ABDUL JALAL PART 2

“Yaya Jawwad kaine?”
“Nine Baby, yaya borno yasu Anty?”
“lafiya kalau Yaya Jawwad, kayi kiba sosai kaman ba kaiba, ina Hanan?”
“tana kitchen tana girki, kema gaki nan kinyi kibar ai, ya mijin naki?”
Tabe baki Jalila tayi tace “yana can lagos” Hanan ce ta taho da gudu ta haye kan cinyar Jawwad tace
“Hi queen, ya kike?”
“Wow Hanan, wannan kwalliya haka, masha Allah, naji dadin ganinku wallahi nayi farinciki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku, yara muku kaunar juna”
Tausayinta yakama su Jawwad, Hanan tace “Jalila kunyi waya da Nana kuwa?”
“Eh munyi waya da su, ya Abuja ya zaman kadaici?”
Jawwad yace
“muba ma zaman kadaici ko My sugar, masu zaman kadaici suna Azabtar da zukatansu sun san kansu” yai maganar yana kallon Hanan, Hanan tace “Sosai makuwa, ba wani kadaici, kullum muna tare, kema kice akaiki gidan mijinki kigani in zakiji wani kadaici”
“Allah ya kiyaye” Jalila ta fada tana harar Hanan. Wayar Jawwad ta fara ringing, Jalal ne yake kiransa, Jawwad yace
“Baby mijinki ke kirana, bari inje in amsa” Hanan ta zauna akan kujera tace “Jalila wai yaushe zaku sauke wannan taurin kan ke dashi ku fuskanci juna?”
“Hanan ya kikeso inyi ne? Nagaya muku Jalal ba sona yake ba, kawai an lika masa ni ne, tun lokacin biki nake rashin lafiya be nemeni ba, ko ta kaina bayabi, se ranar da ze tafiya ya ajiyemin takadda, sam be damu dani ba, Hanan ku kukayi dacen Auren soyayya amma bani ba, nasan da Ahmad na Aura baze watsi da lamarina ba” kan Jalila ta gama maganar har hawaye ya wanke mata fuska. Cikin taushin murya Hanan tace
“Jalila, kina da Aure yanzu be kamata kidinga ambaton wani namijin ba, Sannan Jalila kinsan halin mijinki tun kafin kuyi Aure, bashida shiga sabagar mutane, dukda ke matarsa ce yanzu, Amma kiyi hakuri, komai ze wuce Jalila, kalli yadda kikayi kyau kamar a saceki a gudu, i wish yana nan yaga wannan kwalliyar taki se ya rude, waima me suke bakine kikayi wannan kyan”
Murmushin takaici Jalila tayi tace
“Hanan kenan, kina tunanin zanyi wani abu daze gani ya yabane? Ko ya burgeshi, shi ba sona yake ba kawai an aura masa ni, be damu da yasan a halin da nake ba balle ya yaba kwalliya ta, se an jima ki gaida Yaya Jawwad.
Jalila ta ajiye wayar ta dora sabon kuka me sauti.
ji tayi an dafata, ta dago ta kalli wanda ya dafata Husna ce fuskarta dauke da damuwa tace
“Sorry dear, please stop crying, kidena kuka ko tunanin broz Jalal baya sonki, is not like that, ina kula da yadda kuke share juna kedashi, which is total bad, an riga an daura Aurenku, kamata yayi ku manta da abunda ya wuce, Jalal has a social disabilities at times, tun lokacin da yakoma drunker, mutane suke kyamarsa he decided to isolate himself from the people, he dint interact with people as before, believe me he loves you bazaki gane hakan ba sekin zauna da shi, yanada kirki sosai, ki dena yawan kukan nan please “
Jinjina mata kai Jalila tayi Husna tace
” Yawwa mrs Jalal, Jalal bashi da matsala bayan ta shaye2, zaki maida shi yadda kikeso, yana sonki ne shiyasa yakeyin abunda kike so, ba dan haka ba a duniya akwai abunda ba wanda ya isa Jalal yayi wani abun yayi. Husnah ta cigaba da rarrashin Jalila, a lokacin take gayawa Jalila Tanada Aure, mijinta baya gari ne, shiyasa itama tazo tayi zamanta a gida.
Ilham takasa zaune takasa tsaye, kwanata kusan shida a gidansu suna sakawa da warwara akan yadda zasu bullowa lamarin ita da umanta, yanzunma zancen da suke kenan
“Umma kin san kashinmu ya bushe idan yarinyar nan ta tare da Jalal, aikin ze lalace ne fa, zamu rasa komai, jiran da mukayi tsawon shekaru mu dauki fansa ze tashi a banza ne, indai yana tareda yarinyar nanmun rasa komai, daular da muke hange bazamu sameta ba”
Umman Ilham taja numfashi ta hura hanci tace
“Bazan taba yadda tsawon wannan lokacin daukar fansa ta ya tsaya akan lalacewar Jalal ba, dole in wulakanta khadija in mallake dukiyar da take takama da ita, sena ga ta wulakanta daga ita har Habib din”
Ilham tace “Umma to tayaya?”
