ABDUL JALAL PART 2

‘yan uwa wanda sukazo daga wasu garuruwan, Inna ta dinga nuna musu Su Jalila Da Nana, tana gaya musu ga’ ya’yan da jikokin kanwarta.
Yaya mairo kam da zuri’ar ta kaf babu wanda yazo taron nan, sedai sauran ‘yan uwa da abokan Arziki.
Se dare su Jalila suka dawo daga gurin kunshi, kallo daya zakayiwa fuskar amaren zaka gane yadda suke cikin farinciki, gashi sun dau kyau Masha Allah, suka tafi part din Anty fido a can suke kwana saboda estate din ya fara daukar harami da baki, kasancewar daddyn Hanan babban mutum ne asanshi sosai. Hakama Abba yanada mutane sosai, ga dangin su Jalal, dan haka estate din cike yake da mutane.
Koda su Jalila sukayi sallar magariba, Hanan tace
“gaskiya sena kira Haidar yazo ya ga kunshin nan”
Jalila tace
“ke zumudin me kikeyi? Kwana nawa ya rage?”
“dan kwana nawa ya rage, se indena kula dashi? Se yaga kunshin nan, in yamasa ayi biki da shi, in yace be kyau ba a dirje shi a daren nan”
Gaba daya sukayi dariya, Nana tace
“ni dama muna gurin kunshi Mahmud yacemin; sunzo dazu suna tareda su Yaya Abdallah, ina son mu hadu da shi, inji ko yaci Abinci?”
Jalila kallonsu kawai take tana murmushi, tana mamakin ya sukeji a ransu game da soyayya haka? Ita dai tasan tana son Ahmad, Amma bata tunanin zata iya wannan rawar kafar akansa kamar yadda su Hanan sukeyi, ko lokacin da take son Yaya Jawwad bata tunanin zata iya abunda su Nana sukeyi, tana kallonsu suka canza kaya, sukayi waya da su Yaya Jawwad suka fice babban palourn part din.
Itama sallolinta tayi, tai wanka ta canza kaya, ta samu ta nutsu tana cin Abinci, ta nayi tana chatting da Ahmad, yana ta mata magiya akan ta fito yana son su hadu amma taki, se wasa take masa da hankali.
Maama ta kira Jalila a waya tace taje main part ana neman ta, haka ta tashi ta tafi, da ita so take ta samu ta kwanta ta dan huta, ta fita ta kofar kitchen yadda su Hanan bazasu ganta ba.
Koda taje, da kyar ta gano Maama saboda cikar da akayi a gidan, Maama tace
“dangin mijin Nana ke nemanki, Antyn Jalal tunda sukazo take cigiyar ki fa”
Jalila tace “Ai ban san sunzo ba, suna ina?”
Maama tayi mata Jagora har masaukin da aka basu, Jalila na shiga Antyn Jalal ta fadada murmushinta tace ” ‘yar halak taki ambato, tun dazu nake cigiyarki”
Cikin fara’ a Jalila tace
“Anty sannunku da zuwa, munje gurin kunshi ne shiyasa, ya kukazo? Ya hanya?”
“Alhamdilillah Jalila, Allah yasanya Alkhairi, ya kaimu lokacin naki Auren, kalli yadda kike sheki kamar Amarya”
Sunkuyar da kai Jalila tayi, alamun kunya, ta gefen Antyn ce tace
“Masha Allah itace Jalila kenan, kai Jalila Allah yasaka miki da Alkhairi, muna godiya da nuna kulawarki ga danmu, last week sega Jalal a maiduguri, babban farinciki danayi, wai aikin dayake ta silarki aka same shi, mungode Jalila”
Gaba daya Attention din sauran da suke dakin ya dawo kanta, wasu suna magana da hausa wasu nayi da yare, suka dinga yi mata Addu’a, tarasa Addu’a mema suke mata haka? Kamar wadda ta basu wata gagarumar kyauta.
Dangin Jalal suna da matukar kirki da karamci, nan Antyn Jalal ta dinga nuna mata dangin Jalal, tana gaya mata kowacce mecece a gurin Jalal, ‘yan gayune, kuma kallo daya zakayi musu kasan suna hutawa, gasu kyawawa abunda ta lura da shi shine, gaba dayansu babbar shedar da zaka gane family dinsu da shi, shine wannan dogon hancin irin na Jalal, mazansu da matansu haka suke kayan dogon hanci, Kamar sun saba da Jalila suka dinga yi mata hira, gaba daya Jalila jinta take a takure, Anty ta lura da hakan dan haka tayiwa Jalila sallama, tace seda safe.
