ABDUL JALAL PART 2

Yauma na gama dinner, Amma Jalila tanata hira da Abee tana bashi labarin irin fituntunun data dingayi lokacin kuruciya suna ta mata dariya, Hajiya Salma tace
“Nikam Alhaji Aliyu me kayiwa Jalila haka take sakewa da kai hada hira, mu kaman tsoronmu ma takeji”
Jalila tayi murmushi tace “Bahaka bane ba, Jalila Aliyu Imam, shine cikakken sunana, kuma Kafin Babana ya rasu Abee nake ce masa”
Anty tace “Haba shiyasa wannan shakuwa haka, Ashe ya da uba ne”
Abee yace “Eh ya ranku, yata kuma sirikata kuma malamata”
Zare ido Jalila tayi tace “Wace ni, se dai in durkusa a koyamin, Seda safenku” Jalila ta fada tana mikewa tsaye, sukayi Sallama ta tafi dakinta.
Bayan tafiyarta Abee yace “Kuna ganin raba yaran nan yanada wata fa’ida ne? Yana can matar tana nan”
Anty tace “Eh mana, muna so mugane dagaske yana sonta ne kokuwa?”
Abee yayi murmushi yace “Lallai kun manta waye ďan naku ne, shikenan Allah ya tabattar da alkhairi, Amma nayiwa Jalal murna samun yarinyar kirki kamar ta, tanada hankali sosai”
Haka dai suka cigaba da tattaunawa.
Jalalila kamar kullum ta gama wannan wankan turaren, ta shirya a cikin wata doguwar riga, dayake Anty sunyiwa Jalila sayayyar kayan sawa dana kwalliya tana kan wani karamin kujera tana gyara gashin ta.
Husnah ce ta shigo dakin tana murmushi tace
“Maigidanki yana hanya, broz Jalal zezo ba sanarwa ba komai, kuma nasan badan ke ba bazamu ganshi ba, tashi muje ayi masa girki, Anyiwa me kitso waya tana hanya, ki taso muje”
Hade rai Jalila tayi tace “ba wani girki da zanyi, kuma ni ku kyalemin kaina a haka”
Husnah tace
“Haba Sister meyasa haka ne?” (nikam nace baki san halin Jalila da taurin kai ba)
Jalila tace “wai meye Amfanin inta bawa kaina wahala akan wanda be damu dani ba? Watana daya da kwana Goma a gidan nan ko ta waya baya kira balle yaji ya nake, seni zan ta faman wahala akansa”
Ajiyar Zuciya Husnah tayi tace
“Kina da gaskiya Jalila Amma hakurin dazakiyi yanzu baze kai na baya ba, ki bari ki kama shi a hannu, daga nan seki rama, taso muje su Mummy suna parlour”
Jalila bata da zabi sena ta mike tabi bayan Husnah, suna zuwa parlour Hajiya Salma tace
“Yawwa Jalila, Jalal yayi waya yakusa isowa maiduguri, me kitso tana hanya, dama lallanki jiya akayi shi, in an gama kitson kafin ya karaso ayi masa girkin.
Jalila ta samu guri ta zauna ba tareda tace komai ba, Husnah ta zauna a kusa da ita tana mata magana kasa2
“please sister idan yazo karki hade masa rai haka, karki biye masa dan Allah, ki bawa mara ďa kunya”
Ita dai Jalila jinsu kawai take.
Tunda Daddy ya tafi be kara dawowa Nigeria ba, Mummy tarasa me yake mata daďi, in dai Jalal ya zauna da yarinyar nan to zata kwace mata shine gaba daya, dan tun kafin ya aureta ma yana sonta tunda yanajin maganar ta, tarasa ta inda zata bullowa lamarin, gashi a yanzu tasan bata isa taje maiduguri tayi musu tijara ba.
Kafin Jalal ya karaso har angama yiwa Jalila kitso, kitso akayi mata kanana sosai, gashi hannunta ya sha lalle, duk inda ta gifta kamshi take, ga fatarta ta kara kyau se sheki take.
Anty tace ” Jalila me yakamata ki girkawa Jalal ne? Mara nauyi sosai tunda naga alamar shigowar dare zeyi”
Dan zumbura baki Jalila tayi tace “befiye cin Abinci da daddare ba yafi shan tea ko fruit, wani lokacin koya ci Abinci seya sha tea da daddare” ta fada tana dan tura baki cikin ko in kula
Boye dairiyar su sukayi, banda Husna da seda ta dara, tace “Ya akayi kika san haka?”
“Nike musu girki shida Yaya Jawwad a gida” tabata amsa
Anty tace “Ke Husnah ina ruwanki ne? Jalila ki dafa masa abunda kika ga ya dace kawai”
Jinjina kai tayi ta tafi ďakinta.
.
