ABDUL JALAL PART 2

ABDUL JALAL PART 2

Bayan Jawwad ya dawo daga school suka zauna domin cin Abinci rana shida Jalal, Jalal ba karamin dadi yajiba ganin wainar shinkafa ce, sunci Abincin nan sosai, Jalal yace “Jawwad dan Allah in da sauran Abincin nan ka zubamin in kaiwa daddy, kasan yana son wainar shinkafa” “Hakane Allah yasa akwai, bari inje cikin gida in duba” Jawwad ya tafi domin dubawa koda Abincin, Jawwad na fita aka kirashi waya, Jalal ya daga wayar ya duba, seyaga sunan Hanan, Murmushi yayi ya daga wayar
“Jawwad ka manta dani ko? Baka daga wayata, nashiga wani hali banajin dadin abunda kakemin” gyara murya Jalal yayi
“ba Jawwad bane, Jalal ne” “Jalal kaine yakake ya gida” “lafiya kalau ya Abdallah, kodayake muna waya dashi” “Yana lafiya, Jalal kaga abunda Jawwad yakemin ko? Banajin dadin hakan, dan Allah kasa baki, Jalal inason abokin ka da wasa na dau abun amma yanzu serious nake sonshi, Jalal help me, so masifa ne, da ban yadda da hakanba se yanzu” “kinaji Hanan, kiyi hakuri Jawwad inyace baya Sonki karya yake, kawai yana duba alkar dake tsakaninki da kanwarsa, amma karkidamu zamuyi magana dashi” (???????????? nikam nace su Jalal dama an iya rarrashi haka) Ajiyar zuciya Hanan tayi “to nagode sosai Jalal, agaida su Ilham”
Jawwad ya shigo da food flask a hannunsa, ya ajiye ya kalli Jalal, “gashi nan Abincin Baby ne tace abawa daddy, amma dawa kake waya haka a wayata”
“Jawwad” “Na’am ina jinka” “Meyasa kakewa yarinyar nan hakane” “Wace yarinyar kenan?” “Hanan mana, ta damu da kai, kamanta kaikake min fada akan Ilham segashi kaima kanayi, meye marabar Hanan da waccan fitsararriyar banzan, ba gara Hanan din bama tafita nutsuwa da saukin kai” “Haba Jalal, Jalila da soyayyar ta na tashi, banason yin abunda zan bata mata rai, tarayyata da Hanan baze haifar da da me idoba, kuma Hanan da kake ganinta itama rigimammiyace, kaikewa Jalila wani kallo dan bakwa jituwa”
“Jawwad yakamata kakoma hankalinka, kayi wani abu akan yarinyar nan mana, kana ganinta so classic nasan da wanine ba kaiba zata sauke ajinta tace tana sonsa ne? Kayi wani abu mana” tsaki Jawwad yayi
“Ina tsawon shekaru Ilham ta dauka tana nuna maka so, kai mekayi akai”
“Jawwad kasani nasani, nida Ilham bamu dace ba, kuma kasan dalili, kuma bari in sake jadadda maka, kokuma in tunamaka wani abu, mahaifiyarka bazata taba bari ka auri Jalila ba, musamman in wannan magananniyar matar tana nan, kaima kasani, kayi tunani Jawwad kafin al’amura su kwabe maka” yana gama fadin haka ya kwashi food flask din yai ficewarsa, yabar Jawwad a zaune yana tunani.
Jalal yana zuwa gida ya tafi part din daddy da fara’arsa, “daddy ina fatan bakaci Abincin rana ba? ” “banciba ina shirin ci dai” “Abincin daka fiso nakawo maka” Jalal ya turawa daddy flask din ba karamin murna daddy yayi ba daganin Abincin da Jalal ya kawo masa, “Jalal inaka samo wannan Abincin?” “a gidansu Jawwad” “yaushe rabon da inci masa” daddy ya dan kalli Mummy “Madam kindenamin Abincin gargajiya, mussaman favorites dina” “hmm ba gashi danka yakawo maka ba sekaci ai” daddy yai murmushi “Jalal wayayi girkin nan yayi dadi” “nima bansaniba” Mummy tace “nasan baze wuce Jalila ce tayishiba, dan Maama bata fiye yin girki ba Nana kam dama ba a maganarta akwai son jiki” daddy yace “Jalal inka koma ka turomin takwararka, kafin inkoma England inason inkuma cin irin Abincin nan” hade rai Jalal yayi “daddy waibaka san sunanta bane zaka dinga cemata takwarata” murmushi daddy yayi irin na manya “hmmm to ko in tunamaka tarihin yadda aka samata sunan ne? Dan naga kaman ka manta” “Wai daddy meyasa kake son yimin haka, abune yafaru shekaru da suka wuce kuma kuruciyace baya wuce ba” murmushi daddy yayi “kaji tsoro kenan” “niba wani tsoro danaji” “hmm Jalal kenan, a shikenan tunda kaki yadda” ganin daddy yana neman takura masa yasa yatashi ya fice, bayan fitar Jalal ne Mummy ta kalli daddy “daddyn Jalal, inason muyi magana da kaine” “to ai gani ina jinki”
“Dama gani nayi lokaci yayi daya kamata mucika muradin yaran nan, ina ganin Jalal idan akayi masa aure ze samu nutsuwa, ze rage abubuwan dayakeyi” Ajiyar zuciya daddy yayi
“to yanzu wace yarinyar kike gani zata auri Jalal a wannan halin dayake ciki?” “to ai Jalal yanada wadda yakeso, ga Ilham nan suna son junansu, yakamata kawai ayi magana asaka rana” “kin tabbatar da duk su biyu suna son junansu” “Eh mana sun son junansu, yakamata ayi magana kaje kasamu baban Ilham ayi maganar auren nan” “Kina ganin ba matsala a yin hakan, sunada banbancin halayya, kaman zamansu bazeyi dadi ba” “kaga tunda dai suna son junansu a haka ai shikenan” “Amma ni Jalal be taba yimin wannan zancen ba” “to aini gana nagaya maka” daddy yayi Ajiyar zuciya, be kuma cewa komai ba”.
