KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Yazeed ne ya kalleta yana mai Daga gira alamun yadai?tace uhm dama so nake nace nago….
Yazeed ya datseta ta hangar Cewa in godiya zakiyimun ki barshi dan Ba irinta nakeso Ba tace to irin wanne kakeso yace zan fada miki Ba yanxu Ba. Dan tabe baki tayi sannan tace to Allah ya kiyaye sai kun dawo. Murmushin gefen baki yayi sannan ya gyada kai ya shigewarsa mota sannan suka wuce lukman na fadin wallahi sobon nan yayi yana hajiya dashansa yazeed yace dam inajin haushinka dan wulakanci shine bayan ka shanye naka ka dauki nawa ko?lukman yace afuwan mutumina santi ke dawainiya da ni,tsaki yazeed yaja yana mai kauda Kansa izu.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€
Abangaren ango Sulaiman Kam Sai murmushi take har yashiga dakin mahaifiyarsa cikin shirinsa na daurin aure nasiha tayi masa sannan tasa masa albarka domin kuwa Ba karamin so takeyiwa dan nata Ba cikin yara uku da Allah ya azurtata dashi wato;
Na farko Sulaiman mai shekaru 29, sai abdussalam mai shekaru 25,sai kuma fadeelah wacce take yar auta mai shekaru 17-18 kuma anfi saninta da deela ta zana jarabawarta this year.
Fita yayi ya nufi mota Inda abokansa ke jiransa domin tafiya wajen daurin aure.
Suna cikin tafiya sukayi realising ai birki bayaci nan hankali ya tashi salati suka somayi yayinda motar ke wujiga wujiga dasu akan titi kamin ta karasu da wani gini.
Allah sarki!cikin su Biyar da suka fito 2 ne suka rayu wato Muhammad da Ismail wadda akayi hospital dasu rai ahannun Allah amma ango da mutane biyu take suka cika. INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!
Allah taji kan musulmi.
Abangaren wurin daurin aure kam su ango shiru har 2:16pm.
Cikin gida kuwa mata sun cikashi dam Kamar lokacin bikin minal. Ana cikin shagali Amarya tasha kyau sai murmushi take black beauty akaji mai shela na magana Kamar haka: jama’a salamu alaikum, andaura auren malama zaliha usman da malam lukman shu’aibu akan sadaki naira dubu 80 bisa malam yazeed abdulmajeed umar amatsayin waliyin ango,kuma malam abubakar Yusuf amatsayin waliyin Amarya.
Cak kowa ya tsaya gidan yayi shiru bakajin Komai sai numfashi kamin kuma ya sake kacamewa da surutu masu tambayar Dama Ba Sulaiman zata aura bane ?nayi,Masu zagi da habaici Nayi,masu al’ajabi Nayi mai suma ma tayi nata wato Amarya.
Nan Yan daurin aure suka watse akayi gidansu Sulaiman domin jana’iza.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€
Abinda ya faru kuwa shine ana cikin jiran ango sai……….
Kubiyoni acikin babi na gaba domin jin abinda ya wakana
Shin kuna ganin lukman da zaliha sun dace ? Yaya zaman nasu zai kasance?
Don’t forget to comment and share with your friends.
Thank you.
Miss untichlobanty💕
12 November,2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
🌹by mzz_untichlobanty🌹
CHAPTER 42
Ana cikin jiran ango sai hayani ake ana gaggaisawa da Yan uwa da abokan arziki. Da kaga fuskokin jama’an kasan Cewa cikin farin ciki suke.
Wani matashin saurayi ne ya kutsa mutanen daurin auren sannan ya iso daidai da’iran wakilai da manyan mutane.
Sallama ya musu aka amsa sannan ya tsuguna ya Sanar dasu hatsarin su Sulaiman din.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un suka dinga maimaitawa yazeed ne ya kalli lukman idonsa Adan zare yayinda shima lukman din yazeed din yake kalla.
Lallai Sulaiman ya kasance Dan clique dinsu lokacin da suke secondary wato su uku abokaine saide shi Baya burin zama soja sabanin lukman da yazeed.
Idanun su ne yayi ja musamman yazeed daya tuno yadda minal din keson aminiyarta zaliha. Yaya zasuyi in sukaji wannan labari matsala bibbiyu ga mutuwar Sulaiman ga rashin daurin auren.
Ganin Kamar wajen ya kara hautsinewa yasa suka daina kallon-kallon da suke.