Seda ta tafi sukayi dariya, Hajiya Salma tace “Kai lamarin yaran nan sesu, ni ban san wanda yafi wani taurin kai a cikin su ba, ana so ana kaiwa kasuwa”
Anty tace “Jalal yafita taurin kai, bafa yanzu yafara sonta ba shi, Jalal ya dade yana sonta, nasan komai, Dan yaga ya samu yanzu shine yake basarwa kaman be damu da ita ba”
Hajiya Salma tace
“Aike ta hannun damansa ce kinsan komai akansa, Allah ya daidaita tsakani”
Suka Amsa da Ameen
Lokacin sallar magariba Jalal ya iso gidan, ya sha tafiya dan a mota yazo ya gaji sosai, Jalila bata san ya karaso ba, har bayan sallar isha’i tana palourn Abee yana mata bayani akan wani littafi da yake son wallafawa, Husnah tana gefe tana dan tsoma musu baki lokaci zuwa lokaci, zaman da Jalila tayi da su tafara gane yarensu kadan2, kaman gaisuwa da yaren.
Suna hira kai kace ‘ya da ubane, Anty ta shigo palourn tace
“Jalila kina nan, tun dazu Jalal ya iso fa, nazata kina can kina shiryawa ne, kije ki shirya ki kaimasa Abincin”
Jalila ta dan langabe kai tana kallon Anty. A ranta tace “Sekace wani mijin kirki ko wadda zata biki anata in shirya, bayan nasan ko kallo ban isheshi ba”
Abee ya kalli Anty yace “Madam jeki zamuyi magana da’ yar auta ta”
“to shikenan nidai ayi Sauri, in ba sokuke yayi zuciya ba ya tafi” ta fada tana shirin barin palourn tareda yin murmushi, Ameera tana zaune bata fita ba.
Abee yace
“Jalila tambayar ki zanyi, ki gayamin tsakani da Allah, in dai kin baban dani ki gayamin kina kuwa son Jalal?”
Taji ya mata tambayar ba tareda ta shirya jin hakan ba.
Hade fuska ta danyi tace “Ni dai ban sani ba ko ina sonshi, shima fa baya sona” ta karasa maganar kaman tana shagwaba
Fuskarta ya kalla, Akwai alamar kuruciya sosai a tareda ita, yarinya ce me tunani irin na manya, Amm lokuta da dama kuruciya tana dawainiya da ita.
Yace “Shikenan daughter Allah ya daidaita ku, ki cigaba da hakuri zaki fara sonsa, Mijin kine yanzu, ki manta da halinsa kinemi Aljannar ki, kuma insha Allah komai ze wuce”
Jalila tace “to Abee nagode” harzata fita Husnah tace “Jirani muje in miki kwalliya, nasan idan na kyaleki ba zakiyi ba”
Ta tasa Jalila a gaba zuwa ďaki, ta ďakko mata wani material baki da adon jan flowers, riga da skirt ta mikawa Jalila ta karba tana zumbura baki ta saka, tayi kyau sosai, Husnah ta bata turaruka ta shafa, kamshi dai kam ya riga yagama kama jikin Jalila a gidan nan, Husnah tace
“bari in miki kwalliya”
“ni ba wata kwalliya daza’a yimin”
“Jalila ya hakane? To sa kwalli da jan baki mana”
Jalila ta saka kwalli se jan baki Ja, tasaka kwalli, tayi kyau sosai, Husnah ta bata karamin gyale Ja akanta, Jalila ta kalli kanta a mudubi, kayan nan sun kamata sosai ta kalli Husnah tace “Nikam gyalen nan yayi min karami gaskiya, ki bari in saka babba”
“Haba Jalila, gurin mijinki zaki fa, Mijinki ne ba wani ba, in kuma kinki in barki da su Mummy”
Husnah tasata gaba zuwa Kitchen ta shirya mata kayan Abincin a tray ta rakata har kofar palourn da Jalal yake tace
“please Jalila don’t mess up, karki bani kunya dan Allah”
Jalila ba tace komai ba ta shiga gabanta se faduwa yake yi, Sallama tayi sannan ta shiga, bata tabaccin ya amsa sallamar nan tata. da farko dakin kamshin turarensa yakeyi, Jalila na shigowa kuwa temperature dakin ta canza zuwa kamshin turaren jikinta, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, kanan kayane a jikinsa amma yayi kyau sosai sumarsa se kyalli take, duk ya dena saka wannan kalar dayake wa gashinsa, ya dora kafarsa akan center table, ko a ina zata ajiye tray din oho, ta gefen ido ya dan saci kallonta, tana zuwa bata kula shi ba ta ajiye tray din a kasa, ta juya zataje ta zauna hakan ya bashi damar kare mata kallo, tubarkallah she has a very beautiful heart and body structure, Jalila tana da kyau ga kyakywan surar jiki, ga zuciyarta me matukar tausayi, matsalarta taurin kai da Izza wani lokacin.
Taje ta nemi guri ta zauna a kujerar da take kallonsa ta dora kafa daya kan daya tana kada kafa tareda dauke kanta gefe tana wasa da yatsun hannunta.
Jalal a ransa yace ‘Tsabar wulakanci ko ta gaisheni kota ce min ya hanya ba ruwan ta dani, hakan na nufin dagaske bata sona ne? Ko kuma tsabar rigima da taurin kaine? ” Jalal ya gaza gano amsoshin tambayoyin sa, to bata kulashi da sannu da zuwa ba ma balle yasa ran zata zuba masa Abincin.
Kallon ta ya kumayi, kayanta cif jikinta ga mayafin iyakarsa wuyanta, hanun nan yayi kyau da lalle, kanta ba dan kwali dan haka yana iya ganin tsagar kanan kitso dake kanta.