KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Zama yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace hajiya ki yafemin na lalata rayuwar diyar mu guda daya tak. Maganin hawan jininsa ta Nemo masa duba da yanayin sa tasan zai bukace su.

Minal kuwa tana bude idonta tace idan baka da hankali tabani kaga ikon Allah.
Ummu ce tace ke amina tu magana kikayi koko kunne nane sai alokacin itama minal tayi magana hakan yasa ta rungume ummu tanajin dadi.

Ummu tace aminatu yaya sunanki na asali? Minal tace amina ne kuma banda sunana babu abinda nake tunawa. Ummu tace kenan bakisan me cikin jikinki ba? Ta daga kai. Ajiyan zuciya ummu ta sauke tace ina kyautata miki zaton mutumiyar kirki amma da alamu kinada zafi. Nikam zan ajiye ki idan har kika haihu ba’a nemeki ba toh zan aurar dake, kinaso? Minal tace ni banason a rabani da ummu na. Ummu tace karki damu ko gidannan bazaki bari ba.

Fita tayi tare da karbar tuyanta a hannun sabi tana fadin shege ja iya abin arziki amma bakayi da tuyar kakemin kana samun albarka befi maka ba? Tashi yayi yana fadin ko ki karbi wannan abun ko na barar da komai. Kuma na dauki naira dari biyu tace nide karka sake kayimin shaye shaye da kudi na. Yace ke kika jiyo tare da bazata cikin gari.

??

Safwan ne da sahir suka shigo dakin yazeed da gudu suna fadin daddyn mu ya jikinka? Murmushi yayi tare da rungume su lokaci daya suka kwanta mai hakan yasa babu shakku ya yarda cewa yaransa ne.

Ayush ne ta shigo tana fadin kai kuyi ahankali kunsan daddyn ku bashida lafiya.
Dariya sukayi sukace daddy kaji aunty ayush ko? Wai muna damunka ? dariya yayi tare da cewa yaushe yara na zasu dameni?

Ayush ne tace brother akwai abin da nakeson in fada maka. Gyara zama yayi yace kaga dai yanzu 7 years kenan da rasuwar mummy sufwan ya kamata ka kara aure ko Dan su. Jin Jina kai yayi yace wannan gaskiya bari zan Nemo musu mummy, kunaso ko? Suka daga kai da sauri tare da fadada murmushin su amma dai sahir abun bai kwanta masa ba.

Ayush tace AI na samo maka kanason ka hadu da ita? Shiru tayi kamin yace
KO BAN GANTA BA NASAN ZABINKI YAYI DON HAKA ZAN AURETA!

GENG! GENG!! GENG!!!

Cabdi akwai cakwakiya fa jama’a.

Me zaku iya cewa gameda CHAPTER dinnan? Ya kuke ganin za’a kaya ne wai.

Karku manta kuyi VOTING tareda FOLLOWING Dina.

Ina matukar kaunarku! Daga taku KARAMARSU BABBARSU

Miss Untichlobanty ?

5th April, 2020.
[4/10, 20:41] Miss untichlobanty Writer: ?? KURUCIYAR MINAL ??

?By miss untichlobanty ?

WATTPAD,INSTAGRAM, TWITTER, TIKTOK @miss_untichlobanty

? CHAPTER 81 ?

RECAP

Ayush ne tace brother akwai abin da nakeson in fada maka. Gyara zama yayi yace kaga dai yanzu 7 years kenan da rasuwar mummy sufwan ya kamata ka kara aure ko Dan su. Jin Jina kai yayi yace wannan gaskiya bari zan Nemo musu mummy, kunaso ko? Suka daga kai da sauri tare da fadada murmushin su amma dai sahir abun bai kwanta masa ba.

Ayush tace AI na samo maka kanason ka hadu da ita? Shiru yayi kamin yace
KO BAN GANTA BA NASAN ZABINKI YAYI DON HAKA ZAN AURETA!

CONTINUATION

Akwana a tashi kamar wasa auren yazeed da safina saura sati daya cir. Lokacin da iyayen safina sukaji sunyi mugun mamaki da lokaci daya ta fitar da miji amma basu kawo komi a kansu ba ganin Wanda zata auran mutumin arziki ne ba sha ka tafi ba. Ayush sai rawar kai ake yayinda yazeed ko zaiyi auren ne saboda yaransa Dan shi yanzu ba mace bace a gabansa.

