KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Nanfa suka fara kokarin saka zaliha tayi kuka amma shiru sanda innan minal ta matso kusa ta yi mata nasiha sannan tace ta rike mijin ta da amana ta danne zuciya tunda Sulaiman din ya tafi Anan tayi breaking ta hawaye suka fara zuba tahau shure shure Kamar mai tabin kwakwalwa. Ihu take tana Cewa wallahi ba mutu ba ni Sulaiman dina bai mutu ba,Nasan bazai barni ba ku sakeni,ni kusake ni.
Kanwar iya mai Suna iya murja ce ta fita sannan tace wa jama’a sun gode da halarta da sukayi.
Wannan matarnan ce tace yo ai bansan baban zaliha munafiki,Mara mutunci bane sai yanzu, Ashe batada hankali shine zai aurawa Dan mutane.
Tasss!taji an dauketa da tafi.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€
Agidansu Sulaiman kuwa ana sanardasu wannan labari mahaifiyarsu ta yanki jiki ta fadi hospital akayi da ita Ashe coma ta Shiga.
Laila Kanwar Sulaiman rasa Inda zatasa ranta tayi. Kanin babansu Alhaji Ibrahim shi yasanar dasu wannan labari.
Lallashin laila da sauran family yake domin sunyi rashin da saiga goje(from chapter 10) ya shigo yana fito kallonsa kowa ya tsayayi
Shoki ya kwaso ya sauke sannan ya watsa zanku. Babansa ne ya daukesa da mari sannan yace kaide bansan me zanyi dakai ba da’ace a Asibiti aka haifeka da nace an canja Mani Kai, Allah ya Shirya amma ace mutum Dan uwansa ya rasu ko ajikinsa ?
Soka earpiece dinsa da yayi a kunne sannan ya kalli baban NASA yace kai tsohonnan ka kiyayen Idan ba haka ba kauna zaka raka wacan shegen Sulaiman din. Aikin banza duk kunbi kun cikawa mutane gida da kukan Munafurci.
Ke laila ki mana ko kallon Inda yake bata yi ba yace ba dake nake ba? Ta sharesa falla mata mari yayi yace ke Dan ub*nki Dan kinga anasonki shine zakiyi wa mutane hauka?
Kuka ta fashe dashi tace Allah ya isa wallahi Allah bazai barka ba. Wani mari ya dauketa dashi sannan ya take mata kafa yayi ball da ita yace kucaka kawai.
Fitonsa ya cigaba dayi har ya fice yana fadin Daga gadon asubiti uwar taku ma ta wuce.
Hey lovelies masu Neman update gashinan na muku.
See yah!
Miss untichlobanty💕
19 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
🌹by @mzz_untichlobanty🌹
CHAPTER 43
Bayan daurin auren lukman ya kira ayush ya fada nata yadda akayi sannan ya fada mata yadda sukayi da yazeed tace Ba Komai ta fahimceshi.
Dadi yaji sosai kamin sukayi sallama irin ta masoya.
Sannan suka wuce wurin jana’izan da za’ayita bayan la’asar shida sauran jama’a.
Bayan andawo ananne sukayiwa iya sallama koda ta fito gaisheta sukayi tare da ta’aziyya ta amsa musu sannan sukace batun amaryan ne shine mukace bara muji yadda kuka yanke shawara saboda Asan yadda za’ayi.
Iya tace ai babu wani damuwa rana ita kuzo ku dauki amaryar ku sukace to ba matsala amma my again MJ tadanyi koda mako biyu ne tadan watstsake Daga radadin mutuwar iya tace hakan ma yayi bayan mako biyun sai kuzo. Insha Allah Nasan zaliha batada matsala.
Godiya sukayi kamin suka Koma gidansu Sulaiman domin yiwa Yan uwansa ta’aziyya.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Ya abubakar ne sanye da shaddarsa brown ya shigo gidansu Sulaiman domin yakanje once in a while Dan haka sun saba da Yan gidan bai taradda kowa ba sai laila dake zaune tama kasa kuka saboda duniyar tayi mata zafi Dana can ga rashin uba,yanzu ga mutuwar Dan uwa,ga mahaifiyarta rai a hannun Allah, ga takurar da isma’il (goje) yake mata Dan kafin ya fita ma sanda yayi mata zagin uwa da uba sannan ya fice tareda Cewa ko tanaso ko bataso sai ta aureshi. Ga ciwon boyeyyen soyaiyar ya abubakar dake nukurkusatta tun tana karama domin tun kafin su zaliha da Sulaiman su fara soyaiya sunsan juna saboda kamin baban zalihan ya rasu yayi aiki akarkashin baban Sulaiman din,Dan haka ya abubakar kan takoshi Duba da Cewa shidin bashoda da namiji.