Jalila kwance akan gadonsu ta dakko wayarta ta kira Alhaji Kabiru amma be daga ba, dan haka ta sauka tafara chatting, tana what’s app tana hira da zahra, setaga Alhaji Kabiru yakirata, ta daga wayar amma batace komai ba, setaji yana cewa
“Jabir Nakiraka bata shiga, se yanzu tashiga, kayan sun taho daga kudu, munyi waya sunkusa karasowa kano za a sauke a gidan gonata, kaje ka karba se ka rarraba musu cikin dare, kayiwa Jeje magana shima yazo ya karbi nasu” shiru Jalila tayi, wane irin kayane wannan? ta kashe wayar , ta maimaita “Kaya a rarraba cikin dare, kuma hada Jeje” what’s app ta koma da sauri tai masa sallama, amma beyi reply ba, ajiye wayar tayi tanata tunani, besan lambar waya kiraba kenan, “Allah nagode maka nafara samun hint akan mutumin nan, Allah kabani mafita” wayarta takuma dubawa setaga ya amsa mata sallamar
“barka da rana, ranka ya dade yakake ya harkoki”
“lafiya kalau, wake magana?” shiru Jalila tayi tana tunanin wani suna zata gayamasa, kawai setace masa “Halima ce” “Wace haliman?”
“hmm duniya da gaskiya kuwa? Wadda kabawa complementary card a banki” “ohhh am so sorry, kuma seda na kawo kece dan na dau muryarki, sedai dan bansan sunanki bane, ina fatan kina cikin koshin lafiya, Gimbiya Halima” “Ina lpy” “Amma nayi mamaki, dakika nemeni, danaga kin yaga card din banzaci zaki nemeni ba, nayi farinciki gaskiya” Jalila ta biye masa suka dinga chatting, daga baya ta sauka ta rufe data dinta,
Jinjina kai tayi, “lallai wannan mutumin zakayi saurin fadawa tarkona, Kuma abun mamaki, wani kayane ake rabawa cikin dare, ga sunan Jeje ya ambata, to me hakan ke nufi, wannan ya tabbatar da yana hulda da Jeje, to wace irin hulda Alhaji Kabiru yakeyi da JeJe haka, wanda yasashi zuwa gurin birthday din Jalal a boye, kai akwai lauje cikin nadi” tana tsaka da wannan tunanin still aka kuma kiranta a waya, koda ta duba tagane lambar Dan sandan nan ne, tsaki tayi harta ajiye wayar sekuma ta yi wani tunani ta daga
“Salamu alaikum” amsamata yayi sanna yace “beauty barka da wannan lokacin ya kike seda ta dan tura baki gaba “Lafiya kalau” “dama cewa nayi bari inkiraki inji lafiyar ki, sannan inaso inzo gidanku in ganki”
“What gidanmu kuma mezakayimin” “Meye abun tashin hankali, inasonki ne aurenki nakeso inyi, please” ture wayar gefe tayi takama dariya sannan ta maida wayar kunenta “Ni wallahi kabani kunya yar baby dani yaushe na isa aure, kuma ya za’a yi Abbana ya aura maka ni, ni gaskiya yarinya ce” yadda take shagwabar ba karamin birgeshi takeba
“Haba yar baby wayace miki baki isa aure ba sannan kuma babu kunya a soyayya” “Babana bazemin aure yanzu ba kuma yariga yabadani, amma nima bansan wayabawa ba” Ajiyar zuciya yayi “bayarwa ba aure bane dan haka zancigaba da neman aurenki”
“Hmm shikenan se anjima, zanyi karatu yanzu” “To Baby tunda kinki gayamin sunanki, ayi karatu da kyau, inkinki mu hadu zannemo gidanku inzo gurin Abbanki da kaina” “Sekazo” daga nan ta kashe wayarta “tab ina zan kai wannaan mutumin”
Bayan sallar la’asar, Jalal yakoma gurin Jawwad, koda yaje ya tarar dashi wani iri kaman mara lafiya, Jalal bebi takan tambayar meyake damunsa ba, saboda yasan akan maganar dazu ne,
“Jawwad daddy yace yana son ganin kanwarka”
“wacce daga ciki?” “wadda ta yi Abincin yau”
