KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Jakarsu suka dauka simi simi suka tari Napep dama mamar murtalan ce ta aikesu
Minal ko tahiyatta tayi tana Cewa har Dan shaye shaye zai iya bada shawarar arzikine?yo jakar mafa Ba wani Nauyi gareta ba kawai de tsabar shaye shayensu har garkuwar jikinsu ta zamo batada karfi. Aikin banza!
Gidansu zaliha ta fada ta labarta mata abinda ta riska bayan ta koma gida nanko ta dinga tsokanarta sunata raha abinsu.
BAYAN SATI DAYA
Mom tayi magana da uncles din yazeed Kamar yadda tayi alkawari kuma sun sanarda ita zasuzo
Shirye Shirye ake agidansu minal makota da abokan arziki hardasu aunty fauxy da iya maman zaliha sun shishshigo ana ta aikace aikace domin taran baki
Minal kam Cewa akayi su Shirya itada zally su tafi gidansu zally
Suna cikin daki zaliha ke Cewa ke kawalliya na kasa yarda wai zakiyi aure
Minal ta daga hannu ta zuba mata duka acinya tare da Cewa da fatan kin fahimci Ba mafarki kike…..
Maganarce ta Koma sanda zaliha ta yarfa mata tafi abaya tare da fadin saura daya.
Bankarewa minal tayi saboda dukan ya shigeta kuma bazata akamata
Nan fa suka fara duke duke zaliha ce tayi surrender tace
Ke shegiya ni matsa hanunki saikace wuka
Minal tace zama Kiyi bayani
Suna cikin haka sukaji hayaniya ya karu
Lekowa sukayi sai suka ga luba Maman bilkisu tsaye tana fadin:Kamar da gaske ai dama wannan yar taku kazama ,ballagaza babu Wanda zai kalli ko Inda take balle ya shinshinata,yanxu haka Nasan sadakanta za’a bayar,wallahi kowaye ya karba ancucesa
Aunty fauziyya ne tace ke dakata inhar kinsan……
Minal ne tayi carab yayinda suke fitowa adaki rike da hijab dinsu tana mai Cewa “ko Ba Komai ai nafi su o’o tunda dai ankarbi sadakan nawa kuma zani da mutunci na wasu da ko a sadakan bazasu sadaku Ba fah?sai yawo a gari an zama shaddar kasuwa kowa zai iya tsuguna duwaunsa akai “
Daganan ta fizgo hannun zaliha sukayi waje yayin da ta balla mata harara
Sauran matanne da basufi goma Ba sukayi mata chaaa aka kowa da irin nasa comments din daganan akayi waje da ita
Bayan minti talatin saiga Yaro yayi sallama Wai inji baban kowa
Akawo abincin baki parlourn zaurensu.
Nan inna tace ya nemo yara biyu sai sukai. Haka ko akayi bayan sun gama cin abinci tare da santi suka sha zobo da kunun aya sannan aka tsaida aure nan da wata 3
Uncles din yazeed sunji dadi sosai da irin karamcin da akayi musu hakan yasa sukasan yazeed yayi dace domin lokacin da sukaje gidan su zakiyya ruwa da lemo kawai aka basu ko snacks basu samuba balle abinci gaisuwan ma sama sama .
Mom suka kira suka fada mata abinda yadda akayi aiko taji dadi daganan aka dinga Sanya alkhairi ana watsewa.
Minal sai 5pm ta dawo aka fada mata yadda akayi bakinta har kunne ya abubakar nata tsokananta.
AT NIGHT
mom,Jamal,yazeed and zakiyya zaune a parlour zakiyya na latsa waya while YAZEED and Jamal are watching football, mom kuma na rubuce rubuce
Mom tace yazeed,kowa juyowa yayi ya kalleta tace akwai aabinda nakeson in fada maka……
Dan! Dan!! Dan!!
Cabdi anxo gurin. Me mom zata Fadawa YAZEED kuma yaya zaiyi ko ince zasuyi reacting?follow me to find out….
