ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Washegari yakama ranar daza’ayi dinner, tun safe ake shiga ana fita a gidan nan, gida yacika da mutane,
Shabiyun Rana Siyama ta iso itads ‘yan uwanta, Labari na ishe Jalila Siyama ta karaso aids gudu ta nufi cikin gidan tana zuwa suka Rungume juna, Maama tace
“Jalila kiyi a hankali, karki ji mata ciwo mana”
Jalila tace “Siyama ta, dama zan kuma ganinki?”
Siyama tace “gani kuwa kin ganni” Jalila ta janye Siyama, Zuwa bangaren Anty fiddo, Hanan Ma na ganin Siyama ta rungumeta itama tace “Na dauka tun ranar kamu zakizo, Amma shine baku zoba se yau”
Siyama tace “Ai muma munyi kamu da party a can ne, saboda wanda bazasu samu damar zuwa nan ba”
Suka gabatar da Siyama ga Nana, dan basu san Juna a zahiri ba, Amma sukanyi waya saboda Jalila,
“Nana tace, Sannu da zuwa Siyama, ya hanya?”
“lafiya kalau Nana, ya taro?”
“Alhamdilillah”
Suka zauna suka dinga hira, suka shantake a gurin, suka dinga hira suna tuna kuruciya da shiritar da sukayi, Nan Jalila ta dinga basu labarin Artabun fadanta da Jalal, har lokacin daya taba yi mata duren hayakin taba. Sunsha dariya, Nana sam bata san rashin jituwarsu ta kai haka ba, Amma bata gaya musu fadi tashin da ta dinga da kokarin ganin ya shiryu ba, har labarin su Hannah da Jeje bata gaya musu ba. Suka shantake suna ta dariya.

Anty Fiddo ta shigo ta samesu a zaune suna hirarsu suna ciye2, kaman karsu rabu, Anty fiddo tace
“waikuna nan a zaune, kamata yayi ku hanzarta ku fara shiri, ku tafi gurin kwalliyar nan, kar a bata lokaci” seda ta kai aya ta lura da Nana, taana ganin Siyama
“Tace Amryarmu, gaskiya Abdallah ya iya zabe, Jalila ke Alkhairi sanadiyar kawancenki da Hanan, mun gano ‘yan uwanmu, kuma sanadiyar ki Abdallah yayi mata shima, Allah ya kaimu Aurenki da Ahmad”
Hanan tayi farat tace
“ba Ameen ba”
Anty fiddo tace
“Saboda me?”
“nifa bana son Auren ta da wannan Yaya Ahmad din wallahi, matarsa bata da mutunci, wannan Ameeran tab, ni wallahi bana son Auren su”
“ina ruwana da rashin mutuncin matarsa, dai dai da ita nake, ai dani ze zauna ba dake ba”
Siyama tace
“Nikam Jalila ina Jalal, ina son in ganshi”
Tsaki Jalila tayi tace “ina nasan inda wani Jalal yake”
Hanan tace “Karya takeyi, yana nan Haidar ya gayamin, suna tare”
Nana tace “Too Siyama kema kin san Jalal, ai dole ki ganshi, nasan watakila anjima yaje gurin dinner zaki ganshi”
Anty fiddo tace “kunga abar surutun nan haka, ku tashi ku fara shiri”
Haka su fara shirye2, karfe hudu suka tafi gurin kwalliya.

