KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Yazeed yace Dan Allah karkice sai Muna cinye duka tace tasa ma kuwa. Ajiyan zuciya ya sauke yau ya Shiga uku.

Ruwa ta dibo a wani roba suka wanke hannu yazeed nata complain Wai ta barshi yaci da cokali bai iya ci da Hannu ba. Tace zan koya ma karka damu. Kunun ayan ta zuba musu yayi sanyi harya fara kankara hakan yasa atake kofin su kayi gumi.

Nanfa tasa yazeed agaba hard a zare ido ta yanko katon loma tace ma za bude bakinka abin tausayi yazeed yayi tace gara ma ka gyara fuskarka Dan ban ganiba wallahi.
Nannanuyan ajiyan zuciya ya sauke yace fine na yi surrender.

Abinda bansani ba kuwa yazeed kawai aji yakeja Dan yawunsa har tsinkewa yakeyi dukda Cewa lomar da ta dauko ta masa yawa bude bakin yayi aiko ta dannan mai take ya hadiya ba bata lokaci ya kara bude wa.

Kyalkyalewa tayi da dariya tace ayi magana mutum yace kazanta ne ko ya masa yawa amma gashi muduk ya cinye lomar tuwo turo baki yayi cike da borin kunya yace ai Dan inajin yunwa ne. Tace zama ka fadi Gaskiya ne sannan suka ci gaba da cin abin cinsu Suna tsokanar juna tare da kora kunun ayansu mai sanyi.

Yazeed sanda yasha 3 cups minal ne tasha 1 acewarta sai ya Dan huce kamin tasha saboda aunty fauzy tace Abu mai sanyi yanada illa ga mace ko menene shi.
Saide abinda basu sani ba Anyi musu aika aika acikin kunun.

Bayan sun cinye yazeed yace kai inajin sai Nayi sati kamin in kara cin abinci minal tace shiyasa dazu da kaci dambu da rana ka kasa tashi baka kara cin abinci ba sai bayan sati,yace tsokanata kikeyi ko ? Kinsan halina fa. Ko ba Komai kaci kazantar kazama throw pillow ya janyo zai Willa mata ta ruga a guje tana fadin tsaya in gyara maka gado muyi tausar danni kewa baba tausa a gida dariya kawai yayi yace excuse not accepted.

Wani wayau yakeyi bashida natsalar komi sannan ya fara jin wani jiri jiri idonta ta fara nauyi kawai shi daya sai ya tsinci kansa da yin dariya mai sauti cikin alamun buguwa . Gefensa ya kalla yaga wayan minal Dan haka ya dauka yaje ya buya a bayan kujera budewa yayi yaga batasa lock bama.
Bibbiyu yake gani Dan haka cikin murya buguwa Kamar mutum yasha giya yace kai dole nema in kira Dr Muhammad yaban glasses ban gani.
Neman number din Dr Muhammad din ya fara a bayan minal yace kai Ashe ba wayata bace.

Wayarsa ya fara nema ganin bai sameta ba yace bari in kira wayar inji ta Inda zatayi ringing hannunsa yasa a aljihunsa ya zaro wayarsa yayi dialling number din da yaga tayi displaying my number aransa yace har wayar ma tasan number na. Thumbs up yayiwa iska.

Kira ya fara yi amma sai line busy akece masa, cikin zuciya yace ko Waye yake using wayana oho.
Wayan minal ya kalla yace yauwa bara inyi using wayan aunty kazame, numbarsa ya rubuta yaga babu Dan haka yayi saving yana murmushi irin ya mata aika aikannan.

Minal ko tana Shiga dakin taji Kamar jiri na dibarta amma Ba sosai Kamar na yazeed ba tunda ita bata sha dayawa ba amma sai ta basar gadon ta fara kadewa taji yazeed yana dariya parlour tace ko me ya samu yake irin wannan dariya oho.

Gadon ta gyara Wanda alokacin itama ta fara maye amma Ba worse irin na yazeed ba ctafiyatta bata canza sosai ba amma takanyi tangadi sabanin yazeed da ko tsayuwa baya iyayi.
Handle din kofan ta kama zata fito……..

Yazeed ko jin engine din kofar dakinsa tace ‘dit yasa ya kara buya yana murmushi irin ta yara yana lekowa kadan kadan shi adole kar minal ta ganshi.
Abinda be sani ba shine ba a bayan kujera ya buya ba gefene dan haka da mutum ya fito Daga dakinsa zai gansa.

Minal ko tana fitowa ta hangosa a gefen kujera yana lekenta. Ganin Kamar buya yake yasa ta Daga gira alamun confusion😕

Da shike itama kan da sauki sai ta biye masa tana Cewa maci tuwo kana ina ? Maci towo nifa ban ganka ba.

