KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba tareda ya kalleta Ba yace nace miki kimin wanki shine Dan kin rainani ki kamin jika jika ko?

Muryarta na rawa tace wallahi me kyau Nayi kaga hannuna ma ta nuno masa gefen hannunta yadda yayi jaa Kamar ka taba jini  ya fita tsabar yadda ta dirji kayan

Tsaki yaja yace raguwar banza dan kin wanke singlets 3 da boxers 3 Wanda nasa jiya shine zakina wani nokewa Kamar marainiya

Batasan lokacin da tace aide nafi wasu juyowa yayi adan zabure Dan baiyi expecting ta mayar masa da magana Ba
Hannu yasa ya bige bakinta yace zaki tashi kibar gefena ko saina maujeki in canja miki halitta.

Da Sauri tabar dakin tana mai zubda kwalla,lallai tayi kuskuren amincewa da zancen auren Ba tareda ta saurari ko Waye su baba zasu aura mata ba sai a yanzu ne take kara ganin wautarta

Dakinta ta koma ta tsaya agaban madubi tana kallon yadda tayi kyau dukda kuwa ko petroleum jelly bata shafa Ba balle powder amma idanunta sundan fada ciki sannan ta zama kalar tausayi babu walwala a tattare da ita.

Haka rayuwa taci gaba wa minal yanxu har tayi wata 3 a gidan captain  tanayin aikinta Kamar kullum once in a while sukan hadu da zakiyya inta gama banbaminta minal kawai ce mata take Allah ya baki hakuri sannan ta wuce itako zakiyya babu abinda ta tsana Kamar tayima rashin mutunci ka nuna bai dameka Ba Dan haka sai tayita kumfan baki tana cika tana batsewa

Minal ko gani takeyi Kamar zakiyya taci noti kuma tana bukatan Sabo hakan yasa bata tanka mata har tayi ta gama

Aunty fauzy ta kawo mata ziyara har sai biyu Inda take kara jaddada mata girman aure da kuma yadda zata zauna da abokiyar zamanta lafiya. Ita dai minal kunne kawai ta kasa Cewa komi aranta ko tana Cewa cab ai bakisan halin abokiyar zaman tawa da mijinta ba da ko zancenta bazakiso muyi ba.

Yau saura 3 days auren zaliha Inda gobe ne za’ayi kamu
Minal nason tambayar captain izini tun last 2 weeks amma tsoro take yau kam shahada tayi ta turo kofar dakin da yar sallama a bakinta aiko abinda ta gani shi ya Daga mata hankali captain ne ya fito Daga wanka Daga shi sai gajeren wando fari kal da bathrobe Wanda ya barshi haka ba tare da ya daure igiyan ba wanda yayi sanadiyyar Nuna dukkan ilahirin faffadar kirjinsa mai dauke da gashi kwance luf luf Wanda keda laushi hamar gashin kan jariri.

Rikicewa tayi a maimakon ta fita saita fada bandaki aiko ta sule sai a kasa Inda ta bige makunin shower sannan ta gurde kafanta salati ta sake tare da sakin wata gigitacciyar kara hawaye kuwa tuni sun Dade da fara ture junansu wajen saukowa yiyinda ruwa ya mata sharkab.

Captain da bai San ta shigo dakinba yaji ihunta atake ya nufi bandakin ganinta shame shame a kasa ta jike da ruwa jakab ya sashi Jan tsaki tare da Cewa ke Dan ubanki me ya kawoki cikin bandaki na bayan yau ba ranan wankewa ba?

Kuka kawai take kamin tace Dan Allah ka taimaka mini wayyo kafata tsaki yaja da Kamar zai fita amma yadda take kuka yasa yaga bazai iya barinta ba yasa ya miko mata hannu aiko hannunta ta mika ta rike nasa take sukaji Kamar sun taba wayar wuta ba shiri ya saki hannun ji yayi jijiyarsa ta fara harbawa Wanda yasashi Cewa kaide kayi asara yazeed acikin zuciyarsa

Sake miko mata hannun yayi ya Dagata
Dingishi ta soma har zasu fita yace dakata !me kike nufi?

