KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaunar da ita yayi yace ke Shashasha bakisan a cikin mutane muke ba ? Sannan ko kin manta da cewa jirgi ne da kike kokarin tsayawa tace au na manta ne.
Ameera tace lafiya take ihu? Minal tace albishir yamin shiyasa kamin suka cigaba da magana tace toh ya basu zauna tare da mu ba yace saboda wasu sun rigamu kinga babu dadi ace anyi cancelling saboda a bamu a rashin Adalci ne ko? Ta daga kai yace yanzu suna business class idan mun sauka zamu hadu.
Surutu taci gaba da mai har bacci ya dauketa. Gyara Mata kwanciya yayi kamin ya kunna film abunsa.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo karshe littafi KURUCIYAR? MINAL da fatan an karu kuma an fadakartu.
Toh wasa nake su o oh har an rude za’ayi min caa aka?
Don’t forget to comment in kunason update me yawa
See you soon a next CHAPTER.
Takuce KARAMARSU BABBARSU wato
Miss Untichlobanty ?
4th February, 2020.
??KURUCIYAR MINAL??
?by miss Untichlobanty ?
?CHAPTER 74?
RECAP…..
Surutu taci gaba da mai har bacci ya dauketa. Gyara Mata kwanciya yayi kamin ya kunna film abunsa…….
Koda jirginsu ya iso tashinta yayi tunda ba halin ya dauketa, ta departures’ door suka fito suka fito suka hango cars gida biyu ga wani ya daga carbon paper an rubuta captain yazeed abdulmajeed wajen motan suka nufa nan sojoji sula Sara masa direct hotel din da zasu sauka akayi dasu minal da zaliha an saki baki yayinda luku ke cin magani dan yanzu baya sakar wa zaliha fuska.
Akwana atashi anyiwa yazeed aiki kuma its successful. Nan fa su minal aka rikice nesa yazo kusa. Dakyar da dubara akayi abin, kunya duk ya isheta Dan gani take kowa yasan abinda ya faru.
Wasa wasa yau watansu 3 a Germany amma shiru kake ji babu ciki babu alamarsa ga yazeed yabar aiki jingim kuma next week za’ayi bikin kara masa girma wato ya zama major general yazeed abdulmajeed Umar.
Haka suka tattara ya nasu ya nasu suka dawo mom duk ta damu saboda tanason taga jikokinta kamin rai yayi halinsa tunda batasan sanda zata tafi ba.
Koda suka dawo Nigeria har anayi auren laila da ya Abubakar da kuma zakiyya da Jamal ba tare da bata lokaci ba. Yanzu haka laila nada cikin wata da sati biyu daya ma minal da fari ta dau abin wasa amma da taga cikin Laila abin yadan fara damunta amma ganin ai ba’a wani Dade ba yasa ta kwantar da hankalinta, yazeed na lura da ita kaf amma ya zuba Mata ido.
Shiri suketa yi yayinda minal da zaliha keta yin fada akan lallai sai minal tayi kwalliya yayinda ta dage cewa bazata yi ba.
Zaliha tace kinsan Allah idan dai bazakiyi kwalliyar nan ba zamuyi fada ? Bakisan cewa za’a dauke ki a camera bane ga yan jaridu da gidan talabijin dukzasu zo minal tace tunda ba gasar kyau za’aje ba bazanyi ba kuma ai miji akewa kwalliya ba ?artin banza dawofi ba. Kuma ni ance miki zanje ne dan adaukeni? Zanje ne Dan mijina. Dauko gyalen da zatayi rolling tayi Dan kayan da tasa baya bukatar hijab ta dau Jakarta ta fice dan zaliha ta bata haushi.
?
A bakin kofan side dinta tayi kicibus da yazeed ciccibarta yayi yana fadin wa ya tabamin baby na? Dauke kai tai tana kumbura yace my minal fishing harda ni ne? Sharesa tayi bai dirar da ita ko ina ba sai dakinsa, dakyar yashanyo kanta suka sha romance ganin yana neman zurfafawa yasata guduwa.
Haka akayi bikin Karin matsayi akayi su pictures kowa na farin ciki aka watsesaide kash basusan cewa nanne farin matsalar su ba.