Minal zaune a parlourn ummu suna shan rake taji kamar mararta yadan murda. Dakewa de tayi taci gaba da hira can sai ta fara jin fitsari amma abinda ke damunta shine ta kasa yi Dan ta kewaye yakai sau 10. Ummu run bata lura da zirya hardai abin yayi yawa hankalinta ya dawo kan minal. Koda minal ta zauna ummu tace yar nan ince lafiya dai ko naga sai zirya kike murmushi minal tayi tace ba komai. Abinci ummu ta zubo musu sukaci minal ta dau kwanon zata wanke ummu tace ta barshi itako ta dage tsugunawa tayi ta fara zuba detergent babu shiri ummu ta Mike ta karba tare da fara wankewa daidai lokacin sabi ya shigo yana fito. Wani ashar ya danna tare da dauke minal da Mari har sanda ta fadi kasa Wanda ya janyo tsananta Mata nakuda. Yace bansan cewa ke yar dakikiya bace sai yau idan ba hauka ba ya zakiyi ki saka uwata aiki. Tau! Tau! Kakeji, ummu ta daukesa da maruka har biyu tare da mangaresa.

Hankalinta ne ya iyo kan minal saboda ihun data tsala nan fa ummu tasa ya Kira Mata uwani sukasa minal a daki. Yanda sukaga yini haka suka ga dare, daidai an fara kiran sallan asuba Allah ya albarkace su da……..

Yan biyu Mata yan cukul cukul gwanin sha’awa,dadi ummu ta dinga ji kamar jikokinta na gaske kankace me makota da munafukai da yan tsurku anata shigowa domin ganin yara. Kowa na tofa albarkacin bakinshi. Saide an fara tuka tsiya da minal ne lokacin da akazo wankan jego tace ai Sam batasan da zance ba saide tayi da kanta haka aka hakura aka barta tunda ba halin ayi Mata karfa karfa.

Sati na kewayo wa aka sha suna daidai gwargwado, inda aka samu sahla da zayyana.
Kuma a wan an rana ne aka daura auren ango yazeed da amaryarsa safina. Har yan kawo amarya suka gaji suka watse ango shiru. Su sahir ne suka shigo suna murna suja rungumeta suna fadin mommyn mu, sannu da zuwa. Yake tayi musu tana Dan tutturesu a dabarance yayinda a ranta take cewa kai indai yarannan kamannin uban su suja dauko toh lalle na jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

Dalewa tsakiyar gadon sukayi suna tsalle ta daka musu tsawa tsirata sukayi ta nuna musu kofa sidif sidif suka fice suna kallon juna. Bayan sun fita Safwan yace mommyn nan batada kirki. Sahir yace maybe kawayenta ne suka bata Mata rai. Rugawa sukayi da gudu abinsu ko a jikinsu.

Shiru shiru yazeed bai shigo ba har bacci ya dauki amarya a wajen. Mutuminku ko tun da aka daura aure ya shige dakinsa ya kwanta Baku kara jin duriyar sa ba yanaji aka kawo amarya aka gama bidiri aka wuce tsaki yaja tare da kwanciya haka kawai yakejin haushin kowa dake tare dashi a lokacin ji yake kamar ba shi ba.

Minal kuwa tsakar dare zayyana ta tashi ta fara musu kuka aka bata mama anyi yin duniya amma sai kuka basu suka rintsa ba sai bayan asuba yayinda sahla ta dinga bacci kamar gawa.

BAYAN SHEKARU 8

Dauke shi da Mari safina tayi tare da cewa wallahi sahir idan baka fice mun a daki ba zaka Rena kanka idan ba rainin hankali ba da ban yini ba zaka ganni ne? Tsabar munafurci zaka wani zo wai gaisheni? Kuma saura inji ka fadawa wa ubanku ni da kai ne mangajesa tayi tare da fita ta kunna TV a parlourn sama tare da kure murya kamar cinema.

Mummy ne ta fito tare da cewa haba safina irin wannan murya sukace cinema? Ki rage muryar tv din mana. Tafiya mummy taci gaba dayi amma me ? Sai safina taja tsaki juyowa mummy tayi tace je safina karkiga ina daga miki kafa ko nemi ki kawomin hauka a gida kinaji na ko toh wallahi idan baki kiyayeni ba zaki sani aikin banza da wofi. Mikewa tayi tare da cewa ke tsohuwa dakata kiji….. mummy ne ta datse ta ta hanyar cewa uwarki ne tsohuwa.

Daga hannu tayi zata wanke mummy da Mari ayush tayi caraf ta rike hannunta sannan ta yanka Mata Marin. Dariya ta sheke dashi kamin ta tattare zanyi nanfa suka zage dantse suka casu suns zagin juna ayush na fadin dama a karuwancinki na barki kikayi yayinda safina ke fadin ai yafimin zama da wannan Dan wahalar Wanda tunda mukayi aure sau daya ya rike hannuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button