Baban zaliha ne hawan jininsa ya tashi domin yasan yadda diyartasa ke mutuwan son Sulaiman din tabbas yasan akwai kaddara kuma ya zama dole yin tawakkali amma yaya diyartasa zata dauki wannan lamari? Abu daya ne mafita shine in ta samu Wanda zai kula da ita ya kwantar mata da hankali, to amma taya hakan zai kasance ? Da Kamar wuya tunda Ba bawa wani dama zata yi Ba.
Wannan tunanin yasa hawan jininsa tashi lokaci daya.
Bakinsa na rawa yace Dan Allah Idan akwai Wanda yasan in ya aureta zai iya mantar da ita Sulaiman dinta dukda ko bazata mantashiba amma dai hankalinta zai kwanta ya taimaka ya aureta.
Hawaye ne ya silalo a idanunsa yayinda samari suka dagashi suka sakashi acikin mota akayi asubiti dashi.
Yazeed ne ya kalli lukman kallon aboki ka taimaka ka aureta girgiza kansa ya alamun bazai iya Ba sannan yace yazeed kasan Cewa ayush nakeso kuma how sure are you Cewa yarinyar zata aminta dani?
YAZEED yace na sani lukman amma ka Duba halin da mahaifin yarinyarnan ya Shiga Ina ga ita yarinyar kuma?
Shin kana ganin kaf na wajen akwai Wanda ya cancanci ya aureta? Kana ganin akwai Wanda zai iya kwantar mata da hankali? sannan ya Daga mata kafa ta dawo cikin nutsuwarta kamin ya bukaci hakkinsa?
Girgiza kai lukman din yayi ya budi baki zaiyi magana yazeed yayi saurin Cewa Idan maryam( kanwar lukman din) ne acikin wannan yanayin fa?
Ajiyan zuciya ya sauke yace yazeed ni yanzu Idan ma na aureta ina zan ajiyeta ? Yazeed yace karka damu da wannan ka amince kawai lukman yace amma yazeed kana ganin nayiwa ayush adalci kuwa?
Yazeed yace India har tanasonka zata fahimta kuma ai ita dinma zaka aureta sannan Idan itace awannan yanayi ai bazataso aki auranta Ba.
Lukman yace amma….. Yazeed yace Dan Allah. Ajiyan zuciya lukman din ya kuma saukewa sannan yace shikenan na yarda.
Murmushi yazeed yadan masa sannan ya dafa kafadarsa alamun bada kwarin guiwa sannan.
Tashi lukman yayi ya tsaya sannan yace ni zan aureta.
Kallonsa jami’a sukayi, babu bata lokaci aka aminta dashi musamman da akaga Cewa shidin abokin yazeed, kuma shi yazeed din ya kasance suriki na gari.
Kuma ai masu iya magana na Cewa inkanason kasan halin mutum to ka tambayi su Waye abokansa.
Hakan yasa babu bata lokaci aka daura aure sannan akayi sanarwar jana’izan Sulaiman.
Nan hankali Yan cikin gidan ya kuma tashi aiko nan wasu sukasa kuka yayinda wasu sukayi shewa Suna fadin “ahaiye cass, yo dama anga mai Hannu da shuni an like masa anaso ashiga Dan aci bagas toh ta Allah Ba taku Ba zaliha dai anzama Amaryar lukmanu 😀😀😀😀 auren shige aka mata” wata mata tace yo danma mutanen suna da mutunci naji ance anbada sadaki naira tamanin kome? Kinsan gidan ya kacame banji dakyau Ba.
Wata tace naira tamanin ko sanda rake yafi haka shewa suka kuma sawa dai dai lokacin waliyin zalihan malam ado (Wanda akayiwa yarsa fyade #chapter 2)yayi sallama.
Iya dake sharar kwalla tama kasa magana saboda halin da diyarta ta Shiga domin tunda ta farfado ta kafe waje daya da ido Ba tayiwa kowa magana Ba sannan bata yi kuka ba, ta amsa sallamar sannan ta nufi hanyar kofa tana mai saka hijabinta.
Gaisawa sukayi sannan ya mata ta’aziyya,addu’a sukayi ma Sulaiman din sannan ya miko mata 80k cas Kamar yadda aka bashi sannan ya Samar mata yadda akayi lukman ya auri zalihan.
Godiya tayi masa sannan ta basa 10k nan fa ya rufe ido yace Sam bazai karbi kudin ba. Haka iya ta hakura ta tafi tana kara masa godiya.
Koda ta shigo ciki daki ta nufa ta boye kudin tunda kannenta guda 3 ne kawai a dakin sai innar minal. Matsowa kusa da zaliha data sandake da minal daketa aikin kuka iyan tayi sannan ta lallashi minal nan hankalin minal din yadan kwanta tunda lukman din da aka aurawa zaliha lukman abokin yazeed ne ba wani ba kuma yanada mutunci.