Don’t forget to share and comment
Your one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty💕
8 SEPTEMBER, 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINAL ðŸ†ðŸ†
🌹by @mzz_untichlobanty🌹
CHAPTER 23
…..inaso inje ziyaran family na ne maybe nanda wata 4 kuma zanyi wata 1
Yazeed yace Allah ya kaimu nima next week zan tafi wani mission kuma zanyi Kamar 2-above month kamin na dawo
Mom tace toh Allah ya kaimu. Yazeed yace tare zaki tafi da Jamal kenan? mom tace eh,yace that’s good daganan kowa ya kama harkansa
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹
Akwana atashi yaune yazeed zai tafi mission dinshi zakiyya tace baby inajin zan Komai aiki tunda kaga tafiya zakayi
Yazeed perfume ya fesa kamin ya tako Inda take ya zauna ya rike hannunta yace Ba Komai u can resume sannan ya danyi pecking lips dinta
Hararansa tayi tace kaga matsalarka kenan kai da an zauna ana magana sai ka fara canjawa jiya abu daya akayita yi amma baka gaji ba ni matsa Dan Allah ta fadi hakan tana dan turesa
Yace haba mine na bankwana fa zamuyi 2 months fa zanyi babu ke
Tace ni rabu dani bacci nakeji
Haka yazeed ya gama nacinsa amma zakiyya ta rufe idonta tace Sam
Dole ya hakura ya tafi tace Allah ya tura keya
Sannan ta kara lafewa acikin bargo ko wankan tsarki batayi ba sai bacci after 5 min ta zaburo a guje ta bude wani drawer ta dauko tabulet ta watsa kamin ta koma ta kwanta
ðŸ€yazeed kuwa direct dakin mom ya tafi ya sameta har lokacin tana kan sallayanta tana azkar Dan lokacin to 7 ne
Assalamu alaiki ya Ummi
Wa’alaika Assalam son,kaif asbahata ?
Asbahatu bikhairin,just came to to say bye to u
Take care of ur self u know that I will miss u ryt?
Yes mom I do
Matsowa kusa da ita yayi yayi hugging dinta tare da peck a goshi miyar masa tayi ya dago sai taga idonshi ya ciko da kwalla tace son when did u became a cry cry baby ne?
Murmushi yayi yace kawai zanyi missing dinki ne
Kumatunshi taja tace karka damu kaji ?just concentrate on ur mission
Okay kawai yace mata sannan ya fita
Jamal ne ya rakashi har airport akayi clearing dinsa jirginsu ya tashi by 8am on the dot.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹
Akwana atashi yau yazeed zai dawo kuma saura 3 days adaura aurenshi da minal
Mom ta hadowa minal lefe na gani na fada tayi order from different countries; atamfofi,laces,material,jewellery,takalma,perfumes kayan kwalliya,inner wears etc
Abangaren su minal Komai ya kankama domin mom tace musu karsuyi kayan daki dakyar suka yarda amma dukda haka sukace zasuyi mata gara da show glass mom tace Ba matsala.
Minal ko gyara takesha sosai ta kara kyau sosai mom ma ta loda musu kudi tace idan Suna bukatan karu suyi magana
Dakyar tukun suka karba tare da yarjeniyan mom bazata kara kashe musu kudi Ba daga wannan.
ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€
Motoci ne Jere suka danno kai cikin jidmar mansion kamin suka tsaya yazeed ne ya fito ya kara kyau sosai yayi fari jikinnan sumulsumul
Ciki ya Shiga yayinda aka Parker motocin mom ne tayi masa sannu da zuwa tare da yaushe rabo kamin tace yaje yayi wanka sannan yaci abinci
Around 9 O’Clock Suna zaune a parlour mom tace yazeed yace yes mom ?
Tace akwai abinda nakesan fadama da fatan bazà ka watsamin kasa a ido Ba
Yace mom kawai ki fadi magarnarki
Tace jibi za’a kawo Amarya gidannan
Amarya kuma?Jamal ne zaiyi aure?
Ah ah
To amaryan Waye?
Naka ne
Nawa?!mom kin manta I already married?
Nope,kasan Cewa zakiyya zabinka ne,kuma duk abinda kakeso nima inaso to shiyasa na yarda ka aureta Toh yanxu sai ka auri Wanda nakeso ko?
Amma mom kinsan banida burin kara aure?
Bata rai mom tayi tamike zata tafi yazeed yayi saurin rikota yace indai haka kikeso to na yarda
Murmushi mom tayi Allah ya maka albarka son
Ameen,amma mom wacece ita?
sunanta Amina Idan tazo zaka ganta
Karki damu sweetheart koma wacece ni zan aureta ai farin cikinki shine nawa kuma Ind…….
ME NAKEJI KAMAR MAGANAN AURE ACIKIN GIDANNAN?!
Kwass….kwass zakiyya ta shigo tana wani yatsine tana daga kofar hanci idonnan Kamar zai fado tsabar jaraba.
Zuwa tayi gaban yazeed tace to Baka isa Ba,Wlh yazeed baka isa ba kayi kadan kawai saboda ka kaskantar dani shine zaka wani ce zaka yi aure?ta fadi hakan Kamar zata makuro yazeed din