ABDUL JALAL PART 2

Jalila tana kitchen tana aiki Nana ta sameta
“sannu da aiki Jalila, har tausayi kike bani, ke ba kya gajiya da aiki, da ke zaki rigani Aure ai ban san ya zanyi da aikin gidan nan ba, dan ma su Yaya Jawwad basa nan, aikinsu sam baya karewa”
Jalila tai murmushi tace “Nana uwar son jiki, keda zakiyi Aure ai son jiki banaki bane, madam get ready to face the challenge, Ba sauki a Aure”
“Nasani amma gaskiya bazan iya yadda kikeyi din nan ba, tabdijan shikenan kai bawa baka da hutu”
“Aikuwa mukayi miki aure kikaje kikayi shirme, in yace ze kar Aure Addu’a zamu taya shi, mu fidda anko mu sha biki”
“Kan bala’i ji muguwa, to ta Allah bataki ba”
“Kai Nana sarkin kishi”
“ke ba dole inyi kishin sa ba, ke har mamaki kike bani, ainaga kokarin ki da zaki auri Ahmad din nan, inajinki Hanan tana gaya miki matarsa bata da kirki”
Jalila ta murmusa tace
“Nana kenan, macen da ta amsa Sunanta mace, wadda ta yadda da kanta bata batawa kanta lokaci akan wani kishi, duk rashin kirkin matarsa ai ba akanta zan zauna ba, zan maida hankalina ne akan mijina, zanyi kishine da matar da nasan ta fini Ilimi, kyau, dukiya da asali, se matar data hada wannan abubuwan lokaci daya itace watakila zan kalleta a matsayin kishiya”
jinjina kai Nana tayi tace
“Sannu Jalila, Aini ko Kaza za’a aajiye ace kishiya ta ce to hankalina baze kwanta ba, yaushe zan kashe kaina, ke masu irin wannan zuciyar taki bau da yawa”
A tare sukayi dariya, Sannan Nana tace
“Yawwa Jalila nikam nace ya akayi kika amso qur’anin nan daga hannun Ilham? Na ganshi a karamin drwower”
Dan murmushi Jalila tayi tace “Nawane ai ba nata ba, dan haka tunda ya tafi dole ya dawo”
“Amma dagaske yaya Jalal ne ya baki shi? Kamar yadda Ilham ta fada?”
“watakila shi yabani dan bani da tabbas” Jalila ta fada ba tareda ta kalli Nana ba
“Kamar Yaya baki da tabbas?” Nana ta tambayeta cike da mamaki
Jalila ta juya ta cigaba da aikinta sannan tace
“Kamar yadda nagaya miki mana, bani da tabbas na shi yabani koba shi bane ba”
Nana tace “Kai Jalila kin fiye rainin hankali, mutum yayi miki magana ki raina masa hankali, in tai wari dai maji, Ke Jalila ban gaya miki ba”
“Ina jinki hajiya Nana jarida”
Nana ta dan hade rai tace “kefa ‘yar wulakanci ce, wace irin Jarida kuma?”
Jalila tayi murmushi tace “Allah yabaki hakuri”
Nana Ta dan saki fuskarta tace “Wai bakiga kwana biyun nan Maama duk tayi sanyi bane”
Cikin ko in kula Jalila tace “Ban lura da hakan ba, tana komai nata kaman yadda take a baya”
“Shikenan tunda haka kika ce amma Anjima zaki rakani wani guri”
“Ina kenan?”
“In munje zaki gani, saura daga baya kice min bazaki ba”
Jalila tace
“zan raka ki Insha Allah, Amrya ba kya laifi”
“kai Jalila har kinsa naji dadi” Nana takarasa fadar hakan tareda fita daga kitchen din.
Koda Jalila ta kammala aikinta ta koma daki, ta tarar da missed calls a wayarta, ta dauka ta bude don duba waye ya kirata haka? Kiran na Jawwad ne da kuma Ahmad, tana kokarin kiran Jawwad ne kiran Ahmad ya shigo wayarta, dan haka ta fasa kiran Jawwad ta amsa kiran Ahmad, Jalila ta shafe lokaci me tsawo suna waya da Ahmad, Sosai Ahmad yake bawa Jalila kulawa, dan tana iya shafe lokaci me tsawo suna waya ba tareda ta kosa ba, sukanyi kwanaki basuyi waya ba, saboda yanayin Aikinsa, dan haka duk lokacin da suka samu dama suna daukar dogon lokaci suna tare a waya, tana cikin wayar ne kiran wayar Jawwad ya dinga shigowa, dan haka sukayi sallama da Ahmad, ta kira Jawwad, tana bugawa ya daga
Jawwad yace “Baby dawa kike ta waya hakane? Da farko na kira baki daga ba, Nakuma kiranki busy busy, for more than hour”
“Am sorry Yaya Jawwad , Ahmad ne ya kirani, shine.. sekuma tayi shiru
Jawwad yace
“Hmmm to shikenan nagane, dama munyi magana da Hanan tace; zasuyi magana da Nana irin kayan da zasu saka na dinner, za’a turawa Abba, A dakko musu, kayan sun iso, ta kira layin Nana baya shiga”
Dan zumbura baki Jalila tayi kaman yana ganinta tace
“suka dai za’a siyawa nikuma fa? Ko tun yanzu anfara ware ni”
“Waya isa ya wareki babyn Abba, A sekin zaba sannan za’a basu su zaba suma”
“to shikenan zan musu magana Insha Allah, ya Aikin kuma?”
