ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

“rufemin baki ko in gaureki da mari, kema ta shanye ki, shine zakizo kimin rashin kunya, na rufe kofa in muku dukan tsiya a gurin nan”
Jalila tace

“Wallahi babu matar da ta isa in tsaya ta dakeni, wallahi Nana dana san nan zaki kawoni bazan biyoki ba, kuma ki kyalesu karsu fasa zagina, bacin ranki akan an fasa aurar ‘yarkine, badan anyi yunkurin likawa Yaya Jawwad ita ba ba abunda zesa in fadi wani abu a kanta, tunda tun ba yauba nasan halin yaranki kaf, nasan Naja tana shaye2, an gayamin Sa’adah na bin maza kuma kowanne inada tabattaciyar hujja akan hakan, kuma bari kiji ni ce nan nagayawa Abba yayi bincike akan Naja, kuma bincike ya tabattar masa da ba mutuniyar kirki bace, nan gaba in zakiwa dan wani gori ki duba gaba da bayanki ki tabattar bakida abun gorin tukuna, Allah ne ya sa kamin cin mutuncin da kikemin nida uwata, kuma kadan kika gani wallahi, kekuma Nana ingo key din motar kya taho, ni zan hau ta haya in koma gida”
Jalila tayi ficewarta, da sauri Nana ta biyo bayan ta, da kyar ta lallaba Jalila ta hau motar suka nufi gida, harsuka je gida Jalila bata kula Nana ba ta cika tayi fam, suka shiga da kayan siyayyar da sukayi daki, Jalila ta hade rai sosai Nana ta nisa ta zauna a kusada ita tace

“Jalila nasan zakiji ba dadi abunda nayi miki, na kawoki anci mutuncinki, Jalila nasa ki rakoni ne dan kiga sakayyar hakurin da kikeyi, Jalila me hakuri ba a taba ganin bayansa, duk takurar da sukayi miki abaya zagi da cin mutuci, Amma abun Allah agaban Maama cikin jikin Naja ya zube, Jalila sadaukarwarki da jajircewarki akan samarwa wasu farinciki, Allah baze taba barinki ki wulakanta ba, Jalila duk lokacin da naga hawayenki ina shiga matukar damuwa, amma dayawa kikanyi kukane idan kika kasa samarwa wani farinciki, kokuma wani yayi hurting dinki, amma hakan baya hanaki kokarin ganin kinsa nakusa dake farinciki, shiyasa na kaiki kiga sakayyar da Allah yayi miki akan makiyanki, masu saki zubda hawaye, Jalila ina sarawa kokarin ki, masu irin zuciyarki kadan ne a cikin al’umma, Allah ya dawwamar da haske a cikin rayuwarki”
Jalila ta rungume Nana, tana zubda hawayen da bata da tabbacin na farinciki ne kona bacin rai, tace “Nana nagode da addu’ar da kikayi min, dukda kasancewar su yan uwan mahaifiyarki baki juyamin baya ba, Amma Nana har cikin zuciya ta bana murna da abunda yasamu Naja, duk abunda yafaru da mace daya a society makamancin wannan, gurba cewa ce ta al’umma, da Yaya mairo tayi musu tarbiyya me kyau, Allah ka dai yasan mutanen dazasu amfana dasu, kuma da bazan taba adawa da Aurenta da Yaya ba, Amma ina fatan Allah ya shiryesu, yabasu mafita “
“Ameen Jalila “

Tunda Jalal yayi wannan tafiyar be kara dawowa ba, sedai suyi waya da daddyn sa ko Jawwad, Amma Jawwad yaje sau biyu lagos gurin Jalal, dukkan wani shirye2 suna yinsa ne ta waya shida Jawwad, tunda sukayi wannan rabuwar da Jalila basu kara haduwa ba.
Jalal yayi kalau dashi, bashi da tension sosai, sena tunanin irin missing din Jalila da yayi, ‘yan kwanakin da yayi tareda ita, suna shiri ya tsaye masa, amma da zarar ya tuna maganar ta na babu shi babu ita gaba daya se yaji abun duniya ya dame shi, shi kansa yasan Jalila halitta ce me matukar mahimmanci a rayuwarsa, a yanzu yana kokarin yin salloli biyar a rana, dukda ba kowane lokaci yake yinsu akan lokaci ba, yana kokarin yaki da zuciyarsa yaga yayi salla. Amma duk lokacin da yaji abubuwa sun da meshi, yana zama yayiwa kansa caji da giya yadda yakamata.
Sannan Jalal yasaka a nemo masa Hannah duk inda take, se yaga waye gatanta, dan yayiwa kansa alkawarin se yasa an ladabtar da ita, seta gane shiba sa’anta bane da zatayi masa hauka.

