KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Maganar da yazeed yayi yasa ta dawo daya tunanin da take.
Ke?kin iya up and down?
Harara ta banka mai yasin bazanyi Ba

Kallonta yayi da mamaki da kuma takaici Wai ita bakinta baya mutuwa ne?shi tunda yake banda zakiyya babu mai iya kallon idonta ma tamasa magana balle tsiwa ko zakiyya ma tasan lokacin da take haukanta. hmm zaiyi maganin yarinyarnan da alamu kanta yana rawa.

Hannu yasa ya dalle Bakin Wanda yayi sanadiyar fitar jini kamin yace
Mike ki fara up and down!
Jikinta na rawa ta fara kwanciya yayi ya rufe idonsa fuskarsa na kallon sama.

Sanda tayi kusan na Minti Biyar alokacin ta gama had a gumi sannan ta dubeshi tace oga sir kayi min rai
Wallahi bani kara maka rashin kunya jin shiru ba’a amsa mata Ba yasa ta tsaya da punishment din ta sansado ta leka fiskarsa ganin idonsa a rufe yasa tace
Kutma lallai ma mutuminnan Dan rainin hankali ne.
wato ga inji ko?inyita aiki shi yana bacci,wallahi Allah ya isa na.

Sanda takeyi harta iso Bakin kofa zata fita taji yace
Da izinin zaki aikata hakan?kuma Waye Dan rainin hankalin?

Juyowa tayi a zabure tana zare ido dama Ba bacci yake Ba?
Wayyo Allah bakinta yaja mata.
Zama yayi yace dawo ki zauna.
A hankali take takowa Kamar kazar da kawai ya fashewa a ciki harta tsuguna

Gabansa ya Muna mata ta matso tana zare idanu harta rame Kamar Ba ita ba.
Yazeed yace dago kanki dagowa tayi amma idonta a kasa.
Yace Nayi kama da sa’anki? Ta girgiza kai.
Yace kinada matsalar kwakwalwa ne?ta sake girgiza kai. Tsawo ya saka mata yace use your fucking mouth !

Itadai bata gane ba saboda accent dinsa ya mata tsauri amma sai tayi shahada wajen Cewa kayi hakuri.

Yace kintaba ziyartar gidan mahaukata ne?domin kinyi kama dasu

A ranta tace kutma wallahi ni banyi kama da mahaukata ba Saide kai ne mahaukacin.

Kaine mahaukacin shi ya bayyana azahiri wadda bata masan ya fito ba
A fusace ya mike ya yarfe ta da mari yace nine mahaukacin ?tana girgiza kai tace tace a ah dan Allah na rokeka kayi hakuri subutan baki ne bazan kara Ba. Ball yayi da ita ya fita tare da sawa kofar dakin lock yana ma fadin zan nuna miki hauka yar budurwa!

Koda ya fita waje idonshi yayi ja lukman ya gani yace ya kawo masa igiya

Cike da mamanki lukman din ya dauko igiyar yana nazarin me ogan nashi zaiyi da igiya? Dan shi baiga alamun saniya a gidan Ba lol.

Saniya minal za’a daure

Jin shiru bai dawo Ba yasa ya kwada masa kira domin ya tsani waste of time.

Da gudu yazo a kasa da da’ki’ka 2 domin Dan tazarar dake tsakanin  side dinsu da kuma main one

Miko masa igiyar yayi yana Cewa oga yaushe za’a mayarda yarinyar?
Yazeed yace my friend, get out of my side!

Har lukman ya fara tafiya yazeed yace zonan.
Dawowa yayi yace masa ya batun Jamal din Ba nace a dauko shi Ba? Lukman yace su bala ne suka tafi Daukoshi.

Juyawa yazeed din yayi ya tafi Ba tare da ya tanka masa Ba.
Shiga dakinsa yayi ya samu minal Inda ya barta tayi jugum

Ba Komai ke damunta Ba illa wani bahagon yunwa domin tana fashin sallah,Kamar dai yadda kuka sani minal muguwar acici ce.

Mu hadu a next chapter domin jin yadda zata kaya tsakanin minal da yazeed.

Thank you!

18 June 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:51 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹By miss untichlobanty🌹

CHAPTER 14

Tsugunawa yayi a gabanta yace kawo hannuki !
Kallonsa take a ranta tana Cewa dama oga sir Dan iska ne?