Kallonsa take alamun Neman Karin bayani yace au dake a haka kike nufin zaki Shiga dakina ki jika mini da ruwa saboda Yan garinku basuda lissafi?
Bata fiska tayi cikin rants tace badai garinmu ba wallahi

Yatsansa yasa ya dalle mata baki yace dani kike tayi saurin girgiza kai alamun a ah hannun yasa zai cire mata hijabin dake jikinta ta rike kyam kiciniya suka fara aiko yazeed ya riko hannunta duka biyu da hannu daya sannan ya zame hijabin da hannun daya yayi Ciro dashi

Kallonta ya farayi Inda idonsa ya tsaya kyam akan cikakkun breast dinta Wanda doguwar Riga jikinta da ta like mata har nipple dinta ana kallo wani yawun jaraba ya hadiya ‘kutt kana ya kalli fiskanta aiko shi take kallo and she caught him staring at her boobs red handed
Waskewa yayi ta hanyar tabe baki sannan yace yanxu dama wadannan tsiyar ake boyewa?uhm aike yarinya bama kida abin boyewa danko tsirara zakiyi yawo bakikai akalleki ba uhm kwaila lamba daya kawai sannan ya fice ya barta a wurin minal ko tabe baki tayi tanacewa jeka dai Nasan borin kunyace kawai kumanima ai jikina tafi karfin mugu sannan ta murkuda baki

After Kamar 1min saiga yazeed ya shigo rike da wata T-shirt dinshi fari kal wulla mata tayi sannan ya fice yana yana mai Cewa yi Sauri kibar Mani daki

Domin alokacin har wani hajijiya yakeji tsabar sha’awa
Dan Rabon da yayi harka sati biyu kenan amma yanagudun abin kunya kuma ai yarinyar gold digger ce so he should be very careful kar mazakutassa takaishi ta baroshi.

Minal ko tsayawa kallon Rigan tayi wai me mutuminnan ke nufine Wai ko bazai bata wando bane?

Jin shiru bata fito ba yasa yace Wai Dan kaniyarki bazaki fita bane kullum kika Shiga bandaki Kamar mai haihuwa

Sauri tayi ta saka rigar tana mai Cewa ko yaushe ya taba ganin sanda nake Shiga bandakin oho mutum sai shegen fi’ili

Iya cinyarta rigar ta tsaya Dan haka ta fito tana jajjan rigar domin rufe jikinta
Aiko yazeed na ganinta sanda yaji numfashinsa yadanyi seizing
Kana ya dawo
Ganin yadda takeyi da fiska ya bashi dariya amma taci mur

Muryarsa Kamar yasha giya yace zonan
Zuwa tayi ta zauna a kasa domin bata manta da abinda ya mata ba sanda ta tsaya masa akai yace me yakawoki dakina ?

In ina ta fara tace dama Ami..niya..ta..ce zata..yi aure shine….nakeson naje

Tabe baki yayi yace naji zaki iya zuwa amma ko gidanku ban yarda kije ba

Kallonsa tayi alamun lafiya kake kuwa ?
Baibi takanta yace zaki iya bar mini daki kuma kitabbata kin kwashe tsummokaranki

Fita tayi tana nazari acewai mutum rabonshi da iyayensa kusan wata 5 amma Dan rashin imani ace bazashi ba ALLAH YA ISA

captain yazeed zaune a bakin  gadonsa yana buga game din chase a laptop dinsa Kiran mom ya Shigo dauka yayi

yace salamu alaiki ya habibaty

Mom tace Ameen wa alaikas salam son yakake?

Yace lafiya kalau mom i missed you amma ke naga baki damu da Babyn ki Ba

Dariya mom tayi tace Dan Allah dubeka wani kato dakai Wai baby na kai Wai bazaka barwa ‘ya’yanka shagwabar bane?

Kwabe fuska yazeed yayi yadda yara keyi inka kwace musu alewa yace ai kowa da matsayinsa nidai Nasan ni Babyn ki ne ya kashe ido Kamar mom na kallonsa

Mom tace Allah ya kawo masu albarka sannan tasa serious tune tace yazeed naji shirufa bawani labari gashi har kunyi kusan wata 5 da yarinyannan kuma kasan dai daya Daga cikin abinda yasa naso maka aurenta kenan tunda naga kaida zakiyya bakuda tsarin haihuwa kusa ni sai mai shirin Haifa ta haifo mini

Hade rai yayi yana yatsine sannan ya tabe baki yace ai mom yarinyan ce tukunna ina Duba natsuwarta da hankalinta sannan inga ta dace ta zama uwar yayana koko?kuma kinga bata gama wani girma dazan daura mata nauyina Ba.

Sakin baki mom tayi jin abinda yazeed din yace

Yazeed kuwa jin tayi shiru yasa yace mom kina jina?

Kamar Wanda aka watsawa ruwan sanyi mom tace d’annan dama duk zaman da kukeyi da yar mutane Ba bata hakkinta kake ba? Kai a haka zaka rike mata biyun yazeed ?kana danne mata hakki?ja’iri shine harda wani Wai bazata iya daukan nauyinka ba sai kace wani abin arziki ka ajiye acikin wandon naka?to bara kaji yarinyar da kake renawan tsab zata daukeka harda guntu Dan jakar uba kawai……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button