Karfe tara na dare Jalila tana tareda Amare an musu kwalliya me daukar hankali, kayansu iri daya, sea green din material, da takalmi da purse, Jalila kuma tasaka blue-black na material kaman yadda shine yazama ankon dinner, Tasaka bakin takalmi da jaka, jikinta babu mayafi, Su Jalila ne ‘yan shigo da Amare, masu shigo da amare kowacce gefenta da namiji da, Amare da Angwaye, Jalila Ahmad ne a gefenta, suka shigo da Angwaye, ana musu hotuna tareda likin kudi, suka kai su har kan high table, nan aka tsaya aka fara hotuna, Ba zato ba tsammani Jalila taga Jalal, sanye da shaddarsa coffee colour, me tsadar gaske, ta sha aiki da bakar hula da takalmi sau ciki, tsinstiyar hannunsa dauke da wani dankareren Agogo, fuskarsa ba yabo ba fallasa, ya durkusa gefen Jawwad yana masa magana a Kunne, nan aka shiga hotuna ‘yan uwa da abokan Arziki, Jalila anyi hotuna da ita ba Adadi, nan Hanan ta nunawa Siyama Jalal,
Siyama tace “Yadda Jalila ke masa rashin mutunci bazakace haka yake ba, hadadde dashi” sukayi dariya
ba karamin kyau Jalila tayi a idon Jalal ba, Amma ganinta ba mayafi yasa duk yaji ransa ya baci.
Nan aka fara gudanar da taro kaman yadda aka tsara, dukkan bangarorin sunyi bajinta gurin lika dukiya kaman ba’a san dadinta ba, Hajiya Salma ba’a barta a baya ba gurin yin wannaan hidimar, tunda ta hau kan stage Jalal ya fito ya dinga lika mata kudi, kamar be san ciwonsu ba. Aka dinga mata kirari, ko Mahmud da ta haifa bata masa likin da tayiwa Jalal ba, ta koma gefe, takira Jalila tasa me hoto ya dinga daukarsu hoto itada Jalila da Jalal.
Hakama Sunsha hotuna Jalila da Maama, Jalila tayiwa Maama likin kudi sosai ta dinga rungumeta suna hoto a wayar Jalila, kamar ba Maaman da take gallaza mata ba.
Lallai halayar Jalila daban take, sam bata riko.

Aka jima M. C ya kira Amare da Angwaye kan stage, suna dan takawa, yasaka wakar da Jalila ke matukar so, dan haka stage din nan ba kowa se Amare da Angwaye, Jalila ta fito, tafara Rawa itada Su Hanan Jalila Rawa take me cikeda daukar Hankali, ba wani girgiza jikinta take ba, Amma ta dau hankalin mutane, Ahmad ya fito ya dinga mata barin kudi, ana musu hotuna.
Jalal ya kai karshe a bacin rai, Ga jikinta ba mayafi, ga dinkin yayi fitting dinta, gata tubarakallahu tana da diri me daukar hankali bawata rawa take ba, juyi kawai take Amma Jalal ya kule musamman yadda Ahmad ke mata barin kudi, yana mata wani irin kallo, wayar Jalila ce tafara ringing dan haka ta sakko daga kan stage din ta fita daga hall din domin amsa wayar, tana fita Jalal yabi bayan ta.

Tofa Fans Oga Jalal ya dau Zafi, A tunanin ku mezeyiwa Jalila?
Nayi muku dogon typing dan haka ina bukatar Comments
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ???? ????
My Love for you is endless, daku da masu bina pvt da masu karanta littafin duk ina godiya Allah yabar kauna, ina sonku kaman yadda kuke nunamin kauna

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

What’s app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ????

              *ABDUL JALAL*

         _Story, writing and edited _

                        By
              AISHA HUMAIRA
              ( _Daddy's girl_) 

PERFECT WRITER’S
ASSOCIATION????

(???????? ????????ℕ’???? ℙ????ℝ????????ℂ???? ???????????? ????????’ℝ???? ????????????????????????, ????ℝ????????ℕ???? ????????ℝ ???????????????? ???????? ???????????????????????????????? ????ℕ???? ????ℕ????????ℝ????????????ℕ ????????ℝ ℝ????????????????ℝ????????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

        PART 2         
                      _PAGE  4️⃣8️⃣101

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

         _MY FIRST NOVEL _

Daddyn Jalal ne a tsaye da yana rataye da ‘yar karamar Jaka, da alamu zeyi tafiya ne, Mummy na kan three seater ta kalmashe kafa tana danna remote. Daddy yace

“wai dagaske deeja bazaki bikin nan ba?”
Ya tsina fuska tayi tace

“Nifa bana son yin doguwar tafiya inba a jirgi ba kasani, kuma me zanje inyi musu, banda jaraba ayi biki a inda suke sun kwasa sun tafi wata uwa bauchi biki, ko meye amfanin hakan oho?”

Daddy ya samu guri ya zauna yace
“deeja, in duniya da gaskiya be kamata kiyi haka ba, duk gudunmuwar da Jawwad ya bawa Rayuwar danki, ga tsawon lokacin da kika dauka kuna makotaka, ga harkar kasuwanci da kikeyi da mahifiyar yaron nan, sannan koba komai kema Mahmud danki ne, shima kodan shi bazaki ba? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button