ABDUL JALAL PART 2

Idan lissafinta dai2 ne kimanin watanni shida bata ganshi ba ko a waya baya kiranta, dama ina ta kai matsayin da Jalal ze aje lambarta balle ya kirata.
Jalal yace “Daddy in aka siyi gidan se a sai furnitures ma in saka, kayan kitchen ban san kansu ba maybe su Anty sa saimata, kokuma muje da ita ta siya”
Wannan statement din data ji yafi kowanne bata mata rai, su Jalal basu san ta shigo ba, dan sun bawa kofar baya, nan Take ta shakunu ta karasa shigowa dakin fuskarta babu walwala ta zo ta tsaya.
Jalal na ganinta ya maze ya jingina da jikin kujera ya dora kafa daya kan daya
Ta kalli Jalal tace
“Sannu mara mutunci wanda be san ciwon kansa ba, Jalal saboda ba ka maidani komai ba tsawon watanni shida ban saka a idona ba, kuma saboda kai ba dan mutunci bane har a hada kai ai maka Aire ba tareda izinina ba, saboda munafunci baka tuntubeni ba tunda akayi Auren nan ka hada kai da dangin ubanka kayi tafiyarka inda ta zaba maka, se yau ka dawo kana zaka saimata gida da furnitures, kudin na ubanta ne? Ko shi ya tara maka? Wallahi Jalal se an kashe Auren nan, ban yadda ka zauna da yarinyar nan ba, seka saketa kuma seka baro wannan tsinan nan aikin data samo maka a lagosa, tunda ba ita ta haifamin kai ba”
cikin masifa Mummy take wannan hakilon Masifar, har Daddy ya fusata zeyi magana Jalal yace
“No Daddy yi hakuri, ban sanka da fada ba, kayi shiru kawai, bari zanje in dawo” Jalal ya mike ze fita, Mummy ta kuma fusata tace
“Nizaka mayar ‘yar Iska ina maka magana, Wallahi Jalal in baka saki yarinyar nan ba sena maka baki” cak Jalal ya tsaya ya waigo yana kallonta.
Daddy dafe kai yayi, dan shi a rayuwarsa sam baya son tashin hankali.
Jalal yazo gaban Mummy ya kalleta yace
“Mummy idan kikamin baki akan na wasu zaki ďora, inkin min baki baze dameni ba, tunda wanda yake dawainiya dani be ishekiba, baki da wata cikakkiyar hujja na kin Aure na, bazan saki Jalila ba saboda ina sonta, kema soyayya ce tasaki zama da mahaifina, nima na Auri wadda na rayu da sonta, baze yuwu amin Auren dole ba, tunda kema bashi aka miki ba”
“Jalal ni kake gayawa haka?”
Kai tsaye yace
“Yau na fara gaya miki gaskiya? Bazan Auri macen da bana so ba saboda san zuciyarki, da in saki mata ta gara kimin bakin, dama can a lalace nake, in kika min baki kinga dorawa zanyi”
Yana gama maganar ya fice.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji un, nashiga uku, dan dana haifa ya tsaya a gabana yana gaya min wannan maganganun, Habib Jalal ua zabi mace akaina da na haifeshi, ban taba zaton haka ba, tunanina Jalal shaye2 kawai yake, yaushe Jalal ya fara son Jalila da har yake gayamin wannan maganar akanta, tun yanzu, wallahi na tsani yarinyar nan”
Daddy yace “Khadija be kamata kiyi wannan maganar ba, bari in tuna miki wani abu, Soyayyar da nake miki tasa na zauna dake tsawon shekaru, na fifita ki fiye da Ahalina, kika rabani da kowa nawa, Ashe ba dadi, na fuskanci Soyayya bazata yiwa Jalal da wasa ba, dan haka ki shirya sa hannu ki karbi irin abunda kika aikata kema”
Mummy cigaba da rusa kuka tayi tama fadin
“Wallahi baze yuwu ba, ni na haifi dana ba’a isa amin iko da shiba, babu wadda ta isa ta juyamin yaro, nasan wannan makircin Salma ne, zata ďau fansa a kan ďana, tana tunanin zata mallake min ďa saboda wannan banzan shirin nata? Wallahi bata isa ba” tuni Idon Mummy yayi jawur tana kuka tana masifa, Daddy ba shi da zabin da ya wuce yabar mata ďakin, dukda yadda yakejin kukan nata a zuciyarsa, Amma wannan faďan rashin gaskiyane kawai take yi.
