KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Mutane kuwa ganin abin da akayi wa yazeed ba’ayi masa adalci ba gashi an kasa proving komai, an duba account summary dinshi da kuma information na company transactions dinshi duk kudinshi data company dinshi ne albashinsa ne kawai from government.
Dan haka mutane suka fara zanga zanga cewa dole a sake masa dukiya tunda yana taimakon talakawa.
Zaune take akan kujera tana juya wa tare da busa shisha. Wani number ta Kira tace maza kiyi aikin ku da fatan mutanen sunzo? Akace yes ma tace don’t make a mistake……
Order phone din su yazeed aka Kira ya dauka nan akayi placing order na birthday party abincin 25 people.
Aka hada aka kai bayan 2 hours sai ga police wai abin cin da aka kai is poisonous kawai suka rufe shagon take yazeed ya Kira yan NAFDAC yace ya sun duba abincinsu ba’a basu number ba police yanzu sunzo sun rufe musu aiki.
NAFDAC suka ce gasunan zuwa after 30min sai ga su. Yazeed yace ga yan sandan can suna jira they should talk to them, shugaban tawagar tafiyar NAFDAC din yace it’s true abincin is poisonous. Yazeed yace toh me yasa suka yi musu register a baya ? Sukace ai Sam basuyi musu register ba sannan sukace ma yan sandan a tafi dashi cell dukda cewa military officer ne ai yayi laifi sannan bulldozer zata zo ta rushe part din ko kuma ya bar wa government yace ai ba nasa bane mallakin matarsa ne Dan haka basuda right akai. Sojoji ya Kira har Wanda gwamnati ta kwace masa sanda suka zo sai ga jama’a ma sun iso, domin live komai ke faduwa ga yan jarida rututu.
Sojoji da mutane suka kewaye yazeed mutane sukace ba’a isa a rushe wajen ba yayinda sojoji sukace ko yabar maganan ok su bude wa yan sandan da nafdac wuta. Atake aka fara yarda jita jita wai yazeed shi ke supporting din terrorism wasu kuma nacewa ya hada kai da yan boko haram ne.
Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.
Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji karan harbi.
CABDI ANA CAKWAKIYA, YA KUKE GANIN LAMARIN ZAI KAYA?
MASHA ALLAH! DONT FORGET TO FOLLOW ME, VOTE AND COMMENT AND INA BUKATAR ADDU’AR KU MUN KUSA FARA EXAMS SO ZAKU JINI SHIRU GASKIYA.
THANK YOU! TAKUCE KARAMARSU BABBARSU
miss Untichlobanty ?
23rd February, 2020.
??KURUCIYAR MINAL??
?by miss_untichlobanty ?
RECAP
Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.
Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.
?CHAPTER 76?
Shiru wajen yayi tsit kowa yana register din abinda ya faru.
Faduwa minal tayi akan guiwanta tare da rike hannunta da aka harba. AI nan kakejin dau!dau! An sakewa Dan sandan nan bullet biyu a hannu.
Nan fa shugaban nafdac ya fara hadiya yawu tare da kokarin zamewa ya gudu, wabi cacuma sojoji suka masa sukace ko ya fadi gaskiya ko yaji ba kyau. Tsilli tsilli yayi da ido Dan yaga mutuwa a gabansa. Nan fa ya fara in ina,wani soja me zafin rai me suna musa ya gwabje sa da bindiga atake ya soma bayani cewa kudi aka biyasa ya fadi hakan.
Akace wa ya biyasa yace Alhaji tukur gadon kaya ne. Nan take ya basu registration number tare da bada hakuri yazeed yace ai dole a tsigeshi nan fa ido ya Rena fata m, haka ya dinga bada hakuri yana nuna nadamar da yayi sanda yazeed ya tabbata ya wahala yace yaji ya tafi zaiyi tunani amma fa hakan batayi wa Musa dadi ba Dan haka yasa shi lungu ya dan jijjibgesa ya sauya masa halitta kamin ya barsa.
Asibiti aka kai minal da Dan sandan nan jina jina nanfa magana ta lafa, chef of police din yace a masa afuwa ba laifinsa bane na yan NAFDAC ne da sukayi musu karya kuma munafiki harda shi a ciki.
Haka dai magana ta watse aka sasanta toh anan ne mutane suka sake tada mayar baya akan a sakewa yazeed dukiyarsa.
Shugaban yan sanda yana zaune a office gadon kaya ya kirashi yace asan yadda za’ayi da mutanen nan dake zanga zanga. Nan ya Kira yan sanda 3 yace a saki teargas a wajen zanga zanga. Daya daga cikin su mai suna lieutenant sabir murya kasa kasa cikin girmamawa yace :sir! This is totally dishonest and unfair, some police are the cause of the negative views people have on us. If not for dishonesty? these people did nothing wrong, they did not temper with government property neither did they go against the law. They are just practicing a peaceful riot. To tell the truth me and my people will not participate in this (yallabai wannan fa rashin gaskiya da rashin adalci ne, wasu yan sandan su ke jawa wasu bacin suna,idan ba rashin gaskiya ba mutanen nan basu taba kayan gwamnati ba basu yi wani Abu da ya Saba doka ba, peaceful riot sukeyi Dan haka shi bazai sa yaranshi suyi ba.)
Mari chef of police din ya wankawa lieutenant sabir kuma yace yaje shi bayan kwana 3 ya dawo ya karbo dismiss letter. Yace shidai da ayi aikin rashin gaskiya dashi gara ya rasa aikinsa.
A bangaren su yazeed kuwa bayan an cirewa minal bullet din ta farfado yazeed yana bata shayi sukaji hayaniya a hall din asibiti,saukowa minal ke kokarin yi daga bed dinta yazeed ya kwantar da ita kuka ta fara masa wai tanason ta gani dan haka ya dauketa suka fito Dan sandan nanne suke cakwakiya da sojoji zasu tafi dashi Dan ya harbi matar oga yayinda yake kuka yana fadin bashi ya harbeta ba. Yazeed yace a dakata. Tsit kowa ya yi yazeed ya iso gaban shi yace :kace ba kai ka harbeta ba? Da sauri gyada kai yazeed yace idan na gano kai ka harbeta wani hukunci zan maka yace a tsire ni.
Yazeed yace a kai bullet din da aka harbeta da kuma bullet din bingigarsa a duba su shi kuma kar a tafi dashi a mayar dashi daki aci gaba da kula dashi.
Koda aka Dubo bullet din ba na bindigar sa bane nan yazeed ya fara tunanin yadda zai gano na waye tunda yan sanda ke duba wannan kuma yan sandan ba mutuwa dashi sukeyi ba.
A kwana a tashi minal ta warke yau aka sallamo su kuma basu fadawa kowa abinda ya faru ba especially mom saboda kar hankalin ta ya tashi.
Marhaba umma hani tayi musu tare da sauran masu aikin inda sukayi musu jaje. Su nason minal sosai saboda kirkin ta.
Washe gari zabe? dan haka yazeed yace wannan shekara bazasuyi Zane ba saboda tsaro kar a kuma kawo musu hari. Sabon president yana zuwa ba tare da bata lokaci ba yasa akayi dismissing case din saboda ya gano rashin gaskiya kawai akeyi. Anan ne yazeed yayi resigning.