Yazeed kwance kan cinya minal a parlour suna kallon wani Indian series tsabar abin tausayi minal batasan sanda ta fashe da kuka ba dariya yazeed keta Ma ta wai ta jona Shaun asararru masu yiwa film kuka sai turo kanshi take tana ya tashi tunda abin hakane daidai lokacin luku ya tsindumo babu ko sallama sai haki yake da alamu gudu yayi. Yace ina wayarka inara kiranka baka daga ba? Yazeed yace ba wannan yafi muhimmanci ba, wa ya baka izinin diro min cikin bangare ba ko sallama. Tsaki lukman yaja cikin haki yace kai dalla share wannan bakas……. bai karashe ba yazeed yakai masa naushi tsabar kishi. Minal tayi saurin rikeshi tare da kallon luku tace ya akayi? Yace government tasa an rufe gaba daya account din yazeed saboda ana zargin wai ya hada baki da yan siyasa anacin kudin kasa sannan bazai iya sayar da kadarorinsa ba ma atakaice de har company yanzu duk NASA ne amma suna under government so he does not have a say a kansu har nanda 3 months? Abu daya aka barma daga gidannan sai ka zabi mota daya. Yanzu haka EFCC suna bin cike kuma you can’t use your passport kamar kasan ba kuma baza’a baka Visa bama koda emergency har sai 3 months ya cika.
Yazeed ya zama shock ma dan shi baya ko irin kai wa yan siyasa ziyara da akeyi balle ya saci kudi daga jin magana akwai tuggu a ciki. Bakinsa na rawa yace menene hadin companies din mahaifi na da za’a saka a ciki ? Luku yace saboda idan ta tabbata gaskiya zai zama na gwamnati wai shine hukuncin ka.
Yace ya batun Wanda na bayar dasu ga families Dina? Luku yace eh wannan basu da harka dashi tunda yanzu ba naka bane ajiyan zuciya ya sauke tace atleast munada yadda zamuci abinci maza ka hada meeting da uncles Dina baki daya on Saturday, Luku yace sure kamin ya fice.
Gumi ke tsattsafowa yazeed domin ba dukiya daya rasa bane ta dameshi yadda aka bata masa suna bai ji ba bai gani ba. Rungume sa minal tayi tare da kwantar dashi a kirjinta tace yazzy baby karka damu komai zai wuce is part of kaddarar mu.
Haka yaci gaba da basa baki har yayi bacci a kirjinta sai alaokacin ta lura da yadda hawayensa ya kika Mata Riga. Ajiyan zuciya ta sauke kamin tayi nata kukan Dan ta daure ne kar ta karya masa guiwa.
?????????
?Darius take shekawa abinta tare da cewa kai nifa shegiyace duk wadda ya taboni toh shida kwanciyan hankali sun raba kafa kamar aljanna da wuta.
Mummunin Alhajin da take zaune a cinyarsa ne ya sheke da dariya yace kaji shegiya wai dama kinsan akwai wuta da aljanna kike wannan tsiyar? Hade rai yayi Tace me kake nufi? Daidai lokacin wayanta yayi ringing ta dauka tace ya akayi ta dayan bangaren akace gaskiya fa madam mugu(bokanta) yana korafi cewa idan dai bazaki dinga zuwa yana biyan bukatar sa ba to saide ko dinga aiko da jarirai uku idan ba haka ba ku ?a?e. Tsaki Taja tace ni rabani da jarabarsa ban iyawa ga warin da yake zan karo ma 500k a samo Karin jaririn akai masa. Ta dayan bangaren akace hakan ma yayi.
Daga nan ta kashe wayan Alhaji yace amma baby wai me suka miki hakane kika tsanesu da kike kashe irin wannan kudi? Murmushin rashin imani tayi tace hmm bazata gane ba. Yace ada na barsu ganin abokin hamaiyar tawa ya mutu amma yanzu Dana hadu dake sai naji dole ma in ga kayansu musamman yanda dan ke nema yafi uban yin nasara.
Sauka tayi daga cinyarsa tare da fara safa da marwa a dakin tace kiyaiyar danake musu tafi Wanda kafirai keyiwa annabi na samesu fiye da yadda na tsani mutuwa ta kai Alhaji bari kaji idan har zanga sun kaskanta sun wahalu a duniya toh wallahi babu ja in ja na yarda in shiga wutar jahannama indai sun wahala. Banida matsala koda kuwa za’a ha?a ni da shedan a wuta a matsayin roommates.
Jinjina kai yayi kamin ya tattaro ya harhado tumbinsa ya Mike yaje ya rungume ta ta baya yace yanzu ne na ha? da macen data dace wacce bata tsoron ta baci indai saurinta zai cika gaskiya wannan jawabi naki ya kara sa min kaunarki a zuciyata.