Ilham kuwa tana kitchen tana hada abunda zata ci, sama bata san Jalal ya shigo part din ba, tana daga kai ta window taga shigar Jalal part dinsa, gabanta ne ya fadi, ya wani kara kiba, wani tunani ne yazo mata, hakan yasa ta fito da sauri ta tafi part din nasa, tana zuwa ta tarar baya palourn dan haka kai tsaye itama ta bishi bedroom din nasa, Amma tana zuwa ta tarar har ya shiga toilet, gefen gadonsa ta samu ta zauna ba tare da fargabar komai ba, tayi a kalla mintuna Ashirin sannan ya fito sanye da gajeren wando jikinsa babu riga se karamin towel yana goge ruwan jikinsa, Sam Jalal be kula da Ilham ba, yayinda Ilham ta daskare a zaune tana karewa surar Jikin Jalal kallo,
Gaskiya Jalal ya kai a so shi koba dan dukiyar sa ba, ko ina na jikinsa kwance yake da gashi tun daga kansa har kafafunsa, dogone jikin sa a murde yake, dama ga jikinsa yana cin karfe, kallo daya zaka masa kasan namiji ne me matukar kwarjini, yana ďaga kai yayi ido hudu da Ilham zaune akan gadonsa, a fusace yace “Ke meye haka? Uban me yakawo ki dakina a daren nan? Ta shi kifita ki barmin daki”
Mikewa Ilham tayi ta tako gaban sa ta tsaya tana kuma kare masa kallo, “Jalal dagaske kayi Aure ko?”
“Tambayata ma kike? Ban sani ba, fita ki barmin daki”
Towel din hannunsa ta karba, ta ajiye ta zuba masa ido, Hawaye ne ya fara bin idonta
“Jalal namaka son da ban taba yiwa wani namiji makamancin sa ba, Jalal why? Ina sonka Jalal, meyasa zaka Auri wata bani ba, Wallahi ina sonka, Jalal ka shmmace ni, ka Auri yarinyar da nafi tsana a rayuwata, Haba Jalal meyasa kamin hakan?”
“kina son Jalal ko kina son cutar da shi? Kina sona nikuma na rayu da son yarinyar da kika fi tsana, saboda a duniya a yanzu babu wanda ya gwada min so kamar yadda tayi, I love Jalila with all my heart, ba abunda bazan sadaukar akanta ba, i am sorry, kema Allah yabaki me sonki”
Wani kululun takaici ne ya tokare kirjin Ilham, Amma ta maze, hannu ta mika kirjin Jalal zata shafa kirjinsa amma ya rike hannunta, ya girgiza mata kai,
Ya dan lumshe ido ya bude yace
“Abunda yasa nake kara Son Jalila kenan, ba ruwanta da abunda ba nata ba, karki tsallake iyakar ki, karki taba mata miji kin san halin ta dai base na gaya miki ba, Abunda kike hari tsawon lokaci ya zama nata, a gaskiya ta miki ba dadi, ta rusa shirinki gaba ďay” ya karasa maganar yana ďanyin murmushin mugunta, sekuma ya haďe rai yace
“malama get out from my room”
Ilham tace “Amma Jalal”
“ki fitar min daga ďaki malama, ko ba kya banbance abunda ya dace da wanda be dace ba? Kifita bana son ganinki” Jalal ya katseta
“Yaya Jalal…”
“kifita nace ko in miki Illa, natsaneki bama son ganinki, ki fita ki bar min daki ko in kakkarya ki”
Yadda yakoma yana maganar a fusace ya sa Ilham ta fita da sauri ta bar dakin. Wani dogon tsaki Jalal ya ja ya saka doguwar Jallabiya ya kwanta.
Ilham kwana tayi tana juyi ta kasa bacci, Jalal da ba ruwansa da mata yaushe ya fara Soyayya? Har yake gaya mata yana son Jalila fiye da komai, yadda taga rana haka taga dare zuciyarta kamar zata fito,tana karajin tsanar Jalila a ranta.
Kamar yadda suka tsara, Jalal da Daddy sukaje suka sai gida a tarauni, gidan yayi matukar kyau da tsaruwa, yanada girma sosai gidan, palour biyu, bedroom uku kowanne da toilet se kitchen biyi da store da katuwar harabar gida.
Daddy ya samu Abba akan, an sai gidan dasu Jalal zasu zauna, Jalal ze sai furnitures, Abba yace be yadda ba shi zewa Jalila kayan daki, Jalal ba dan yaso ba ya hakura, Abba da Maama sukaje suka ga gidan sun yaba gidan sosai, Abba seda ya cikawa Jalila ko ina da kaya, gidan ta yayi kyau ya tsaru matuka.
Sam Jalila bata san abunda ake ba, ita dai taga su Hajiya Salma sunata kara shiryata, Hajiya Salma taje ta samu Jalila a daki tace “Jalila ki ware gashinki, me kitso zatazo ayi miki kunshi da kitso, ranar Asabar zaki tare”
Zare ido Jalila tayi tace “Wai Asabar me zuwa?”
“Eh mana, mijinki yace; se kin tare ya gaji da wannan sintirin”
Shiru Jalila tayi ta sunkuyar da kai, Hajiya Salma tace