Jalila na fitowa tana sauri takoma part dinsu ta hadu da Yusuf a hanyar shiga babban parlour, yace
“Yawwa Alhamdilillah, naji dadin ganinki a yanzu, zomuje kimin wani dan aiki”
Jalila tace
“to Yaya” yana tafe tana binsa a baya, ya shiga inda ake ta hada2 dafa Abinci, ya dakko wani kwando da manyan warmers akai da plates, da spoons da serving spoons, yabawa Jalila ta karba ta rike, shikuma ya dakko cartons na ruwa da lemuka, yace
“muje Bakinmu nasa akayiwa girki, dare yayi Abinci ya kare
” Jalila ba tace komai ba ya shiga gaba ta biyo bayansa, wani part din suka nufa, ita bata taba sanin da gurin bama, saboda parts din da suke bangare daya na estate din ma dayawa, tundaga waje harabar part din ake iya juyo hayaniya na tashi da dariya na ‘yan maza, Yusuf ya shige gaba yasa hannu ya bude kofar ya shiga, ya juyo ya ce mata
“Shigo Jalila”
ba musu ta bishi da kayna a hannunta, kallo daya tayi musu ta sauke kanta, mazane sun kai su bakwai a cikin palourn, inma basu fiba, dan haka duk taji ta takura, kanta a sunkuye ta dan risina ta gaishesu, suka amsa mata gaba daya, dayan yace “A’a wannan kaman Hanan”
Taji muryar Abdallah yace
“Ba Hanan bace, sister dinta ce, Amaryar Ahmad to be”
Ahmad yace
“Tun dazu nake magiya ki fito in ganki kika ki, cikin sa’a sega Yusuf ya kawomin ke, amma dan mugunta ya hadaki da wannan kayan nauyin, memakon shi ya dakko”
Sunkuyar da kai Jalila tayi tana sauke kwandon hannunta, Yusuf yace
“Au ban maka abun Arziki bako? Nida yakamata ka godemin”
Ahmad yace
“nina isa in fadi haka, ince bakayi min abun Arziki ba, Kamin abun Arziki sirikina, wallahi Yusuf ji nake kaman a daura namu auren nida Jalila” ya dan kalli Jalila yace
My Queen yakamata muyiwa Daddy magana, yadda kikayi shar dake haka kamata yayi kawai muma ayi namu”
Jalila ta sunkuyar da kai cike da jin matsananciyar kunya.
Daya daga cikin Matasan yace
“dan banza uban zumudi, dole kayi zaman jiran shekara guda, kacigaba da lallabawa da Ameera, kokuma kayi biyu babu”
Gaba daya kunya suke bawa Jalila, tayi kokarin mikewa domin tabar dakin, ta mike kenan kawai idonta ya sauka ana Jalal da tunda ta shigo bata kula da shi ba, farar Jallabiya ce a jikinsa fara kal, sumar kansa ta sha gyara se sheki take, watanni hudu kenan bata ganshi ba, amma ya kara kiba, gaba daya ya tattara hankalinsa akan danna waya da yakeyi amma gaba daya idonsa akan Jalila yake, yana mata wani irin kallo da takasa gane na menene? Tuhumace, kokuwa meyake nufi?
Muryar Abdallah taji yace
“Queen kin san kuwa ranar dinner, Siyama zasuzo ayi dinner anan, ranar daurin aure in angama da nan, zamuje kaduna a can gidansu za’a daura namu”
Cikin sakin fuska ta juyo tace “Dagaske Yaya Abdallah, zanga Siyama? Rabon da in ganta tun ranar dana bar kaduna”
Ahmad yace “tasan Amaryar taka ne?”
Abdallah yace
“tabdijan Aminiyarta ce ta kuruciya, wadda take Jawa duka, kai Jalila ai an girma an dena neman magana, Siyama tana bani labarin wahalar da ta sha saboda ke, gaskiya badan badan ba sena rama mata”
Jalila ta dan zumbura baki sannan tace “Seku rama din ai”
Ahmad yace “Ka rama me? Munci bulus ko queen?” ta dan jinjina kai tana murmushi.
Koda aka bude warmers din nan, jallof couscous ne, ya sha nama da kayan vegetables, ta dan kalli Jalal ta kalli Abincin tasan Jalal baya cin Couscous kome zeci oho?
Kai bazakace Jalal yayi existing a dakin nan ba, duk hayaniyar nan da’ake yi, kala bece ba, shida kujerun gurin kusan daya, dan ko uffan baya cewa, ko abun dariya sukayi fuskar nan tasa murtuk take babu alamar wasa.
Kallon da yake wa Jalila gaba daya yasa ta tsargu har taso ta diricice, dan haka tace “seda safenku”
Ahmad yayi farat yace
“tsaya in rakaki zamuyi magana”
Yusuf yace
“Sena gayawa Amira, wannan rawar kan da kake yi”
“Karka fasa gaya matan”
Jalila ta nufi hanyar fita, dan gani take kaman Jalal ze iya tashi ya dizgata agaban mutane, tana kokarin wucewa tayi tuntube da kafar Jalal kasancewar ya mike kafafunsa kuma takusa da kafafunsa zata wuce, ga shi a rude take dan haka ta kusa faduwa, Allah ya temaketa bata fadi ba tace “Subhanallah” shikam Jalal ko a jikinsa dan ko kallon inda take beyiba, Ahmad yace
“Haba ya haka? Kana kokarin nakasa min mata, ka baje kafafunka akan hanya, at least yakamata ka bata hakuri”
Wani irin kallon baka isaba Jalal yayi masa ya maida kansa kan wayarsa ya cigaba da abunda yakeyi, ba tare da ya furta koda harafi daya ba Jalila tace