“Aiki Alhamdilillah gashi muna ta fama”
“To Allah yabada sa’a”
“Ameen Babyn Abba”
“Ina Jalal? Ya nasa Aikin?” Jalila taji tayi maganar ba tareda ta shirya yinta ba.
Jawwad yace “Kinfara missing dinsa ne?”
Sekuma taji gaba daya ta dirirce tarasa me zatace
“Amm a’a kawai na tambaya ne, don’t mind me, yaushe zakazo”
Jawwad yace
“A’a tsaya, naji dadi da kike tambayarsa, dama be kamata ya samu aiki ta hanyarki, yakama hanya ya tafi nesa da gida kuma ace bakya bincikar ya yakeba, Jalal dai yana nan lafiya, kuma yadda yake nunamin yana jin dadin Aikin nasa, Alhamdilillah ana samun cigaba a rayuwarsa, muna godiya kanwar mu, Allah yabiya ki ladan wannan dawainiya damu da kike”
“Ameen Yaya, to shikenan, naji kaman Maama tana kirana”
Jawwad yace “to shikenan munyi waya da Maaman dazu da safe, Amma in cewa Jalal kina gaisheshi?” ya tambayet cikin zolaya
Da sauri tace
“A’a karka fada, ni bana gaisheshi”
Jawwad yai murmushi yace “Shikenan se anjima”
sukayi sallama, ta danyi Ajiyar zuciya, sannan ta mike, ta tafi bandaki dan daura Alwala anata kiran sallar Azahar.
Da la’asar Nana ta uzzurawa Jalila suka dau mota fita, seda suka tsaya a kasuwa sukayi siyayya, Sannan Nana tace ta rakata Asibiti dubiya, Sam Jalila bata kawo komai a ranta ba ta raka Nana Asibiti, suka shiga female ward, Nana ta tambayi wani daki, aka nuna musu, Seda suka shiga dakin sannan Jalila ta lura da suwaye a dakin, Su Yaya mairo ne a dakin, se Naja dake kwance kaman gawa, ana samata ruwa,
da Jalila tasan gurinsu Nana zata janyo ta, da bata biyota ba, Amma me sukeyi a Asibiti? Ta tambayi kanta, Sallamar dasu Jalila sukayi ne yasa su juyowa suga su waye, Ganin Nana da Jalila yasa su hade rai, Jalila ta samu guri ta tsaya, Nana ta karasa ta zauna, tace
“Yaya Mairo ina wuni”
Rai a hade yaya mairo tace “lafiya”
“Yame jiki kuma?” Nana ta kuma tambaya
A fusace Yaya mairo tace
“ban sani ba gulayya, uwarki ta gaya miki shine kikazo ganin kwaf, hadda dakko wannan annamimiyar shedaniyar, to da dan uwanki ya fasa Auren Naja bata mutu ba tana da rai, sannan ki gaggauta dauke wannan tsinanniyar yarinyar ku bar gurin nan, dan na tsani yarinyar nan bana kaunar ta, Yarinya sekace mayya, wayasani ko bayan Kafirci ta gaji maita, kila ta sha a Nono, kiri2 tana kokarin rabani da ‘yar uwata, za’ ayi Auren nan amma ta shiga ta fita ta hana, makira sedai kici kanki wallahi, kurwarmu tafi karfinki”
Jalila dake gefe tace “kinga nifa ban san nan zamuzo ba, dana san nan zamuzo da bazan biyota ba, ni ban san Naja bata da lafiya ba, dan haka kidena zagina, wallahi kika kuma zagarmin uwa sena rama, ko ina maita zanci naman kune? Me zan ci ajikinku jikin matsiyata, Azzalumai”
Sa’adah ta taso a fusace tazo gaban Jalila ta nuna ta tace “ke karki kuskura ki zagarmin uwa”
“in aka zagetan me zakiyi?”
Jalila ta tambayeta tareda sauke hannun sa’adah tace
“uwata da aka haifa a cikin Arna, da ita nake Alfahari, dan haka duk wanda ya kuma Yunkurin zaginta se inda karfina ya kare”
Nana ta mike da sauri taje tsakaninsu ta tsaya tace
“haba dan Allah, nifa ban kawo Jalila gurin nan dan kuyi rigima ba, nazo in duba Naja ne nace ta rakoni, me yakawo zancen maita, yaya Jalila tayi hakuri a lokuta da dama da kuke cin mutuncin ta, Yaya mairo a rayuwa mussaman idan kanada ‘ya’ ya bakayi wa dan wani gori, kokuma mummunan baki, ……