Bangaren Jalila ma tana son sanin halin da Jalal din yake ciki, tana son sanin ko har yanzu yana shaye2? Wace irin rayuwa yakeyi zamansa a lagos? Tana tausayin Jalal sosai, musamman idan ta tuna da labarin rayuwarsa da kuma amanar da Antynsa ta bata, ko ba komai dukda fadan da sukeyu takan tuna Alkhairan sa, Amma da ta tuna abunda Mummy da Ilham sukayi mata, gaba daya se ranta ya baci, se taji bata sha’awar kuma shiga shirgin rayuwar Jalal, dama saboda Jawwad suke haduwa, in Jawwad yayi Aure ko ganinta baze kara yiba balle mahaifiyarsa ta zargi wani abu.

Rana bata karya, sedai uwar diya taji kunya inji hausawa, Duk abunda aka sama sa rana inda rai da lafiya zezo, Shirye2 sunyi nisa game da wannan bukukuwa da wadannan iyalai ke tun kara, Jawwad yayiwa Hanan saiti uku na kayan lefe, be cika mata tarkace ba, sedai yazuba mata kaya masu matukar tsada da kyau, haka Nana ita set hudu mahmud yayi mata, itama an zuba mata dukiya (kunsan family su Jalal akwai masu gidan rana) gaba daya kayan lefen bauchi aka kaisu, a can aka karba kayan, na Abdallah ma aka kai kaduna gidansu siyama, gaba daya Basa zama, koda yaushe Hanan tana yawan zuwa kano saboda siyayyar biki.
Duk wani shirye2 Jalila ce kan gaba gurin tsara yadda abubuwa zasu gudana, An shirya gaba daya bikin zasuyi shi a garin bauchi ne.
Saura sati daya a fara biki, su Nana suka tafi garin bauchi inda acan za’ayi dukkan wata hada2 ta biki,

Jawwad da Jalal tare suka je har maiduguri suka kai musu katin bikin Jawwad, dama ga abun dai2 da bikin Nana, rabon da Jalal ya taka kafarsa garin maiduguri har ya manta, Amma bisa ga mamakinsu sega Jalal, dangin Daddy sunyi matukar farincikin ganin Jalal, ya nutsu ba kamar da ba, yasa manyan kaya hada hula, gashi suka samu labarin har aiki yake, sunyi farincikin ganin sa, sun samu kyakyawar karba daga dangin Jalal, dama Jawwad ma dan gida ne, seda suka kwana biyu a garin maiduguri suka wuce bauchi shida Jawwad, sam Mummy bata san batun Jalal yaje maiduguri ba.

Ayi hakuri yau typing babu yawa, nayi busy sosai ne

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Watpad @Ayshercool7724

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

              *ABDUL JALAL*

         _Story, writing and edited _

                        By
              AISHA HUMAIRA
              ( _Daddy's girl_) 

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

        PART 2         
                      _PAGE  4️⃣7️⃣100

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

         _MY FIRST NOVEL _

Shirye2 sunyi nisa sosai ana ta hada2, za’a shiga satin biki, Jawwad da Jalal sun kwana biyu a bauchi suka koma kano domin rabon invitation ga abokan Jawwad, Amma har suka tafi Jalila basu hadu da Jalal ba, duk inda amare suka shiga Jalila na biye dasu, tare sukaje gyaran kai, da kunshi na amare, hatta gyaran jiki da Jalila ake, se sheki take kamar itace Amaryar, in kaga yadda take zakewa kai kace itace amaryar, Ana gobe za’a fara bikin ‘yan uwansu Jalal daga maiduguri suka zo (dangin su Mahmud) lokacin da suka zo su Jalila sun tafi gurin kunshi, tunda suka zo Antyn Jalal ke cigiyar Jalila, Amma aka sanar da ita sun tafi gurin kunshi, guri na mussaman aka tanadarwa dangin mijin Nana. Ana gobe a fara bikin su Jawwad suma suka dawo shida Jalal, duk inda zashi kafarsa kafar Jalal.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button