“ki kylaeni kawai, nasan abunda zanyi, tunda ke kinkasa abunda ya kaiki gidan tsawon lokaci”
“Umma kenan, ba kasawa nayi ba, nayi iya yina, ba daban wannan Jalilan ba da tuni an wuce gurin, Amma ni hankalina a tashe yake umma, kin san abunda Aure ga Jalal yake nufi fa a shirin mu, so soyayya da wata mace bayanni ga Jalal kim san barazana ce a garemu, wallahi ko bacci bana iyayi”
“ni nace ki bar komai a hannuna, nasan me zanyi”
“Shikenan Umma”
Mummy har gidansu Jawwad taje da kanta, ta tarar da Maama tana ta fama da aikin gida. Cikin fara’a Maama ta tareta tana mata sannu da zuwa
Aikuwa a fusace mummy tace
“kinga niba yashe bakinki nazo gani ba, ba hakoranki nazo ki nunamin ba, baban su Jawwad na nan ne?
” A’a baya nan lafiya kuwa? “
” ina fa lafiya, saboda tsabar munafunci a haďa kai da ke a cuceni, a Aurawa Jalal wannan yarinyar dake kanki kinsam bata da cikakken Asali, meyasa baki yadda an
An aurawa ďanki ba se nawa ďan, wannan yarinyar mara mutunci akan me? Sumi2 da ita kamar ta Allah amma tana bin ďana”
Maama tace
“Subhanallah ni kaina ban san da batun ďaurin aurensu ba se ana i gobe ďaurin Aure, kuma iyayensu mazane suka yanke wannan hukuncin baniba, da amincewar mahaifinsa aka aura masa ita”
“ke kikasani koma suwaye suka amince, saboda tayi kwantai tarasa miji se abawa ďana, Allah kadai yasan abunda aka dukunkune aka bashi”
“Mummy Jalila ba kwantai tayi ba, tanada masoya, Allah ne yayi matarsa, Sannan be kamata kidinga wannan maganganun ba karkizo kiji kunya wataran kamar yadda naji kunya nima, Ni data zauna taredani tayi zaman hakuri dani na tabattar Alkhairi ce ga rayuwar Jalal, a irin zamanbda tayi a hannuna nasan halinta”
“kinga dan Allah ki sauraramin bana bukatar jin wa’azinki, tunda baya nan, ki gaya masa ya shirya karbar karamar bazawara, dan sena kashe Auren nan, ban ga dacewar Jalal da wannan yarinyar ba”
Maama tace “Shikenan duk yadda kika gani, komai ya samu bawa mukaddarine, dadinta ma ďan naki ba wani kintsatse bane balle aji haushi dan an rabu da shi, naga ke kanki baki isa da shi ba, temaka masa akayi aka bashi yarinyar nan, kuma duniya da gaskiya baki isa ki biya Jalila da mahifiyarta abunda tayiwa ďanki ba”
Maama takarasa maganar tareda shigewa ta bar Mummy a gurin.
Mummy ta dawo gida tana cizon ya tsa, tana tunani iri2 a ranta.
Jalila hankalin ta ya ďan kwanta, Husna na debe mata kewa suna hira lokaci zuwa lokaci, sannan duk lokacin da ta keso zata ari waya takira wanda takeso, Mijin Antyn Jalal professor Aliyu Ishaq yana koyar da darasin turanci a saudiyya, be fiye zama ba, yana da tarin Ilimi, gashi mutumin kirki ne, yana da barkwanci da raha, Girmama shin da Jalila da take da yadda yaga tana gudanar da Al’amuranta yasa take burgeshi, yayiwa Jalal murnanr samun yarinya me kwazo da tarbiyya kamar Jalila. Be kara sarewa da lamarin Jalila ba seda Antyn ta bashi labarin irin Abubuwan da Jalila ta dingayi da kokarinta akan rayuwar Jalal, ya zamana Jalila tana sakewa da shi fiye da kowa a gidan, kamar yadda Ake kiransa Abee haka take kiransa, Jalila tana son mu’amala da mutane masu ilimi dazata Amfana dasu, indai Abee ze fito parlour Jalila zata zauna Suyita hira tana masa tambayoyi akan abubuwa da dama, shikansa duk lokacin da be ganta ba ya dinga tambaya tana ina kenan, yana mamakin kaifin hankalin ta da basirarta, gata da ilimin Addini “