Anan dai ya abubakar ya zama abokin Sulaiman kuma ya saba da laila sosai tun tana shekaru 9 shi kuma 18 Inda yake ce nata baby laila har kwalliya yake mata sannan duk sanda tayi ado to shi zai fara gani. Shiyasa duk yadda goje ke mata naci ko kallonshi baikai tayi ba balle tasoshi gashi mugun Dan daba ne kuma tsaf zai iya kisa.
Sallama ya abubakar din yayi jin ba’a amsa Ba yasa ya shigo da alamu tayi zurfi a duniyar tunani Dan haka yazo gabanta ta yazauna Hannu yasa ya tallafo fiskanta dukda ko yasan Cewa bai dace Ba saboda yanxu ta girma ba kamar da ba yanzu shekarunta 17 amma yanayin daya ganta zuciyarsa ta raurawa bazai iya ganinta cikin yanayinnan Ba.
Da ido kawai ta kuresa yace baby laila Kiyi hakuri Nasan Cewa munyi dashi Kiyi hakuri kinji Allah ya jikan Sulaiman rungumeshi tayi tsam kamin ta fashe da kuka shima dai daskarewa yayi na wani lokaci domin rabon da susami kusanci irin wannan tun tana 12 barsu dai sukan rike Hannu once in aw while saboda Sabo dasukayi dayin hakan.
Kasa hanata yayi illa ma Daga baya ya zuro hannunsa ya rugumeta tsam.
Daidai lokacin su yazeed suka shigo ciki suma tunda bawani zaman makoki za’ayi Ba Dan basason bidi’a Dan haka babu mata a gidan sai waje ne ma mutane basu gama watsewa Ba.
Parking motarsu sukayi awaje kamin suka shigo suka ja suka tsaye baki a bude sallamar tasu ta makale domin abinda idanunsu sukayi artabo dashi ya Abubakar ne rungume da laila tan kuka yana shafa kansa da Hannu daya.
Kallon juna sukayi kamin suka sakewa juna murmushi.
Gira daya yazeed ya dagawa lukman yayinda lukman din ya masa thumbs up
Sidam sadam suka Shiga suka zauna a akujera yayinda ya Abubakar yace shh Dan Allah ki dena kuka sai lokacin laila ta bude baki cikin sarkewar murya tace ya abibi (yadda take kiransa) nikam na Shiga uku rayuwa tai min zafi.
Shafa bayanta ya farayi yace karki damu Komai zai wuce Allah ne gatan bawansa kuma ina tare dake ki daina kuka kinji tace to Ummi. Yace yes Ummi tana inane muje kiraksni inyi mata ta’aziya.
Kuka ta kara fashewa dashi tace Ummi ta fadi ankaita asubiti.
Kallon juna su yazeed sukayi alamun what ? Gaskiya rayuwar yarinyar yana garari.
Ya Abubakar kuwa Cewa yayi Kiyi shiru kinji zata zamu lafiya Insha Allah Kiyi hakuri ki daina kuka. Ko kinaso nima in miki kukane ya fadi hakan a muryar wasa. Girgiza kai tayi tana turo baki yasa hannunsa yadan ja kumatunta yace good girl murmushi tayi kadan yayinda yake goge mata hawaye.
Yazeed ne yayi gyaran murya yana Dan shafe sajensa, Adan tsorace suka saki juna laila tayi saurin cewa bari in dauko hijabi na mu tafi asibiti sannan ta gudu yayinda Abubakar ke Sosa kai yana Dan dariya yace a’ah su angwayene dakansu? Ai banjo shigowanku ba.
Gyada kai yazeed yake yana smirking irin ai dole yayinda lukman kuma ya fadi abinda ke zuciyar yazeed din.
Yace mutumina ai dole bazakaji shigowarmu ba irin wannan dumi da kake sha.
Chanja zancen ya Abubakar yayi ta hangar Cewa kun Shirya my tafi asibitinne? Sukace mukam a Shirye muke shiri ai saikai. Mikewa yayi yace ai nima na Shirya sannan ya nufi kofa yazeed yayi saurin rikosa tareda Cewa in-law dawo Duba rigarka dakyau. Lukman yace wani ai sai ya dauka dambe kayi.
Akunyace yadan Jade rigarsa squeezing din ya ragu. Lukman my man maganar nanfa bata Kare ba gara ma kaji.
Daidai lokacin laila ta fito. Gidan biki suka fara biyawa domin su dauki minal aje dubiyan da ita.