Dama yawanci sojojin nan mazinata ne ga shan giya da sigari
Dan iska me zibin samudawa

Tafadi hakan a zuciyarta domin it a atunaninta wani abin zaiyi da hannunta domin tun batakai haka Ba inna ke ce mata duk namijin da ya tabata bada sannin innar Ba to Dan iska ne amma banda baba da ya abubakar

Tsawa ya daka mata aiko ta miko hannun nata. Igiyan ya fara shirin kulla mata ai atake ta fara kuka da hawaye

Kallon ta yayi kamin yayi murmushin gefen baki yace:
Ashe de baki cika jarumar Ba
ai nadauka taurin kanki bazai bari kiyi kuka Ba.

Ajiye igiyan yayi a wajan ya fita daga dakin ya jirkita pin din ya rufe.

Kuka ta fashe dashi tana burburwa a kasa har ciwon dake hannunta ya fara jini bata saniba

Wani sautin da cikinta ya bayar shi ya tuna mata da cewar bataci abinci domin sau biyar takecin abinci banda kananun kwamulashe da take yi

Tunawa tayi da wani lokaci

Flash back

Inna Wai haryanzu baki gama miyar bane nifa kinsan bama er mutunci da yunwa

Inna dake kitchen tace Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
kinga ni ki rabu dani kinfiso Nayi irin wannan miyan naku na ‘ya’yan yanxu

Amina ce tafara waka tana buga gwannon hannunta da

Iyya yunwa batada kara,iya yunwa ba’a mata lahaula,iya yunwa batada Sabo wayyo iya yunwa na iya karwa Iya yun……….

Muryan inna ta jiyo wadda ta leko tana kallon ikon Allah

ta Ce to ai bazansan kinajin yunwa Ba sai kin fara bin makwabta

Turo baki tayi tana guna guni ta mimmike kafa a kofar daki tace
inna shiyasa nace kiban na dafa kika ki ki Duba fa yadda dare tayi

Inna tace wai karfe biyar kike so na dinga gama abincin dare ne ?

Kara turo baki Amina tayi tace inna to ai………

Sallaman da baba ya Watso shi ya sa ta antayo da guru tana Cewa baba sannu da zuwa

Yayinda take turo baki ta huhhura hanci
baba yace :
Uwata ya akayine?

Minal tace inna ce had yanxu bata gama abinci Ba gashi yunwa nakeji gashi had dare yayi

Murmusawa baba yayi yace uwata yanzun ne dare yayi?karfe 6:30 ai beyi Ba

kinga dauko mana taburma

Taburman taje daukowa yayinda inna ke Cewa
mallan an shigo kenan,ya aikin?ai wannan sususun bata ma bari min gaisa Ba

Baba yace Alhmdllh ,uwartawa ce Ba tada dama muryarta suka jiyo ta leko ta taga(window) tana Cewa
Allah ya kawo Mani har kunnena gulmata akeyi ko?

Dariya suka fashe dashi yayinda baba yace ja’irar yarinya kasa kasa

Inna tace malam bara in kawo maka ruwa

Sai a lokacin Amina ta fito ta shimfida tabarmar yayinda baba ke Cewa
ina Kanwar taki deeje ko duk gajiyar makarantan ne?

Tace Ba wata gajiya baba tana can de tana abinda aka saba baccin asara

Baba ya Dan dara yace gaba de baccin asara ai tana kokari kayi kusan wata hudu a makarantar kwana (boarding) baka ganin iyayenka ga wahalar labour ai dole tayi bacci

Labulen da aka banko ne yasa suka dago dukkansu suka kalli kofar

Deejeh ce ta fito tana watsa hamma Amina ta dauje bakin tace ke dallah rufe mana shegen bakin naki me zubin sokawe

Dije tace a ah salga ne Ba sok…………..

Ai bata karashe Ba taji bugu.
Babane yace uhm yarannan bara kuga, ya mike ya tafi waje domin yayi alwala yaje masalti ya samu falalar jiran liman domin yasan idan suka fara Toh sai Allah.

Kayi magana Kamar kana zugasu kayi duka su dau gaban duniya su daurawa juna

Inna da ta dawo da ruwanta a hannu ta taradda tabargazan dake faruwa nan ta saita ma kowanne notin kansa

Nan suka ballawa kuna harara wadda yake nuni da mun daura gaba.

Innako takaici ya mata yawa

Amina akwai gajan hakuri,saurin hannu da tsiwa

itako khadijah fitsara ta mata kaka tuku a tsuliya

Bayan baba ya dawo daga masallati nan ya dauko ledan daya shigo dashi dazu yace

Uwata d’azu dazan dawo isubu mai gashi yaban tsirannen yace na kawo miki. Minal tace kace Allah ? Tana mai jin dadi.
Inna ce ta shigo da farantin tuwo malmala biyarne a ciki ta ajiye.

Washe hakwara Amina tayi tace kai inna kin kyauta wallahi Dan Nasan bazan iya kara minti 30 me kyau Ba yunwa zata kar ni

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button