Dariya kasa kasa yazeed yayi yace wawuyace bata Hannu ba, nemansa  na karya ta farayi kamin can tazo Inda yake tace na kamaka!

Dariya yayi yace kai…aunty kaza..me A…she ki…..nada wayo?

Kallonsa tayi tace kai yaronnan giya kasha?tsutsuru yayi da ido yace aun…ty ni ban…sha giya ba. Allah da gas..ke na..ke Kiji ba..kina ma haha.

Ya fadi haka yana buso mata iskar bakinsa. Kauda kai tayi tace Allah giya kasha gashi muryakka tayi ta Yan shaye shaye? Wato su murtala da babba da nake musu fada akan shaye shaye shine suka kawowa mijina Mayan maye?zanhadu dasu.

Yazeed ne yace da..ma ni mijki ne aunty ? Tace eh a bugs kake shiyasa ka manta. Mikewa ya fara kokarin yi zai fadi ta rikosa dukda ba wani karfin gareta ba tunda itama ta bugu,kofar bansani suka nufa suna tangal tangal yazeed na fadin shhshhh karki Fada..wa kowa sa..boda kema kin…sha.
Kuma kina Fadawa mamana zan Fadawa innanki zaro ido minal tayi tace bazan fada ba Dan Allah karma Fadawa inna wallahi ub*ana zata ci.

Sai alokacin ta lura da yazeed zai bige da gini Dan haka tace kai Ashe ma gini ne?ni na dauka kofar katokoce ai. Sannan ta janyoshi suka nufi daki

Dariya yazeed yayi yace amma Gaskiya kin bugu yanzu ke baki taba Sanin Cewa da Leda akayi kofar dakina ba?

Tace Kaine dai ka bugu ka manta giya kasha yace kema giya kikasha tace kaima giya kasha sai suka hada baki wajen Cewa giya muka sha! Sannan suka fashe da dariya.

Longest chapter ever🙌

Da fatan yayi cheering mood dinku saboda inaso ana tafiya ana dariya, wani wajen ayi tashin hankali,wani wajen abin dariya,wani wajen abin tausayi kunga zaifi bada colour.

DA YAZEED DA MINAL WA YAFI ABUN DARIYA A YANAYIN BUGUWA?

Ina jiran comment dinku and don’t forget to

COMMENT! AND COMMENT !! AND COMMENT !!! AND COMMENT !!!! AND COMMENT!!!!! AND COMMEEEENT !!!!!!

yeah I am crazy today nima nasha kunun ayan ne ai😝😁.

Miss untichlobanty💕

6th December,2019
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

CHAPTER 52

Suna shiga daki yazeed ya fara kokarin cire riga amma ya kasa minal tace kai me hakan ? yace aunty sanyi nakeji ki ciremin rigana sai kimin tausan.

Minal ta fashe da dariya tace amma ka bugu dayawa kai bakasan Cewa damina akeyi yanzu Ba? kuma mutum yanajin sanyi shine zai cire Riga? Shima dariya yayi yace woooo kin fado war was yanzu lokacin zafine toh, tace Ba zafi bane yace zafine tace Ba zafi bane yace ZAFINE tace na hakura zafine amma dai ka bugu tunda Cewa kayi sanyi kakeji.

Yace kin yarda kema kin bugu tace na yarda. Rigan ta taimaka masa suka cire. Sannan ta daura hannunta a kirjinsa tace kai yaronnan aradu jikinka Nada kyau gwaliyo ya mata yace banga naki baaaa.

Tace ai nawa yafi naka kyau yace karyane tace kai auntyn ka ne take karya?kunne ya kama tare da turo baki yace sorry aunty amma dai kinsan na Fiki kyau ko? Turo baki tayi Kamar zatayi kuka tace Allah Baka fini baaaa.

Yace nafiki manaaa ki yarda kukan shagwaba ta fara sannan tace Allah Baa fini Ba tsaya fa ka gani kokarin cire Riga ta farayi amma ta kasa Neman zip din riganta tayi amma ta rasa. Tace kai so ka dubawa auntynka zip din ta.

Yace ina zanzo kuma bayan kina rike da dayan hannuna tace mantawa Nayi dubamin tana sakinshi ya tafi luu tayi Saurin rikoshi tare da zaunar dashi. Juya masa bayanta tayi ya Duba can yace naga zip din amma banga kan Ba tace ka Duba na gaji da tsuguno can yace Allah ki kama telan dayayi mini dinkinnan ki hadasa da Yan San;sama a kasa yasa miki zip dinfa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button