“Jalila ce tayi, Allah yasa ba laifi tayiwa daddy ba” “nima bansaniba yace dai taje yanason ganinta”
“zangaya mata Insha Allah” “yayi kyau bari in tafi in kyaleka naga kana cikin damuwa tunda mukayi magana dazu, karka bata lokacinka gurin dogon tunani, maganata itace gaskiyar lamari, duk inda zaka juya kayi tunani kasani maganar dayace mahaifiyarka da yan uwanta basa som wadda kakeso kuma bazasu bari ka aureta ba, dan haka mafita kacireta a ranka ka maye gurbinta da Hanan”
“Jalal tayaya wannan abun ze yuwu, ni Jalila nakeso, Kuma maganar Maama nasan zata amince ne in na lallabata” murmushi Jalal yayi “Shikenan Allah yabada sa’a, amma karka manta da batun kiran daddy” yana gama fadin haka ya fice.
Tunda Jalal yafuta tunani ya damu Jawwad, wayarsa ya dauka ya kira Jalila suka dinga hira, har ya manta da abunda yake damunsa, daga nana yagaya mata daddyn Jalal yace taje yanason ganinta.
Jalal yana komawa gida, kozama beyiba kiran Hannah yafara shigowa wayarsa, tsaki yayi ya ajiye wayar ya shiga sabgoginsa amma tacigaba da kiransa, takirashi yafi sau goma, a fusace Jalal ya dau wayar
“Hannah kina bina bashine? Wannan kiran haka meya faru?”
“Niko nake binka bashi Jalal, meyasa kake wahalar dani hakane? So seya koma kiyayya bana sukuni idan banganka ba, Jalal dan Allah ka tausayawa zuciyata, Jalal kasan Masifar So kuwa? Na tabbatar dakasani dabakaimin haka ba, Jalal ka dubi girman Allah ka tausayawa zuciyata” murmushi Jalal yai kaman Hannah naganinsa
“Hannah kenan, ina mamakin sanda soyayyar da kikemin ta rikide zuwa ta gaskiya abun akwai mamaki gaskiya, but don’t mind me akan abunda na fada kinji, nagaya miki gaskiya tun farko, baze yuwu ace nayi yawon club sannan ace matata ma tsohuwar yar club bace, dukda zuwa club dinmu yanada banbanci, kiduba a samarin club dinnaki kisamu wani ku daidaita amma ba Jalal ba”
“Amma Jalal ai nace maka na tuba wallahi inka aureni zandena”
“Ni ABDUL JALAL nafi karfin ragowar garorin bariki, ki kiyayeni” yana gama maganar ya kashe wayarsa.
Daddy sam yakasa yadda da batun Mummy gameda Jalal, shidai yasan Jalal ko zancen mata bayaso ayi masa, amma ya akayi haryake soyayya da Ilham besaniba dukda yana dadewa baya nan, amma yasan da zeyi masa zancen, dan haka ya yanke shawarar kiran Jalal yaji tabakinsa.
Hanan na kwance akan katafaren gadonta, tayi zurfi a tunanin ta, taji an turo kofar dakinta, dan daga kai tayi taga mum dintace, batace uffan ba tai shiruu tacigaba da tunani, gefenta Mum tazo ta zauna ta dafata “Auta meyake damunkine, yan kwanakin nan kullum cikin damuwa kike meyake damunkine” a hankali Hanan ta tashi zaune “Mummy na ba wata damuwa, damuwar school ne kawai kinsan akwai tension na makaranta”
“Hakane Hanan, amma yusuf yakawomin kararki fa” dan ya mutsa fuska Hanan tayi “Meyace miki?”
“gaba daya kin canza masa yakasa gane kanki, meyake faruwa ne?”
“mummy kinsan tun farko dama ni bawani yimin yaya ba kinsani, Mummy kinsan wani abu kuwa”
“A ‘a sekin fada”
“tun farko kinsan ba son Yusuf nakeyiba, Mum zuwana kano naga Yayan Jalila cousin dinta wanda takeso, da saboda in tsokaneta nace ina sonshi, amma daga baya abun yakomamin Gaske, Mum ina son Abunda Jalila takeso ne, kuma yazama dole tabarmin dan basu dace ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Leave a Reply

Back to top button