba ce, bata san wayeba dan haka ta saka wayar a silent.
Tunda daddy yazo garin nan Ilham take kasa kunne taji, anyi batun aurensu da Jalal amma shiru yau kwanan daddy uku da dawowa amma bataji Mummy tace komai ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa tasamu Mummy, dakin Mummy taje bata nan, dan haka ta tafi kitchen, aikuwa Mummy na can tana hadawa daddy fruit salad
“Mummy sannu da aiki”
“Yawwa daughter, kin tashi daga baccin ne?” “ina wani Bacci Mummy alhalin duk ina cikin zullumi da damuwa” “akan mefa?” “Mummy maganata da Jalal mana, har yanzu naga Daddy ya dawo amma bakice komai ba fa”
“Ilham kenan akwai gajen hakuri, ina nan zan gayamasa insha Allah kafin yakoma za asa ranar aurenku” Murmushi Ilham tayi “Allah yasa Mummy, dan na kagu inganni na mallaki yayana” “hmm daughter ba kunya ko” Ilham ta dan rufe ido tana dariya.
Jalila tagama kwalliyarta tasaka turare, ta mike taje ta dauki Abincin Jawwad ta nufi part dinsa dashi, tana zuwa ta tarar bakowa a palour, ta ajiye abincin tasamu guri a palourn ta zauna, tana jiransa koyana wanka ne, ta dora kafa ďaya kan ďaya tana danna wayarta, hankalinta yana kan wayar sosai, tana game tanayi tana murmushi, warin sigari taji ya daki hancinta, da sauri ta ďaga kanta, tai tozali da Jalal ne ya fito daga bedroom din Jawwad, kallo ďaya tayi masa ta ďauke kanta taji tsigar jikinta ta tashi, dagashi se gajeren wando, kana ganinsa kasan yana cin karfe, a murďe jikinsa yake, ga ko ina na jikinsa lullube yake da gashi, fatarsa se sheki take, babu alamun wahala a tareda shi, ya nufo inda Jalila gadan2 zazzare ido Jalila tayi, kirjinta ya shiga dukan uku2 tanaso tayi magana amma takasa.

More Comments
More Typing…………………

????️ ????️ ????️ ????️ ????️ ????️ ????️

Koda yaushe bazan manta da gudunmuwarku ba ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ???? ???? ???? inajin dadin comments dinku, sauran masoya wanda nasani da wanda bansaniba ina godiya
If you want Join the what’s app group via this link ????????????????????
@https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Or contact me via my number, i mentioned at the above page
If you are not reading the novel please don’t join.
[09/04, 12:29 PM] Ayshercool: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _ABDUL JALAL (2020)_

   _Story and written by_
  AISHA HUMAIRA (daddy's girl) 

PART 2
PAGE7️⃣ 60

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

          _MY FIRST NOVEL _

Jalila da kyar take fizgo numfashi, nufota yacigaba dayi, yana zuwa seya wuceta yatafi gurin Tv yanata shan tabarsa, yaje yasaka wayarsa a caji, Jalila kuwa se binsa take da kallo, yagama sa cajin ya taso yakuma dawowa harya wuceta ya dawo ya zauna a gabanta ya kura mata ido, dauke nata idon tayi, “naga kina son kallona ne shiyasa na zauna kigama karemin kallo” ya busamata hayakin sigari a fuskarta, da sauri ta dago tareda toshe hanci, ta dan fara tari, “wai meye haka, Allah ya sawwake inzauna ina kallonka, kato da kai kazomana gida tube sekace dakinka” “dakin Jawwad dakina ne, dan haka ko tsirara naga dama zanyi yawo” yunkurawa tayi zata mike, ya maida ita kan kujerar ya kafeta da ido, yasa kafarsa daya a gefenta, ta kalli inda yasa kafarsa aranta tace kalli jikinsa duk gashi kaman wani dan biri, lighter ya jefomata yasa wata sigari a bakinsa, yaimata alama ta kunna masa, wani mugun kallo tayi masa ta dauke kanta “Allah ya kiyaye ya rufamin asiri, nikabani hanya in wuce, kalleka dan Allah” hannunta daya yakama cikin mugunta ya murde mata yatsu, ihu tayi saboda zafi, take tafara zufa cikin tsawa yace “Kunnamin ko tarihi ya maimaita kansa, inkuma duramiki sigari yanzun nan” jiki na bari ta kunna lighter ta mika hannunta ta kunna masa, “dan Allah ka sakarmin hannuna, yatsuna zasu cire” a hankali yasakar mata hannu, idonta har yayi ja, yacigaba da busa mata hayaki, gashi ya tareta da kafa bazata iya guduwa ba, hannu ta kai zata toshe hancinta, “wallahi kika toshe hancinki sena wanka miki mari, sena baki mamaki da hannunki zaki shata” bashiri ta ajiye hannunta yana busa mata hayaki, se tari takeyi tana dauke numfashi “gaskiya Jalal dan iskane bashida mutunci, yanzu inna matsa da rashin kunya ze iyayimin akuya” seda ya shanye tabarsa tsaf sannan yadubeta “nine Namiji mara daraja ko? Ni Jalal nikike zagi ko?” shiru tayi tana kallonsa, daka mata tsawa yayi “ba dake nake ba kike wani kallona mara kunya” cikin dakewa tace “karya nayi, aiba kadyanayi ba namiji me daraja baze abunda kake ba” “hakane Amma kin bar kari tun ran tubani, kinyi sake namiji mara daraja yamiki Illa, wadda bazaki ganetaba a yanzu, idonki kawai ya nuna a tsorace kike kar in miki wani abu, ba abunda zan miki a yanzu, amma kisani bana yafiya, bana mantuwa, sena hukunta ki akan cin mutuncin dakikemin bazan kyaleki ba, sena gwada miki abunda nakeji idan kika ci zarafina, kidena shishshigi akan abunda baki saniba” Yayi ajiyar zuciya “tashi ki tafi kibani guri kuma kar inkuma ganinki a part din Jawwad dai 2 wannan lokacin, dan kinsan baya nan inkuma kika kuma zuwa to nasan abunda kikazo gani”
Sumi2 ta tashi, taje bakin kofa ta tsaya ta kalleshi “to me zanzo gani, kaikanada abun kallone jiki duk gashi ba kyan gani sekace jikin biri, kokuma wannan jijiyoyin zanzo kallo, jiki kamar dan wrestling aikai ko kyan gani baka dashi, kasa wannan katon hannunka ka matsemin yatsuna Allah yasakamin dan ban yafeba kuma duk barazanar ka bazan dena fadan gaskiya ba, sannan kayi kadan kayimin Illa ko a yanzu ko a gaba, mugu kawai “tai ficewarta, Jalal kam yana jinta tana banbaminta ko dago kansa beba balle ya kalleta.
Ta wuce cikin gida tana yarfa hannu saboda zafi, tana zuwa daki taga Nana ta shirya da alama fita zatayi
” Ya dai naganki kin hade rai, me akayi miki ne? ” Jalila ta yamutsa fuska “Bakomai” “Shikenan dama kenake jira kizo ki rakani gidan, Yaya mairo, tace tana son ganina”
“Tab amma badani Jalilan bako?”
“Kamar yaya?” “kamar yadda nagaya miki mana, haka kurum ketace tana son gani baniba, dan haka ba inda zani, banje gidanta ba ma cimin mutunci take, inaga innaje mata gida, kitafi kawai, ba inda zani” “Shikenan tunda bazakiba, dama banason tafiya nikadai ne” “sauka lafiya ki gaishesu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button